NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 120 of 223

gaishe shi kamar wata munafuka, dan ni Allah ya gani ina matuƙar shayin wannan bawa nasa, ya amsa min a daƙile, ban damu ba inda sabo mun saba. "za kiyi baƙo zuwa anjima, ai na zai zo ya sameki?, danni yanzu kano zan je". maganar a ƙasaƙasa yayi, na fahimci ba ya so Yagana taji, na haɗiye wani yawu a maƙoshina da ya wuce min da ƙyar, kamin na ba shi amsa da cewar,"ya sameni a can gida". Yagana ta sallame daga sallar lokacin ta juyo tana shafa adu'a, adu'ar da ko yinta ba ai ba saboda sababi na cinta. "Amadu fata na gari lamiri, kuma insha'Allahu babu abin da zai sami awakina, in dai ba so kake mu sami saɓani da kai ba to ka daina ja musu jafa'i...na rasa wannan abu duk abi a sawa al'amuranka ido, alhalin kai baka damu da bawa ba, ni acikin jikokina ma mantawa nake da kai, dama kai ba mutumin da za'a iya zama da shi ba ne, Uwarka ma ban da ƴar kanta ce ai da tuni kasa ma ta hawan jini da wannan tsinannan miskilancin naka da na rasa aina ka gado shi, kana ganin ɗan'uwanka Kabiru fuskarsa kullum a sake duk wurin da ya shiga faran faran da shi, amma kai duk wanda ya zauna tare da kai sai zaman ya gundure shi, sai kayi wani gumm kamar wanda ke fama da cutar warin baki...Allah ya gyaraka, amma ka sauya hali ni shawara nake baka, idan kayi aure a haka Matarka yaji zata dinga yi". yay murmushi yana cewa,"Hajiya Yagana ikon Allah, ai daɗi da ke a tsiya da ke". sai da ta gama jan carbi kan tace,"ka rabani da tsiya dan wannan kalmar a gindin Zulai ta ƙare, ahh tou". yace,"Yagana wai ba kya kara ne?". sai ta ɗaga murya tana faɗin,"har Uwarka fa ta gama cin amarcinta bata taɓa kawo min farantin shinkafa da sunan abinci ba, ƙarshe ma sai cewa tayi ita ba zata iya girki da uwar miji ba...da labarin yazo kunnena naje har gidan na cashe ma ta, sai da taga ina da iko da igiyoyin da ta ke taƙama da su sannan tasha jinin jikinta dani ta hankalta...Amadu ba wannan ba ma, yanzu me ya kawoka gidana da sanyin safiya haka ko gama wartsakewa ban ba?". na dubi agogo naga har ƙarfe sha ɗaya da rabi amma ta ke kiran sanyin sassafe. ya ciro kuɗi a aljihu ya miƙa ma ta,"gashi kici goro, sallama dama nazo yi miki dan gobe jirgin sassafe zan bi". "to kuma sai a kace maka babu rana babu dare da ba zaka iya biyo wannan lokacin ba tunda sallamar ta zama dole a wurinka". ta karɓi kuɗin,"to an gode Allah ya shi albarka, yasa afi haka. dawowa ta gaba dai sai a dawo da himmar aure, zaman ya isa haka in ba so kuke ku shiga sahun tuzurai ba, sa'anninku duk sun tara ƴaƴa jiyama sai da naje sunan matar Saddiqu". yace,"Yagana ai mu da sauranmu har yanzu yara ne, shekara 33 fa kacal". ta kwaɗa wani salati tana riƙe haɓa da cewa,"ina zancen yara anan, kana ganin yanda Kabiru jin daɗi da hutu ya maida shi wani babban mutum, jiya fa da na dawo daga unguwa na shigo ɗakin nan na tarar da shi sai na zube ina kwasar gaisuwa ce nake wani babban me faɗa aji ne a ƙasar nan, ko fa fitila ban kunna ba jiya a ɗakin nan saboda yanda hasken fatarsa ya gauraye ɗakin nan, ƙamshi kuwa kace shi ne kamfanin turaren, baka ji ba daka shigo?...to shi matsalarsa ɗaya hannun ɓera gare shi, shi yasa ban cika son zuwansa gidana ba". bani kaɗai ba, hatta Ya Amadu sai da yay dariya, dariyar da ta lotsa dimple ɗinsa har ciki, ita kuwa kamar ba ita tai maganar ba, tana ɗaure kuɗin da ya bata a gefen zani ta ƙara cewa,"ba batun dariya bane Amadu, in dai Kabiru ne yana da halin ɓeraye shi yasa ma yau zanje wajen Malam Kabiru ai masa rubutu ya samu yasha kamin ya koma, kar yaje can ya ɓallo mana wani ɓallin...jiya fa da zan fita Zannira ta min aiken tuwon masara da lafiyayyar miyar kuka taji man shanu, na tura abuna ƙasan buhun can saboda ma kar Yarinyar nan ta shigo ta ganshi, ashe ajiyar banza nayi, dan ina dawowa na tarar da ɗan banzan yaron nan ya gama aikawa da shi cikinsa, kai kuwa Amadu kace min Kabiru bai kamu da cutar ɓeraye ba, dan su ne masu zaƙulo ajiyar da ba tasu ba...kuma fa saboda rashin kirkinsa ya kai intaha ko haƙuri bai bani ba, sai ma mita da yake min wai nayi shiru kansa na ciwo. ni kam Rakiya ai na gaji da zaman Kabiru, lokaci yayi ya koma can dama ni bamu samu haɗuwar jini da shi ba". na buɗe ba ki nace,"Kai Yagana, da Ya Kabirun ne ba kwa jituwa?, ranar fa da ya kawo miki gasashshiyar kaza kika ce kaf jikokinki kinfi ƙaunarsa". ta waigo ta ɓalla min harara,"aku uwar magana wa ya saka da ke?...wannan ai haɗa fitina ne baccin yanzu kika gama jin wa'azi, irinku ne masu ji basa aiki da shi. ni Kabirun ma ya shigo ya san yanda zai yi a haɗa da ke a tafiyar su Adawiyya ku koma tare, ba zai yiwu ki dinga haɗani da mutane ba...fisabilillahi yanzu ai sai kisa Amadu yaga baƙina, ya ɗau kuɗinsa dubu biyu ya ban kuma kina wani batu na daban, ke dai sam baki da hali kina da ƙatuwar matsala". dariya kawai Ya Amadu keyi, kan ya bata labarin musuluntar Emanuel, ta kuwa bushe da dariya har da kifawa,"shegiya ƙaniya! ɗan banza duk yanda akai mafarki yay ana cin ubansa a ƙabari har aka hasko masa zurfin gidans
🏠