ɓar musuluncinsa ba, nafi yarda da yay amfani da siyasa ne don kawai Baba ya bashi ni ɗin, domin ya rama abinda nayi masa a waccan ranar, ga Baban kuma ya amince masa.
hawaye suka cika min idanuna, kewar Gwaggona da mararin kasancewarta a wannan lokacin ya kamani, wata ƙila da ta na raye duk ba za azo kan wannan gaɓar ba, ba za aiwa ƴarta abunda taƙi jini ba wato auren wuri, ba za'a aurawa ƴarta wanda bata so ba, ba kuma za'a dakushewa ƴarta karatun bokon da ta cimma burinta akansa ba, dama na sa ni! na kuma ji a jikina tun a ranar da Gwaggona ta rasu wani shafi na ƙaddarar rayuwata ya buɗe. na ɗago da idona a hankali na dubi Baba da idanuwansa ke akaina ƙyam, ko ban shiga zuciyarsa ba amma nasan babu komai acikinta fa ce tsoro da fargabar amsar da zan bashi, kuma ni kaina ɗin ina jin rashin kyautuwar abinda zanyi, to amma me?, alokaci guda sai naji duka ɓarika biyu na zuciyata sun sauya ra'ayi, sun sauya ƙin amincewar da nake shirin yi zuwa yarda, domin idan har naƙi amincewa Baba maganar auren nan tamkar nayi butulci ne a gare shi, sannan kuma shi ma kansa Emanuel ɗin naji ina jin tausayinsa, haƙiƙa ko bana sonsa zan iya amince masa saboda alkhairin da yay mana a sanda ake zaman makokin Gwaggo.
ba wannan ba ma tukunna, ni yanzu a duniyata ina jin zan iya mallaka komai nawa ga duk wanda yay adu'a ga Gwaggona, balle shi da Baba ya faɗa min ya ɗau tsawon sati guda yana ma ta adu'a, kuma har ya bada kuɗi akai sadaƙa ladan ya isa gareta, Gwaggona da bani da kamarta duk faɗin duniya. bayan wannan ma! Allah ya sani tun ban mallaki hankalina ba nayi alƙawarin babu abin da Babana zai nema daga gareni na kasa yi masa, ko da kuwa rayuwata yace na sadaukar, Allah ya sani na jima ina jiran wannan rana da Baba zai umarceni da auren mijin da ya zaɓa min na amince masa kai tsaye, dan ta hakanne kaɗai zan iya rama masa da irin sadaukarwar da yay a gareni. zan iya yin komai dan ganin na wanzar masa da farinciki, Baban nan nawa da nake mutuwar so, Baban nan da ya sha wahala akanmu a rayuwarsa, ba don komai, sai dan ganin rayuwarmu ta inganta, Babana dai! Mahaifina! Mahaifina da ya sadaukar da ƙodarsa guda ɗaya aka saka min a san da nake shekara goma, Babana da ya ƙarar da komai nasa a san da za'ai min aikin ƙoda, Baban da ya sha wahalar jinya ta sanadin bada ƙodarsa da yay a gareni, wanda har sai da muka fitar da rai da shi, to akan me yanzu zan butulce masa kan wannan ƴar ƙanƙanuwar buƙatar tasa?. to ni kuwa ko da wane nufi ne ma Al'mustapha zai aureni ni kam na amince, ni ba butulu bace, dan haka a yau ko da raina ne Baba yace na bayar wallahi zan bayar in har zaiji daɗin hakan. Baba ya katse tunani, maganar tasa ta shigo cikin kaina da wani irin dagargaza zuciya, nasa hannu na share hawayena, sannan na ɗago na dube shi da murmushi nace masa,"na amince Baba, na amince zan auri Al-Mustapha in har hakan shi ne muradinka, kuma hakan ba zaisa ka saɓa alƙawarin da ka ɗauka ba, na amince zan zauna da shi a matsayin mijina bisa turbar da ka ɗorani akai, Baba na maka alƙawarin zan koyawa zuciyata sonsa idan har hakan shi ne zai faranta maka, ko babu komai nasan ba zan taɓa ganin ba daidai ba idan har na bi umarninka". nai shiru saboda kukan da ya danne sauran maganata. Baba yay murmushi sannan yace,"matso nan gabana Mairo". na rarrafa na ƙarasa gabansa, ya kamo duka hannayena ya riƙe a nasa yace,"na gode Mairo, na gode Allah yayi miki albarka ya saka miki da alkhairi...kuma ina mai tabbatar miki ba za ki taɓa wulaƙanta a hannun wannan yaron ba, ni ba magini bane saboda haka ban duba filin wurin ba, amma ina da yaƙinin Al-Mustapha ba zai cutar da ke ba. a gobe insha'Allahu zan ɗaura miki aure da Al-Mustapha, fatana ɗaya a gidan aurenki kici gaba da ginuwa akan wannan kyakykyawan halin dana sanki da shi, ki zama tamkar mahaifiyarki, mace me gaskiya da amana, Mace me haƙuri, juriya, kawaici da ƙyamar abin hannun wani...Allah yayi miki albarka ya kuma jiƙan mahaifiyarki". na amsa masa da,"amin Babana". daga haka zaman namu ya watse, Baba yace ba zan tafi gidan Yagana ba anan zan kwana tun da dare yayi, ba haka naso ba, dan ko kaɗan yanzu bana son kwanan ɗakin Gwaggo babu ita. lokacin da nake fitowa daga ɗakin Baba, sai naga Inna Zulai da Adawiyya sun bar wurin da sauri sunyi ɗaki, sun ji komai, dan alama ta nuna ba tun yanzu suke laɓe a wurin ba, nai wani guntun murmushi kawai ina girgiza kaina. ko sanda na isa ɗaki na tarar har Kulu ta kwanta, na tura ƙofa na rufe sannan na wuce na hau kan gadon ƙarfen Gwaggona, na kwanta daga bayan Kulu, wacce idona ke haska min tamkar Gwaggona. na cure a wuri guda, tun da na kwanta babu abin da nake banda hawaye, tun sautin kukan da na ke bai fita har ya fara fitowa a hankali. maganar Kulu daga kaina naji ta ce,"kukan me kike?". nai ma ta shiru har sai da ta ƙara yin magana. "tambayarki nake kukan me kike?". sai kawai na tashi zaune na rungumeta ina ci gaba da shashsheƙar kuka, tasa hannayenta ta kewayeni tana faɗin,"kukanki yana