ɗaga min hankali, yana sosa zuciyata, yana hanani natsuwa, idan ba so kike zuciyata ta buga ba to ki faɗa min me akai miki kike kuka?". Muryata ta fito cikin sheƙar kuka ina fizgar numfashi nace,"aure Baba zai min". Maganar tata ta doka tsalle a zuciyar Kulu, mamaki ya bayyana ƙarara a fuskarta, tsoro kuma da fargaba suka cika zuciyarta, wa Malam zai aurawa ƴarta ba ta sa ni ba?, bai kuma sanar da ita ba?, ko dai ƙarya ta ke faɗa ma ta? ko kuma taji maganar tasa ba dai-dai ba?. gudun kar da Mairon ta gane halin da ta shige tai saurin ture komai daga ranta, ta lallasheta da bata haƙuri har ta samu zuciyarta ta sauko ta bar yin kukan. kuma daga hakan sai bacci ya ɗauketa saboda karatun qur'anin da Kulu ke karanto ma ta a cikin kunne. sai da ta tabbata baccin Mairon yayi nisa, sannan ta sauka daga gadon ta fita don zuwa ɗakin Malam, sai dai tana fitowar ne kuma tai kiciɓis da wucewar wannan mutumin da ke lulluɓe jikinsa da daddare, wanda ko a daren jiya taga gimlawar inuwarsa ta ƙasan ƙofar ɗaki, da alama kuma ɗakin zai shigo sai bai sami damar hakan ba, saboda ƙofin da tayi na hana idonsa ganin komai. ta sani shi ne silar ciwon ƙafar Gwaggo, dan rana ta ƙarshe da ya shigo ɗakin ya fita da ta zo ta tarar da syringe a ƙasa wanda aka jefar saboda tsoron tahowar me shigowa ɗakin, ta ɗaga syringe ɗin ta duba na allurar botulinum toxin ne, gubar da zata iya kashe duk al'ummar ƙasar da akaiwa feshinta, ko da ta saka ihu kowa ya fito a lokacin babu wanda aka gani.
daga baya zuciyarta ta saƙa ma ta koma wanene a cikin gidan nan yake, wanda ya ƙware a ɓadda kama, ashe zuciyarta ba zargi ta ke ba, hakanne, don gashi kuwa yau idanunta sun gane ma ta ko wane, dan taga fuskar a san da ta fito lokacin da ake ƙoƙarin lulluɓe kai. zuciyarta ta tsorata da abin da zai iya faruwa, saboda haka ta haƙura da maganar da zata yi da Malam a daren yau, ta jira gobe idan Allah ya kaimu, tana gudun karta fita yazo ya cutar ma ta da ƴa, cutarwa da ba zata bari, dan ko ta Gwaggonma ba tayi shiru ta ƙyale bane, kwanaki ashirin ne kacal da rasuwar, tana jiran mutuwar ta sake barin jikin kowa kamin ta tona asirinsa, kuma lokacin da SIRRIN da ya jima a ƁOYE zai fito fili. dan haka sai ta mayar da ƙofar ta rufe ta dawo ciki, ta kwanta ta rungomo ƴarta jikinta tsam, amma duk da haka tsoro bai bar ranta ba. kuma a cikin baccin nata ne taji wata magana da bata san amon sautin waye ba tana faɗin,"ni ban taɓa tsara abu ya tafi ba a yanda nake so ba, shirina na gaba akan Kabiru da ɗan'uwansa ne, ina so a gobe ku sace Kabiru, kuma ku buƙaci adadin kuɗaɗen da zan lissafa muku, sannan kubi bayan ɗan'uwansa ku haddasa hatsarin da kowa ma zai rasa ransa, babu ruwana da sauran rayukan in har shi ɗin ya mutu...bana aikin asiri, da ƙwaƙwalwata nake amfani, a tafin hannuna nake zana duk wata manufa tawa, na kuma juya yanda nake son duk wani tsarina ya kasance, saboda haka a gobe wannan aikin ya gudana". a firgice Kulu ta farka, dai-dai lokacin da ita ma Mairo ta farka a firgicen, dukansu salati su ke tashin hankali bayyane a fuskokinsu. sai da Kulu ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya sannan hankalinta ya sauka akan Mairo, wacce ta takure, jikinta sai rawa yake, ga wata uwar zufa da ta haɗa. "menene Mairo?". ta tambayeta tana me yi ma ta rumfa, ba tare da ta fasa bin kowacce kusurwa ta ɗakin da kallo ba tana biyo adu'oi a bakinta. "mafarki nayi". "mafarki kuma? me kika gani a cikin mafarki?". na ɗago na dubi Kulun a tsorace sannan nace,"wai acikin wani jeji me duhu an ɗauremu ni da Basma, ga kuma wata ƙatuwar rijiya me zurfin gaske a kusa damu, wata Mata da ban san kowa ce ba tazo tana jawomu zata jefamu ciki sai ƙyalƙyala dariya ta ke, tana faɗin wai a tsarin rayuwarta bata lissafa da wani abu da zai shige ma ta gaba, tana dab da hankaɗamu cikin rijiyar sai kawai Gwaggona ta bayyana acikin wani irin haske me kyau, tana kuka tana roƙonta akan karta aikata mana hakan ta duba maraicinmu, Gwaggona na cewa kada na bari ta jefamu na sami ƙarfin da zan ƙwaci kanmu, nai gaggawar zuwa na ƙwaci Ya Kabiru daga mummuna hatsarin da ke tunkararsu kuma duk ata sanadin wannan matar, kar na bari, kar na bari komai ya samemu. daga faɗin haka kuma sai Gwaggon ta ɓace, muka nemeta muka rasa, shi ne Basma ta gartsawa Matar cizo a hannu ba shiri ta sakemu, maimakon mu faɗa rijiyar sai ita ta faɗa ciki...kuma kema sai ga ki kinzo mana kina murmushi da dukkan nuna wata ƙauna ta uwa a garemu, sai dai kina kama hannuna ina fizgewa ina tureki akan sai kin barni kin bar rayuwata, shi ne sai wani farin mutum ma yazo, rabin jikinsa haske rabinsa duhu, yana cewa na taho gare shi, amma sai kika ce min a'a kar da naje, shi ɗin ba abin so bane, shi ɗin mutum ne me hatsari, shi kuma wani saurayi da ke zaune kan wata kujera ya harɗe ƙafafunsa yana kallonmu da wani murmushi me cike da tarin ma'anoni da yawa, yana ta wani abu kamar basarake, bini bini sai yaja shati da yatsu biyu a goshinsa, yana murza karan hancinsa kamar me