u shi yasa ya karɓe kalmar Shahada da wuri...to na masa barka, idan ka koma ka miƙan gaisuwa kace ina gaishe shi tunda yanzu ya zama namu".
Ya Amadu zai tafi Ya Kabiru ya shigo, tun daga tsakar gida da Yagana ta jiyo sallamarsa ta ke kiran,"ɗan halak kaƙi ambato, ɗan albarka shigo ka ganni da baƙin asuba kamar korarru". ya shigo ɗakin yana amsheta da tasa tsiyar shi ma. sanye yake cikin coffee ɗin yadi me ƙaramar riga, yay kyau sosai a cikin ɗinkin, sai zuba ƙamshin da Yagana ke faɗi yake, yana sanye da baƙin glass ɗin da ke ƙara ƙawata kyawun halittar fuskarsa. ya ƙaraso ciki yana sawa Ya Amadu ƙafa kamin ya wuce inda Yagana ke masa nuni da kusa da ita. "Matar ya dai?". ya faɗa yana taɓa kumatunta. ita ma ta shafo fuskarsa tana koɗa kyan da yayi, har da cewa ba zata bawa yarinyar ƙauye shi ba, idan ya koma yaga ta aure a can ya aure kawai. sai kuma tace na shiga ɗaki na ɗauko mata ƙwaryar zuma, na kawo ta karɓa ta dire a gabansa tana faɗin,"Zuma ce farar saƙa, jiya bayan fitarka Mujibu yay min aikenta, ko sha banyi ba nace sai ka fara sha tun da nasan kai ma'abocinta ne, sha kaji me kyan ce". ta faɗa tana gutsurowa ta kai bakinsa ya karɓa, ni dai kallonsu kawai na ke ina murmushi, kuma kallon bana Yagana bane na Ya Kabiruna ne, da kallon na sa ke hadda tasirin wanzuwar wani abu a tare dani da ban san ko menene shi ba. ban san lokacin da wata dariya ta suɓuce min ba har da ƙwalla, lokacin da Yagana ta tura ƙwaryar zumar gaban Ya Amadu tana faɗin,"ga shi nan uban kwazazzafa sai ka gutsira, in faɗa maka Kabiru tun da ya shigo ya dameni wai dole sai na ba shi ai kai ba sai kasha ba, naƙi nace kai na ajiyewa, shi ne fa dalilin wannan uwar harar daka ga yana watsa min...dama tun kuna yara haka yake sai a zuba muku abinci ya wawashe ya barka da ƴar ƙaramar murya kana kuka, ƴaƴan Zulai ai akwai cin tsiya cikinsu a buɗe yake".
tabbas Yagana sai ta kashe auren da ke da soyayya ma, ba mara soyayyar ba, yanka sharri a wurinta ba ya da wani wahala, kuma idan tana yi sai ta ɗaure fuska ka rantse da gaske ta ke, duk tabi ta ɗaure mutum da jijiyoyinsa. da taga yanda Ya Amadu yay kicin kicin sai ta bushe da dariya tana faɗin,"Allah sarki Amadu, Allah ya jiƙanka ba dan ka mutu ba...kai Kabiru da wasa nake yi, kar naje ya ƙullaceni idan ya koma garin arna yasa su ɗaure min baki na shiga uku". kiran sallar azahar ɗin da akai ita tada su Ya Amadu suka fita zuwa masallaci, sai can Ya Kabiru ya dawo shi ɗaya lokacin na gama kwashe shanyarmu zan shige ɗaki, na rasa dalili, na rasa me yasa yanzu indai na gansa sai na ke jin ina faɗawa cikin wani irin yanayi me wuyar fassaruwa, gabana yayta faɗuwa. har ya iso gabana ban sani ba, dan nayi nisa a zuzzurfan kallon da nakewa bakinsa da ke motsawa da salon murmushi, ya lakuce min hancin yana faɗin,"kallon fa?". nace,"Ya Kabiru nima ka sammin abin da kake sawa kana ƙara kyau". murmushi yay ya kama hannuna da ba kayan, mu kai ɗakin Yagana. "duk kyauna ai ban kai Balarabiyar da Gwaggo ta haifa ba". a san da nake ajiye kayan nace,"tab ana cewa yanzu nafi kama da inyamurai kana haɗani da larabawa". "inji uban wa?". ya faɗa yana ɗaure fuska kuma yana tsareni da ido. su Sadiyya naji su na zancen, yanzu kuwa idan na faɗa masa ai babu wanda zai hana shi ɓaɓɓala ƙasusuwan yarinya a yau, dan haka sai na fizge da faɗin,"a jikina kawai nake jin kamar mutane za su ke faɗan hakan". har yanzu bai saki fuska ba, kuma bai bani amsa ba, sai ya kamo hannuna ya zaunar da ni a kusa da shi kamar wanda zai ɗorani a saman cinyarsa, kafin ya ɗora bayan hannayena akan tafukan hannunsa yana bin su da kallo.
"wancan ranar na faɗa miki fatarki bata son wanki karki ƙara, ashe baki ji ba, shi ne har da yin wanki me yawa haka". muryar tasa ta fito cikin sautin faɗa yana me shafa fatar wurin da ta kusa ɗaɗewa, ƙwarai an jima ana faɗa fatar jikina bata son wahala, shi yasa ko lokacin da Gwaggona na raye ban fiya aikin ruwa ba, aiki ma ko da Ya Amadu ya raba mana shara aka bani, idan kuma za'ai wankin yara ni na ke shanya, aikin taɓa ruwa ba ya wuce irin ɗan kaɗan ɗin nan. Yagana ta sako baki,"to kai an faɗa maka wannan yarinyar tana jin magana ne bayan ta zuciyarta". sai ya ɗago ido ya dubeni, ni kuwa Allah yaji ya gani ina cikin wani hali, dan yanzu ko ido bana son haɗawa da shi, tun da Ya Kabiru ya soma shafa fatata da tai ja ta ɗaɗe naji numfashina ya katse a ƙirjina.
"kin yi amfani da Sol de Janeiro Coco Cabana?". sai da nayi ƙoƙarin saita tunanina kan na kaɗa kai na amsa masa,"a'a, wanda na buɗe ma ai bai ƙare ba". a yanzu cikin ƙwayar idona yake kallo kamar me son karanto wani abin, sannan yace,"je ki ɗauko". na miƙe jiki kamar mara laka na shiga uwar ɗakin Yagana, na ɗauko akwatin da ya shaƙo min ita da tsaraba da zai dawo, na buɗe na ɗauko cream ɗin da yake nufi, sannan na fito na ba shi. ya ɓare robar sannan ya shafa min man a hannuna. "yau ta zama rana ta ƙarshe da zan ƙara ganin kinyi wanki da kanki. idan