a zai kawo barazanar nisanta kusancinmu ba, wallahi ba zanyi nisa dake ba Gwaggona, in har Aure ne zai rabani dake to na rantse miki da Allah ba zanyi auren ba, ai dai har saina kawo saurayi gidan tukunna Baba zai aura min shi ko, to wallah ba zan kawo shi ba tunda nasan Baba ba zai yi min auren dole ba, idan ya zama dole kuma zanyi auren to sai dai a zaɓa cikin biyun ɗaya, ko mu tare acikin gidan nan ko kuma na fasa auren gaba ɗaya, saboda haka Gwaggona ki kwantar da hankalinki babu abunda zai nisanta ni dake, ina kusa dake har ranar yankewar numfashina". Murmushin daya tsaya iyaka leɓenta naga tayi, wanda fassararsa tafi kama da ba zaki fahimta ba. Zan ƙara yin magana ta tari numfashina da bagarar da zancen da muke, tana ɗagani daga jikinta tace,"karfa ku makara azo ana sai kun kawo klin da sauransu". Ta faɗi hakan tana gyara min fuska da cewa,"Allah yayi miki albarka Mairo, ya tsare min gabanki da bayanki, yayi riƙo da hannayenki". Sai kuma ta hau yi min nasihohi na tsoratarwa akan rayuwa, ta kama kaina ta karanto min adu'ar da ta saba yi min a duk sanda zamu fita, tun banfi shekara shida ba na haddace Adu'ar da nake ji na fita daga bakinta agareni, "a'uzu bikalmatillahi tamma, min kulli shaiɗani wahamma, wa min kulli ainin lamma". Daga tsakar gida na jiyo Adawiyya na ƙwala min kira, tana faɗin takwas saura. Gwaggo ta ƙarasa tofeni da adu'oi tare da faɗar "tashi kije Allah tsare hanya, a kula sosai don Allah don Annabi". Sai dana kai bakin ƙofa zan fita ta kirani na dawo, ƙasan filo ɗinta naga ta ɗaga ta ɗauko wani abun hannu mai tsananin kyau sai ɗaukar ido yake, ta kama hannuna ta sanya min, magana nake so nayi akansa amma mamaki ya hanani, sai tambaya ɗaya da ta tsaya akaina, aina Gwaggo ta samo wannan warwaron me kama dana sarakai?, banda me bani amsa dan nasan ko na tambayeta ba zan samu amsar da nake so ba.
Fitata ɗakin Baba na shiga, na sa me shi ya kamalla karin kumallon safe yana zaune yana sauraron radio, na ƙarasa na zauna gefen dama da shi na zauna ina gaishe shi, fuskarsa ɗauke da annuri ya amsa min yana cewa,"har an fito makarantar?". "ehh Baba mun fito zamu tafi. Baba a bamu kuɗin makaranta". Ya zura hannu a aljihu ya ɗauko naira hamsin ya bani yace na ɗauka ashirin na bawa Adawiyya ashirin, goma kuma mu bawa Saleh.
Na ƙara matsawa kusa da Baba kamar yanda ya umarce ni, shi ma kaman dai yanda Gwaggo tayi min haka yay min, hannunsa na dama saman kaina yana karanto tarin adu'oi masu yawa yana tofa min, Tun shigowata ɗakin na lura da wani yanayi tare da Baba wanda ban saba ganinsa aciki ba, kai bama na ganinsa aciki, dan shi ma yau bashi da walwala, kuma a kallo ɗaya zaka gane akwai abunda ke damunsa, kusan dai irin yanayin dana sami Gwaggona aciki, sai dai shi ko da ya ɗago fuskata murmushin farinciki naga yanayi, sai dai kuma ni Mairo me wayo ce, dan tuni na gama karantar wannan murmushin na ƙarfin hali ne, sai da yayi gyaran murya tukunna naji yace,"a irin wannan ranar aka haifeki Mairo, ita ma kuma ranar da aka haifeki an kwana ana ruwan sama, saboda haka ina tayaki murnar zagayowar haihuwa Ƴata, Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarki, ya kareki daga sharrin mazan zamani, yay riƙo da hannayenki". Adu'oi ne iri-iri Baba ke jera min su, kamin shi ma ya ɗora min da tasa nasihar, nasiha me kamanceceniya da irin ta Gwaggo, Sai dai tasa akwai banbanci da irin ta Gwaggo, dan tun daga farko har yanzu da ya nunfasa cikin nasihar fitar kowacce kalma me isar da saƙo ce, kum duk zurfin tunanin da mutum zaiyi zai ɗauki lokaci kamin ya gama nazartar abunda ake son isar masa. Jikina gaba ɗaya naji yana neman mutuwa saboda wasu ƙalmomi na ƙaddarori da naji Baba na min karatu akansu, karatun kuma da naketa so na fahimta amma na gagara, dan kamar karatun yafi ƙarfin kaina a yanzu, amma wataƙila anan gaba na iya fahimta, to amma me yasa aciki ya tsoratar dani sak da irin tsoratarwar da Gwaggo tayi min?, lokaci ɗaya na haɗa maganganunsa da nata suka zama ajimlace, dukansu karatu iri ɗaya ne sai dai kowanne da yanayin da yay koyarwarsa, idan baka da saurin ganewa za kayi tunanin karatu ne daban-daban, to amma duk dana gane karatu ɗaya ne na kasa warware kalaman da nasan saƙo ne da yake mallakin wanda ake karantawa.
Ganin kaina na neman fashewa na haƙura da abunda ya girmi tunanina, na daɗa fuskantar Baba da tambayarsa shekaruna nawa a yanzu?. Ya bani amsa da,"shekararki goma sha huɗu cif Mairo". "to amma Baba me yasa Gwaggo ke cewa Sha uku?". "ita zaki wa wannan tambayar. Yanzu tashi ku tafi kar a makara". Na sauke numfashi tukunna na miƙe da ƙafufuna da suka yi sanyi, nayi mishi sallama na fito a ɗakin.
Adawiyya nata jefa min tambaya da sauyawar yanayina, sai dai ban bata amsa ba har muka ƙaraso ƙofar gida, a zahiri a duniyar nake amma hankalina ya cilla can wata duniya ta daban.
"Mairo, Mairo, Mairo". Kiran da Ya Kabiru ke ta min kenan, amma ko ɗaya banji ba sai da ya ƙara dana huɗu sannan na dawo firgigit daga duniyar tunanin dana faɗa, ya ts