man da kansa yace in har da gaske wurinsa yazo to a shigo da shi cikin masallacin, ya zube gwiwonsa a gaban Liman ɗin, ya duƙar da kansa ƙasa, ya shaida masa cewa yana so ya shiga cikin addinin musulunci, ba wai don saboda wani ya tursasa shi ba, ko kuma don bin umarnin wani, sai don saboda ra'ayin kansa, ra'ayin zuciyarsa, saboda kwaɗayin wannan ni'imar da hasken da Amadu ya jima yana masa nasiha akansu. saboda haka a faɗa masa adadin kuɗin da zai biya ko da ya kai nawa ne, idan ma da abin da a keso bayan kuɗi a faɗa masa duka zai bayar, shi ma yana so ayau ya shiga cikin wannan addinin da tun wayonsa yaji ana faɗin shi ne addinin gaskiya. Mairo bayan ubangiji, sannan kuma da Liman da babu shi anan, daga Innarki har Amadu shaida ne a yanzu Emanuel ba arne bane musulmi ne, ya zama cikakken musulmi tun a daren jiya kafin sallar isha'i, ya amsa kalmar la'ila ha'illahu har ƙarshenta, kuma ya amsa sunansa na Al-Mustapha. haƙiƙa ubangiji me iko ne abisa dukkan komai, Emanuel ya ƙara amsa cewar zai shiga musulunci ne tun a sanda imani ya ratsa zuciyarsa ata dalilin kalamai na wa'azi da Liman yay masa masu ratsa zuciya da ɓargon jiki. Liman ya faɗa masa musuluncin ba kasuwanci bane, kuma ba'a biyan ko sisi idan za'a shiga addinin musulunci, saboda Allah maɗaukakin sarki ya halicci dukkan halittu ne domin su bauta masa, kuma ya sawwaƙe musu abin da zai taimaka musu na arziƙinsa. kuma Ubangiji da kansa ya faɗa a littafinsa me tsarki, surah ta (51) aya ta (56-58) yake cewa ,"(56) Kuma ban halitta aljanu da mutane ba sai domin su bauta mani. (57) Bana nufin wani arziƙi daga gare su, kuma bana nufin su yi min hidimar ciyar da ni. (58) Lallai Allah shi ne kaɗai mai azurtawa, me ikon yi, me gafara. saboda haka babu abin da ubangiji ke buƙata daga gareka Emanuel fa ce ka amsa kalmar Shahada, ka kuma yi mubaya'a akan ƙa'idar,"annama ilahukum wahid". domin akan wannan ƙa'idar aka gina addinin musulunci. ka shaida babu wani Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah, Kuma Annabi Muhammadu Manzonsa ne, Waɗannan kalmomin su ne ƙofar shiga musulunci, kuma rukuni mafi girma, kuma ba a yin hukunci da musuluncin mutum sai yay furuci da su, da kuma yin aiki da abin da suka ƙunsa, daga sannane ka tashi daga kafiri ka koma musulmi Emanuel. Liman ya ɗau alƙur'ani yay masa nuni da shi yace Emanuel wannan shi ne zancen Allah, littafin da aka aiko Manzonmu Annabi Muhammadu (S.A.W) da shi. ka samu damar yin riƙo da shi domin ka tsira daga wannan narkon azabar da zaka riska a ranar alƙiyama in har ka mutu kana kafiri. a cikinsa zancen Allah yake gaba ɗaya, Emanuel ba don san kanmu ko kuma mu yaudari zuciyarka ba, amma babu wani addini na gaskiya sai addinin musulunci, kuma babu wata kyakykyawar hanya saita bin ubangiji, in har kabi Allah, kayi koyi da koyarwar Manzon Allah, Ka yarda ba zaka ƙara yin shirka ga Allah ba, ka riƙe gaskiya da amana, ka yarda ba zaka aikata zina ba, kiyaye jinka da ganinka daga haramun, ka yarda da haramcin sata, ka tsare kanka daga saɓawa ubangiji, to haƙiƙa ka rabauta daga dukkan wani narko na azabar ubangiji. domin haƙiƙa Ubangiji ya tanadi gidaje guda biyu wuta da Aljannah, ya kuma yi alƙawarin cikasu da mutane, za'a cika Aljannah da mutanen da suka riƙi gaskiya suka tashi a tafarkin Manzon Allah, ita kuma wuta za'a cikata ne da mutanen da suka ɓata, suka yi watsi da gaskiyar da ma'aikin Allah yazo mana da ita. Dan haka Emanuel idan ka shirya zaka karɓi kalmar La'ilaha'illah Muhammadur-Rasulillah. ni kuma zan amsa mubaya'arka, zan roƙa maka gafarar ubangiji domin haƙiƙa Allah mai gafara ne kuma me jin ƙai.
a Wannan lokacin duk wanda ya kalli Emanuel sai ya hangi irin raunin da zuciyarsa tayi, jikinsa gaba ɗaya yay sanyi saboda tasirin waɗan nan kalamai, ya shiga faɗar kalmar da Liman ya umarce shi ya maimaita bayan ya faɗa, Mairo sai da nayi hawaye, daren jiya tare muka yi sallar isha'i da Al-Mustapha a masallaci, kuma yau da asuba ma ni nasa Amadu ya tashe shi, ya roƙi Amadu akan ya dawo da sauri domin ya fara masa bitar karatun alƙur'ani...Mairo ban amsawa Al-Mustapha zan aura masa ke ba sai bayan ya musulunta, kuma hakan ba yana nufin zan tursasa miki ba dan shi ma bai ƙara tunkarata da maganar ba, sai dai a yau da safe nasa Amadu ya kira min shi na shaida masa na basa ke, idan ya shirya ya fito zan ɗaura muku aure, amma duk da haka ki faɗa min ra'ayinki dan ba zan miki dole ba, ba zan tauye miki hakki ba, alƙawarin da na ɗauka kawai nake tsoron saɓawa, dan ban san wane irin hukunci ubangiji zai min ba".
shirun dai na yi ba shiru ne na haka kawai ba, wani irin shiru ne da nake jin guguwa na kaɗawa acikinsa, shirun da acikinsa na kasa zuƙar numfashi me daɗi, tun a sanda Baba ya shiga kora min wannan jawabin nayi mutuwar zaune, gaba ɗaya abin jinsa na ke tamkar almara, yanzu ba maganar auren ce abin mamakina ba, mamakin yana ga musuluntar da Emanuel yayi, kuma tsoro sai ya kamani, naji a zuciyata ban yarda da wannan tuban nasa ba, ban kuma yarda da kar