NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 119 of 223

an kuɗin da ku ka ga na karɓa wurin Amadu naira dubu hamsin ƙar ya nayi masa da cewar zanja jari, boka zan kaiwa ya magance mana komai, yanzu nan zan shirya na wuce dan a kammala aiki da wuri, yau ai sai dai Malam yaji kunya a idon jama'a, dan sai jama'a sun gama taruwa yaron zai zo yace ya fasa, ban damu da duk ƙananun maganar mutane da za su biyo baya ba tunda ba akan ƴaƴana bane". naja numfashi nai tattaki na ƙarasa bakin ƙofar ɗakin, sannan na buɗe baki na kwarara sallama, hakan kuma yasa su kai tsit da abin da suke son ƙara cewa. Inna ta taso ta fito tana washe min baki da murmushin makirci, na tsuguna na gaisheta. "yau da sassafe haka, ko kun yi halin da ƙawar taki ne?". nace da ita,"a'a Inna ai anan gida na kwana. dama Inna ce tace ki bada kwanon abincinki tana sauri zata fita ne". "to shikenan bari na ɗauko miki". ta faɗa tana komawa cikin ɗakin, na ƙara cewa da ita, "Inna su Adawiyya sun je makaranta ne?". "a'a kin ganta anan tana aikin kukanta na gaira babu dalili, na rasa uwar da akai ma ta". na saki murmushin da ya fitar da sauti ina cewa,"ke dai Adawiyya kin shiga uku da damuwa, to idan kin gama kukan ki fito muyi break fast...Sadiya kema Inna tace kije ki ɗauki naki". Adawiyya ta fito jikinta a sanyaye, fuska duk ta kumbura saboda kuka. "ai gwara ni sau dubu akanki, idan ina ciwo bana kwakwazo". a wannan karan dariya nayi bayan na amshi kwanon abincin da Inna ta miƙon, na yi gaba ina ce ma ta,"ai kuka yanzu kika soma indai ba za kisawa zuciyarki haƙuri da salama ba...kuma ki sauri ki fito dan tafiya zanyi gidan Yagana". abincin muke ci amma gaba ɗaya na lura cin dole ta ke yi masa, damuwarta ta fito fili ƙarara ta kasa ɓoyuwa. bata san tawa damuwar taci uwar tata ba, hasalima ni ƙatuwar matsala ce dani da ban san ta inda zan tunkari al'amarin ba, al'amarin shirinsu na kunyatar da Baba akan fasuwar ɗaurin aurena. tabbas nasan duka zuciyoyinsu babu imani, musamman Inna da idan tace zatayi abu to sai ta aiwatar hankalinta ke kwanciya, tunani nake kamar naje na sami Baba na faɗa masa ko kuma na faɗawa Innata, to amma kuma idan na faɗa ɗinma babu amfani, dan babu me yarda da maganar da babu shaida. a can gidan Yagana tun da na shiga na sameta tana bacci na kwaso kayan wankinmu na fito da su, a cikin kayayyakin da Ya Kabiru ya siyo min na ɗauko wani sabulun wanki me ƙamshi, ina wankina ina sauraron karatun ƙur'anin da aka saka a gidan radio ina binsa, da yake izu talatin ɗin ƙasa ne kuma mun sauke a makarantar allo, sai naji zuciyata ta fara washewa daga dukkan damuwarta da fargaba. na gama shara na fito daga wanka sai ga Saddiqa ta shigo, na tafi da ɗan saurina na rugumeta ina yi ma ta oyoyo. Saddiqa sabuwar ƙawar da nayi ne a lokacin rasuwar Gwaggona, jika ce a wurin Baba Lami a kano su ke tazo hutu ne gidan Malam Liman. mun sha hira sose da ita kafin ta tafi, sallama dama tazo min akan zata koma gida hutunsu ya ƙare, hirar da mu kai da ita duk sai ta ɗebe min kewa, tana ta bani labarin makarantar bokonsu me su na turkish international school, kuma naji makarantar ta burgeni sosai har na ƙudurta a raina zance Ya Kabiru can za'a kaini, tun da dama har yanzu yana tunanin wadda za'a kaini ne, shi da Ya Amadu sun ce sun fi son private school me kyau da inganci, wadda ba za'ayi dana sanin biyan kuɗinta ba, kamar dai irin ta su Adawiyya, amma ni basa so nayi bording saboda matsalar idona da kuma firgita da nake yawan yi cikin dare. "ke ƙaro mana radiyon nan". Yagana ce ta faɗa tana daga zaune tana karin kumallon da Saleh ya kawo ma ta yanzu, babu yanda banyi da ita ba ta ɗauki sabon brush ɗina ta ke amfani da shi taƙi, wai ita tafi ganewa gawi ko kuma tasa ruwa ta kurkure bakinta, ita bata yarda da wannan abin me yaji na bature ba, haka kawai ya ɗaɗe ma ta dasashi, ko kuma shi brush ɗin ya karya ma ta ƴan haƙoranta da Allah ya bar ma ta. "ku guji munafurci domin yana daga cikin manyan kaba'irai, wanda Allah SWT yaywa masu yinsa tanadin wutar jahannama. a littafinsa me tsarki yana cewa,"innalmunafikina fil darkil asfali minannar, fabashshirhum bi'azabin azim". munafurci yana nufin cin naman mutane, ka ɗauki zancen wani ka kaiwa wani, ka haɗa husuma a tsakanin mutane da kuma zama da mutum da zuciya biyu...". wa'azin da ke ta shi ta cikin radion kenan daga bakin wani Malami, kuma jiyo sallamar Ya Amadu daga waje yasa na rage sautin radiyon ina amsa sallamarsa, dan Yagana tuni ta tada sallar wadha sallar da bata wuceta, ni kuma kasancewar cikin jini shi yasa banyi ba domin nima bata wuceni, dan na koya daga wurin Gwaggona. "tsohuwar gidan nan sai ki dinga wani ƙunshe kanki a ɗaka kamar wadda taiwa kishiya laifi, aita kwaɗa sallama ba ki sa ni ba, ranar da wani ya shigo yayi wuff da turken awakinki naga ta tsiyar ƙunshe kai kamar daddawar ɗaƙa". maganar yake yana sanyo kansa cikin ɗakin, tun da yay maganar za'ai wuff da awaki Yagana ke tai masa gyaran murya, sarai yasan da shi ɗin ta ke, dan har ya zauna dariya yake ƙasa-ƙasa. na duƙa na
🏠