sai naji wata iska me zafi ta shura ta fuskata kamar yanda iska me ɗumi ke bin cikin iskar guguwa, kuma a hankali sai naji wani abu na ɗiga ajikina me zafi kamar ruwan da ke tafarfasa a cikin tukunya, tabbas akwai abin da ke shirin faruwa da ni, sai dai ban san menene ba tunda shi ɗan Adam ba ya sanin lokacin da masifar rayuwa zata kasance da shi, sai dai kawai ya tsinci faruwar musifar akansa. na zuƙi wata iska a hancina wadda nake jin ta banbata da irin iskar da nake shaƙa tun bayan zuwana duniya, Ya Rabb! kasa koma me ke shirin faruwa dani na iya tunkararsa, ka bani ikon ɗauka, ƙaddarata a rubuce ta ke kuma ban isa na guje ma ta ba, ya ubangiji ina roƙonka da ka juya mummunar ƙaddarar da zata sameni zuwa me kyau.
na ɗago daga tagumin da nayi na kalli Kulu da ke gefena, a cikin idanuwanta da ba su ƙarasa rufewa gaba ɗaya ba na hango tarin baccin da ke cikinsu, nai guntun murmushi dan da alama gyangyaɗi ma ta ke bata sa ni ba, sai na miƙe daga kan sallayar na ɗauko bargon rufarmu na shimfiɗa a ƙasa, na kamata zan kwantar da ita saita farka, mu ka haɗa ido nai ƴar dariya ina cewa,"gyangyaɗi fa kike, ki kwanta kinga dai bacci ba'a ɗaukar bashinsa". murmushin da ya tsaya iyakar leɓenta tayi,"ai tare muka raya daren da ke, kema zo ki kwanta ga idanunki nan duk a kumbure". "ki fara kwanciya nima yanzu zan kwanta". na faɗa ina gyara ɗaurin zanina. naji tace,"ina za ki hala gari ko gama wayewa bai ba, yara ma ga su can ina jiyo dabdalarsu ba su gama wucewa makaranta ba". "wurin Baba za ni". sai tayi saurin yunƙurawa ta miƙe zaune,"kar ki sa ke ki ba shi labarin mafarkin da ki kai, kin dai ji na faɗa miki". da sigar faɗa tayi min maganar, kuma naji na ɗauka, domin ina ganin girmanta, dan haka na bata amsa bayan sauya ra'ayina da cewar,"ba zan faɗa masa ba wallahi, ina so ne na koma makarantar asuba saboda na ƙarasa cike haddata, shi ne zanje nai ma Ya Amadu zancen tunda kinga yace gobe zai wuce da wuri". ta gyaɗa min kai,"hakan yayi kyau, Allah ya taimaka, sai kin dawo, ki kula da kanki, Allah ya tsare". "amin". na amsa ina nufar hanyar ƙofa, duk jikina yay sanyi kamar yanda na ke aiwatar da komai cikin sanyi tun mafarkin jiya da nayi.
a tsakar gida na tarar da Inna Amarya tana shimfiɗa tabarma, na saka takalmina ita kuma har ta kai kicin ta ɗauko botikin koko da ta dama, na ƙarasa da sauri na karɓa ina faɗin,"sannu da aiki Inna". "yauwa har an tashi?". "ehh Inna, yau kin kammala sanwa da wuri". nayi maganar ni da ita mu ka ƙaraso kan tabarmar ina ajiye botikin kokon ita kuma tana ajiye kofunan zuba kokon, ta ke ce min,"wallahi zan fita ne ina so naje jigawa, kin san Babanku kuma ba ya son tafiya da rana, shi yasa nayi himmar gama komai da wuri tun da ke yanzu ba zaman gidan kike ba balle na bar miki aikin". "aikuwa dai kinyi dabara, dan kina kaiwa sha biyu Baba zai ce ba za ki ba. Inna amma dai ba bikin gidan Umman Abbas za'ai ba ko?". "ba shi bane, ita ɗince dai ta kirani kuma ina tsammanin ba zai wuce akan bikin zamu tattauna ba". na ɗan ɓata fuska ina cewa,"Inna kin ce fa idan za kije zamu tafi tare". "kiyi haƙuri sai gaba idan zan koma tukunna...shiga ɗakin Zulai kice ta ba da kwanon abincinta, idan Adawiyya ta tashi ta fito kuci na ku, Sadiya ma tazo ta ɗau nata".
Na shiga falon Inna Zulai da sallama, du ka basa nan su na cikin ƙuryar ɗaki, daga can ɗin na jiyo muryar Adawiyya na faɗin,"Inna yanzu shikenan inaji ina gani sai ta rigani aure ban fara cimma muradina ba, kina ji fa abin da Baba yace wai yau zai ɗaura ma ta aure". Sadiya ta amshe da cewa,"ni gaba ɗaya Adawiyya na rasa gane kanki a al'amarin kishin da kike da Mairo, ina ce dama shi ɗan gidan Sarakan kike so kuma an shiga an fita kin gama samunsa, to mene kuma za ki ɗaga hankalinki akan batun aurenta tun da ba da shi za'ai ba, ke ba dama kika samu na goranta ma ta ba ta auri mutumin da yake kafiri a ada". Adawiyyan ta kuma cewa,"ni fa duk in da za'ace Mairo zata ji daɗi baso nake ba, shi ɗin fa da zata aura ba ƙananan mutane bane, babba ne shi ma dan ubansa shi ne major general na ƙasa ba ki ɗaya kamin yayi retire, wallahi inaji Ya Amadu na faɗar mahaukatan kuɗi ne da su, hatta gidan da suke zaune idan kaje zaka rantse ba'a ƙasar kake ba..me kike tunani idan Mairo ta koma rayuwar can gaba ɗaya?, wallahi sai tafi yanda ta ke ɗin nan kyan gani, kuma bada jimawa ba kiga ana haskata a gidan talabijin, ai ke kin gani ma a vediyon da Ya Amadu ya nuna mana san da tana kafira". a wannan karan da tayi shiru kuma Inna Zulai ce ta amshe da cewa,"Adawiyya idan kika kaini bango zan fita a lamarinki, na faɗa miki ki bar asarar hawayenki ki zuba ido ki gani idan auren zai tabbata, na faɗa miki muddin ina raye rayuwar yarinyar nan a wahala zata ƙare, bana faɗar abin da ba zan cika ba, ba kuma na tunkarar abin da ba zai kaini ga nasara ba, a wanne dalili zan zuba ido ina ganin su na ci gaba ni kuma rayuwar tawa ƴaƴan a dakushe kullum, ƴaƴana su ƙare a auren manomi, ai ba zai yiwu ba...wann