NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 117 of 223

shirin ɗaukar wata fansa, kuma su na kama da ɗaya mutumin da kika ce kar na je gunsa, duka sai na ji kun bani tsoro, hatta da ke ɗin da kika buɗen hannaye na isa zuwa gareki, amma a lokacin zuciyata wani zafi ta ke ji a kanki...dan haka sai na kama hannun Basma muka shiga dajin da gudu don kuɓuta daga cikinsa, saboda ganinku nake kamar za ku cutar dani ne koma kun cutar dani ɗin...sai dai ashe ba hanyar ɓullewa muke ɗauka ba cikinsa muka ƙara shigewa, daga bakin wata ƙatuwar bishiya sai naga Ya Kabiru a hannun wasu tsamurarrun mutane kayan jikinsu duka baƙaƙe, sun yi masa jina-jina yana miƙo min hannu a kan nazo, wai naje gare shi ba dan na cece shi ba sai dan ya mutu a ƙirjin matarsa, shi ne kawai na tafi da gudu kamin na ƙarasa suka fille masa kai". na ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, jikina banda kyarma babu abinda yake, sai kalmar na shiga uku da nake ambata. na sake ƙanƙame hannun Kulu tare da zare jikina daga nata, na ɗago kai na zubawa fuskarta kallo, idan ba wai kallon rashin fahimta nake ma ta ba, fuskarta na nuna firgici sosai, firgicin da ta ke son ɓoyewa, kuma ta yanda wani abu ya wuce ta maƙogoronta na tabbatar da ita ma ta shiga ruɗanin da na shiga, fararan idanuwan nan nata sun ƙara yin haske kamar fitila, yanayin yanda ta ke kallona na yin nuni da irin tasirin nazarinta akaina ko kuma labarin mafarkin da na bata. sai ta kwanto da kaina saman ƙirjinta, ta ƙarasa zame ɗan kwalin kaina, ta ɗora hannunta saman gashina tana shafawa, muryarta a hankali ta fara magana, cikin muryar nan tata da sau tari na kanji ina samun wata iriyar nutsuwa da jinta. "dukkan wani mafarki ba gaskiya bane sharrin shaiɗan ne, dan haka ki kwantar da hankalinki babu abin da zai faru a cikinsa sai alkhairi insha'Allahu". "amma fa Kulu har da Gwaggona na gani aciki, sannan kuma ki ce min wannan mafarkin ba zai zama gaskiya ba, ki tashi dan Allah muje mu sami Baba a ɗaki, wata ƙila shi ya iya gane me hakan ke nufi". ina jin san da ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya da hucin zafin numfashinta ya sauka ajikina. tabbas mafarki ƙarya ne, to amma ta yarda da maganar Bella da ta taɓa ce musu, "duk da mafarki ba gaskiya bane, amma wani lokacin yana juyewa tamkar madubi ya iya nuna abin da zai kasance a zahirin". tabbas kuma ta shaida hakan, domin ta gani akan mafarkinsu da ya zama iri guda da Aaliya, ga shi a yauma mafarkin Mairon na nema ya haska ma ta madubin zahirinta. "ki bini a karatun da zanyi". abunda ta faɗa kenan, sai kuma bakinta ya kama da ayatul kuriyyu, na shiga bin karatun bakina na rawa kalmomin na harɗe min, dan har yanzu tsoro bai bar jikina ba. sai da muka kai ƙarshen suratul falaƙ, sai naji tsoron ya bar jikina, nutsuwata ta fara dawowa, firgicin da nake ciki yabi ta iska, na sauke ajiyar zuciya, sannan Kulu ta umarceni da na sauko muje muyi alwala muyi sallah, insha'Allahu koma wane irin sharri ne ubangiji ya juya shi ya zama alkhairi, ba mu miƙe akan sallayarmu ba har sai da muka idar da sallar asuba, sai dai har a lokacin mafarkin bai bar dawo min ba, kuma cike nake da son sanin ma'anar da ke cikinsa, dan haka kawai ba zanyi wannan mummunan mafarkin ba, dole akwai wata ayar a cikinsa da ta ke zuwa gareni, musamman kalmar mata da naji Ya Kabiru ya ambata. Kulu kuwa safiyar sai ta sakance ma ta mara daɗi, domin tun a mafarkin Mairo na jiya zuciyarta ta shiga cikin taraddadi, tabbas a yanzu, kuma a yau tasan anzo kan gaɓar, a yau ba sai gobe ba Gaskiyar da suke ta binnewa a matsayin sirri zata bayyana, a yau ba sai gobe ba Mairo zata san gaskiyar komai, domin shi lokaci ba ya wasa da kansa, yana bada mitsitsiyar dama ne ga me shirin yin wani tsarin aiki acikinsa. bayyanar gaskiyar ba ita ce tashin hankalinta ba, Aaliyah!Aaliyah!!! ita ce zata zame ma ta matsala, ita ce zata zame ma ta tsaiko, ita ce zata wargatsa ma ta duk shirin da ta tsara. ta sani! ta san wace Aaliyah! ta san daga lokacin da suka haɗu zata saka ƙafa tayi fatali da wannan rufaffiyar kwalabar da suka rufe a tsakaninsu, idan ma har fashewar da kwalabar tayi bai yi ma ta zata iya sa ƙafa ta ƙarasa mitstsiketa ta yanda wannan alƙawarin nasu zai karye a lokacin, alƙawarin nan da suka ɗaukarwa juna kamin rabewarsu. *_ME KUKE TUNANI, ME KUKE TSAMMANI?_* *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *31)* tun bayan da na idar da sallar asuba zuciyata ke faɗamin tabbas mafarkin da nayi gaskiya ne kuma zanga gaskiyar ta bayyana a zahiri nan ba da jimawa ba. a wayewar garin yau ina ji tamkar an buɗe min kundin rayuwata ne ina karanta haƙiƙanin abin da zai yi tasiri akaina a yau.
🏠