ya sauka a garin nan, kuma da Amadu ya shaida masa yanda muke gudanar da zaman makoki, haka ya kama hotel ya zauna a can shi ma yace har sai an gama zama sannan zai koma gida. a washe garin sadaƙar ɗaya yaron nan da ya tashi zuwa sai ganinsa mu kai da lodin kayan abinci, shinkafa babu ƴar hausa buhu goma haka ya ajiye ƴar gwamnati, banda galolin mai da duk sauran kayan abinci dai da kika san anaci, ruwan jarka na faro kuwa da kika ga kowa nasha mota guda haka yasa aka ajiye a ƙofar gidan nan, ya ɗauki maƙudan kuɗi naira dubu ɗari da hamsin ya bawa Amadu yace a dinga cefane da su, na karɓa nace masa a'a ba zamu karɓa ba, ko waɗancan ma dan ya riga ya kawo ne ba tare da yayi shawara damu ba, kuma ba'a maida hannun kyauta baya, amma da duka za'a haɗa a ba shi, dan haka ya riƙe kuɗinsa an gode. duk yanda nayi da shi ya karɓa yaƙi yace shi bai bayar dan wai mu yi bikin mutuwa irin nasu ba, ya tambaya ne idan musulmi ya mutu kyautar me ake musu akace ba'a kyauta sai dai a bada sadaƙa, dan haka shi duk abunda ya bayar ya bayar da shi sadaƙa ne, kuma wannan kuɗin idanma ba zamu riƙe ba ayiwa Gwaggo sadaƙa da su. ko da yaushe yaron nan yana tare damu a wurin zaman makoki tun daga safe har dare sannan yake mana sallama, tashi sallah ne kawai yake rabamu da shi, kuma haka yayta wannan zaman har akai sadaƙar bakwai, a kullum tambayata yake wace iriyar adu'a muke yiwa mamacinmu, na faɗa masa, kuma tun daga wannan rana kullum sai yayi kyawawan adu'oi masu tarin yawa wa Gwaggonki, ranar sadaƙar bakwai har kuka sai da ya sakani, yace yana tausaya miki ne kina ƴar ƙarama da ke kin rasa mahaifiyarki, kuma an faɗa masa dalilin ciwonta har da silar rashinki a kusa da ita, kuma ba kowa yay sanadin tsayin ciwon nata ba illa shi, shi ma yana da babban kamaso a rasa mahaifiyarki da kika yi, dan Allah na roƙeki ki yafe masa, duk abin da yay bai aikata miki da son zuciya ba, sai ma dan gudun kada ki tagayyara idan yasa cigiyarki, kidnapers za su iya yin ƙarya su ƙarɓeki. amma ki yafe masa, yana kwatantawa ne akansa ranar da aka ce shi ma babu tasa uwar ko uban ya zai yi. ya daɗe a ranar da zai tafi yana cewa dan Allah nace kiyi haƙuri, har Amadu yace ya tsaya a kiraki yace a'a ace yana miki ta'aziyya kawai, ba zai iya haɗa ido da ke ba dan aduniyarki babu wanda kika tsana sama da shi yanzu, kuma za ki iya kashe shi dan kin faɗa masa hakan.
bayan wannan a washe gari sai gashi ya turo min mahaifinsa da maganar wai yana so ya aureki, mahaifinsa ya rantse min yay alƙawarin ba za su cutar da ke ba, kuma ba zasu rabaki da addininki ba, banbancin addini ba zai sa su ƙyamaceki ba, na faɗa masa cewar addininmu ya haramta auren musulma mace da kuma namiji kafiri, dan haka ba zan iya bawa ɗansa auren ƴata ba. ya tafi cikin rashin jin daɗi, amma a washe gari sai ga Emanuel ɗin da kansa yazo, a jiya kenan, har hawaye sai dai yay min akan magiyar aurenki, ban yarda da irin tsananin son da yake ikirarin yana miki har cikin zuciyarsa ba sai da na kalli ƙwayar idonsa, ya faɗa min soyayyar ba wai ta yanzu bace, tun ta sanda ya haɗu da ke ne, kuma inda yayi niyyar cutar da ke da tuni ya cutar da ke, dan zuciyarsa ta daɗe tana ingizashi akan ya aikata wasu abubuwa marasa kyau a gareki amma ya dinƙa kwaɓar zuciyarsa saboda son da yake miki na gaskiya ne. sai dai duk ta yanda naso na fahimtar da shi rashin yiwuwar abin ya gaza fahimtata, yace shi kawai bana so na basa ke ne, har wata ƴar'uwarsa ya kira min a waya dan naji wace ita, arniya ce ita amma mijinta musulmi ne, saboda haka idan har auren waɗan can zai kasance kuma na ku zai kasance. da ƙyar da ƙyar yaron nan ya fahimceni daga ƙarshe, san da ya miƙe ya tafi ba kiji yanda zuciyata ta tsinke ba, da ace addininmu bai haramta auren Kafiri da Musulma ba da babu abin da zai hanani aura masa ke, ba don komai ba sai dan karamcinsa a garemu, mutumin da ya zauna tsawon sati guda acikinmu ba ƙyamatarmu talakawa ne ballantana addininmu, abin da muka ci shi yake ci, kuma kullum adu'a yake ga mamacinmu, ta ya zaka ƙi karɓar buƙatarsa ta alkhairi a gareka?.
ba wannan ba Mairo, wallahi ban rufa daga tunanin da na faɗa ba sai ga yaron nan ya dawo yana shaida min idan har zan aura masa ke to tabbas zai musulunta, nace masa a'a ni ban yarda ba, sai dai ya musulunta saboda Allah ba dan ke ba, yay min rantsuwa iya rantsuwa da gaske yake yi zai shiga addininmu idan har zai sameki, saboda ba zai iya rayuwa ba idan har babu ke a tare da shi, nace ni ba zan mallaka masa ƴata ba saboda zai musulunta dan ita, nafi so ya musulunta saboda Allah, ni kuma idan har ya musulunta dan Allah nayi masa alƙawarin zan aura masa ke a washe garin ranar, ta yanda zuciyarsa ba zata sauya shawara ba anan gaba bayan ya aure kin. bai ƙara cewa da ni komai ba yay shiru, anan bakin masallaci muka bar shi muka shiga sallar magriba, har muka fito yana nan a zaune, ya kira Amadu yace yazo ya kai shi wajen limamin masallaci, Amadu shi yay masa jagoranci zuwa gaban Malam Liman, Li