NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 122 of 223

ke ba kya ƙaunar lafiyarki to akwai wanda ya damu da ke, ya kuma damu da lafiyarki, ya kuma ƙi jinin duk abin da zai taɓa masa lafiyarki". a wannan karan muryar tasa a hankali ta fita, murya da ta shiga bin kowacce jijiya ta jikina tana neman ƙassara ɗan sauran kuzarin da ya rage min. yawu kawai na haɗiya na kaɗa kai wajen ba shi amsa. har yanzu dai bai saki fuskarsa ba, sai ma ƙara tamketa da yay, ya ɗauke wuta kamar babu shi a wurin, nima na kasa wani ƙwaƙwƙwaran motsi, sai bugun zuciyata da ke ƙara tsananta, na kai yatsa zan goge ƙwallar da ke neman saukowa, sai dai kamin na kai ga hakan hannun Ya Kabiru me ɗauke da hanky ya goge min. na kalle shi naga yana kallon wani gefe na daban. a raina faɗi nake na shiga uku, wai zuciyata wacce iriyar zuciyata da bata da lissafi, Yayana ne fa, Yayana da mu ke uba guda, amma ta ke wani ƙazamin tunani akansa. na zuƙi wata iska me ɗumi sannan nayi ƙoƙarin ture dukkan wani abu da tunani ke haddasa min shi a raina, na gyara zamana na saƙala hannuna ta cikin hannunsa, ina leƙen wayar da yake shafawa. "lectures ku ke?". "umm". ya bani amsa a taƙaice, ni kuwa nan duk neman shiri nake yi. a lokacin sai na tuna da lambar wayar Saddiqa da ta bani ɗazu, na ɗauko ina ce masa,"Ya Please save this number for me, ta ƙawata ce ina so na kirata zuwa anjima naji if she arrives home safe and sound". wayar kawai ya miƙo min bai tankani ba, na karɓa nayi dialling sannan nayi saving na miƙa masa. "taki ce ai". jin abin da yace na gyara zama babu shiri, na kai hannu na juyo da fuskarsa da ya kauda gefe, bakina yaƙi rufuwa saboda murna. "you say what?, Ya cewa fa kai tawa ce?". na tambaya ina jujjuya wayar da nasan tasa ce, mamaki ya lulluɓeni a san da ya fito da wata daga aljihunsa, iri guda exactly da ta hannuna, sai yanzu na lura ta hannuna tafi tasa sabunta, sai na saki baki nama rasa wanne irin farin ciki zanyi. na shiga kwararo masa adu'a kamar yawun bakina zai ƙafe, sai kawai ya miƙe yay ƙofa yana faɗin,"ban siya dan ayi shirmen banza ba. research only". "an gama Yayana na kaina, Allah ya jiƙan mahaifiya yasa afi haka". daga haka kuma ya fita. *Abuja, 12:00pm.* tun zamansu a dining dan yin break fast idon Madam Gloria ke kan Emanuel, da dukkanin tunaninta na son gano abin da ke damunsa a kwanaki biyun nan, wani abu na damunsa, kuma yana ɓoye wani abu, tabbas tasan da hakan domin ba haka yake ba, shi mutum ne me walwala amma a cikin kwanakin da suka shuɗe taga duk ya sauya, koma ta kira canjin nasa da tun ranar da shegiyar yarinyar nan ta bar gidan, alƙawari ne tayiwa kanta in dai ɗanta ya sami matsalar damuwa akan yarinyar to tabbas sai ta shafe rayuwarta da rayuwar ahalinta sun zama tarihi. ta ƙara tabbatar da akwai matsala tare da shi tun san da aka zauna don cin abincin, amma shi ya kasa ci, illa aukin juya fork ɗin da yake akan wainar ƙwan. tayi gyaran murya hakan yasa duka yaran suka karkata hankalinsu kanta hatta kuwa Granny, yau babu Dad ya tafi wata seminer a can india. "baka da lafiya ne?". ta tambaye shi idonta a kansa, sai ya girgiza ma ta amsar a'a. "to mene ka tasa abinci a gaba kaƙi ci?". ya shafi gashin kansa ta baya yace,"ina tunanin meeting ɗin da zamuyi a gobe ne". ya faɗa yana miƙewa yaja kujerar baya, agogon hannunsa ya kalla yaga ƙarfe sha biyu an kusa sallar azahar ma kenan, cikin dabara yace da Mom ɗin,"i want to rest, zan kulle ɗakina kar a dameni". baki kawai ta taɓe ta bishi da ido har ya haura sama. tunda ya shiga ɗakin yasa lapton a gaba da zummar yin aiki sai yaji ya kasa, komai nema yake tsaya masa cak, ya saka duka hannayensa a sumar kansa ya yamutsa sannan yasa ƙafa ya ture table ɗin da ke gabansa, kamin nan ya kwanta akan gadon. tun ranar da ya musulunta yake jinsa tamkar wani sabon halitta, tamkar ba Emanuel ɗin da yake a baya ba, kuma tun wannan ranar yake jinsa da wata iriyar natsuwar ruhi da kwanciyar hankali a tare da shi, ga kuma wani farin ciki na babu dalili da yake yini a cikinsa, komai nasa sakayau ba kamar da ba da yake jinsa da nauyi. ko a jiya da su kai waya da Amadu abun da yace masa,"Sir ka kasance me godiya ga Allah da wannan ni'ima da yay maka, ka zama me gode masa da ya sa ka rabauta, ka gode masa da ya kuɓutar da kai daga duhu zuwa haske, ka ci gaba da roƙonsa akan ya tabbatar da kai acikin addinin da yake na gaskiya ba tare da wannan ni'imar ta yanke maka ba har ƙarshen numfashi". a yauma abin da ya haddasa masa rashin nutsuwar nan da yake da faɗuwar gaba ta yanda zai tunkari iyayensa da maganar cewar ya musulunta, da waɗanna kalamai zai fahimtar da su cewar a yanzu shi ne akan hanyar dai-dai su kuma su na kan hanyar ɓata, shi kuma a gaskiya ya gaji da wannan ɓoye-ɓoyen da bai saba ba ko kaɗan...ga maganar Malam da yay masa ayau na zancen aurensa da ɗiyarsa, sai kawai ya rumtse idanunsa ya shiga karanto adu'ar da ya gama haddarta a jiya, wadda ya yini a masallaci wani mutum na biya masa ita, dan Amadu ne ya turo masa ita ta waya shi ne shi kuma da yaje salla
🏠