NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 111 of 223

in ƙur'anin dana karanta, sai ce min tayi,"ki ce ash hadu". a dole tasa nayi ƴar ƙaramar dariya, haka ta ke min yanzu ko alwala zanyi sai tace ki faɗi kalmar shiga musulunci. saboda na ƙara kunnota nace,"Don't worry Hajiya Yagana i will say it". aiko kamar jira ta ke na rufe baki taja tsaki, ta hau sababi, ta bani dariya sose, da yake yanzu gaba ɗaya ma da turanci muke magana da Ya Kabiru, to idan zamu yi zaman awa guda agabanta muna magana, tai ta jan tsaki tana mitar an isheta da ɗan banzan yaren da bana uwa da uba ba. a hanya muna tafiya Adawiyya ke ƙarasa min zancen da ba ta ida ba a ɗazu, wai Suhail yace shi yana so ya auri wadda ta fito daga gidanmu, kuma gashi ba zai iya aurena ba, saboda haka idan har ita ta amince masa zai aureta. ba ƙaramin daɗi naji ba da jin zancen, har na ɗora hannuna a kafaɗarta ina zolayarta da cewa,"wa ya ga gimbiya Adawiyya...dilla ki amince masa mu raƙarƙashe, kinga shikenan mu ma mun zama jinin sarauta". tai min wani banzan kallo tana cewa,"Allah raba gatari da saran shuka, me zanyi da mutum me ɗaukar maganar mutane". nayi murmushi ina kama hannunta nace,"kema dai Adawiyya ba ki so gaskiya ba, magana ta Allah who ever gets in to the situation am in dole mutane su zarge shi, balle ni da nake mace, shi yasa nace miki na toshe kunne na da duk abinda mutane zasu ce akaina...amma dan Allah ki bar batun wai ba za ki amincewa aurensa ba, Suhail mutumin ƙwarai ne, kuma gidansu ma mutanen ƙwarai". kamar ba zata ce min komai ba, sai kuma ta numfasa tace,"naji". da haka muka ƙarasa gida inata tsokanarta, ita kuma sai ciccin magani ta ke. ɗakin Gwaggo da ya koma ɗakin Kulu a yanzu na shiga, tana zaune da hisnul muslim a hannu tana karantawa, nayi sallama na shiga ta amsa min tana hararata. ina murmushin da ya bayyanar da dukkan haƙorana na ƙarasa gareta ina rugumeta nace,"am sorry my second Gwaggo, Allah yau aiki mukaiwa Yagana shi yasa ba ki kalleni ba tun safe". duk da haka taƙi ɗago da kai ita alalla tana fushi, sai na karɓe hisnul muslim ɗin na ajiye shi na kwantar da kaina bisa cinyarta, na shagwaɓe fuska ina kama kunnena nace,"Am so sorry, Allah nima tun ɗazu hankalina na kanki". sai tayi murmushi tana kallona, ta shafo kumatuna tana cewa,"ai idan nayi fushi da ke ko duka jama'ar kano za ki tara su tayaki bani haƙuri ba zan haƙura ba...shikenan haka akeyi fisabilillahi sai kusa na ƙara zama marainiya, ita Basma na ma ta uzurin makaranta, amma ke kin tattara kin gudu wurin Yagana kin barni ni ɗaya a ɗaki kamar mayya, bayan sarai kin san bani da kowa a gidan nan yanzu sai ke, ke kaɗai nake gani naji daɗi, kuma kece ke ɗebin kewar Yaya, dan Allah karki kuma yini baki zo na ganki naji sanyi a zuciyata ba, wallah bana samun nutsuwa idan ba kya cikin gidan nan". nayi wani fari da ido nace,"to Gwaggo 2". sai taja hancina tana gajeriyar dariya, sannan muka shiga hira, tana bani labarin taji Baba ɗazu yana faɗa akan ba zata bar gidan nan ba, amma bata san a cikin Inna Amarya da Inna Zulai wa yaje masa da zancen ba, wai sun gaji da zama da mahaukaciya tunda dama dan Gwaggo ta ke zaune to yanzu saita bar gidan tun da babu Gwaggon, Baban yace karsu ƙara ce ma ta mahaukaciya, da lafiyarta, zanen ƙaddara ne ya maida ita hakan, kuma zamanta a gidan nan babu fashi, sai dai idan bayan ransa. tausayinta ya kamani, nayi ɗan jim kafin nace,"to kema Kulu ki koma gidanku mana in dai kin san inda ƴan'uwanki suke". sai naga tayi murmushi me kama da ciwo kan tace,"lokacin hakan yana tunkaro ni, na kusa nan bada jimawa ba". Muryar Ya Kabiru ta shiga kunnuwanmu a sanda ya ɗaga labulen ɗakin, muka kai dubanmu gare shi, shi ma na lura yanzu yasan Kulu na magana, tun da bata shayin yi agabansa kuma shi ma babu mamakin hakan a tare da shi, muryata a ƙasa nace,"da ɗaya bayan ɗaya kowa na gidan nan sai ya gano gaskiyar kina magana". ƙaramar dariya ta rakani, ni kuma na miƙe na isa bakin ƙofar da Ya Kabiru ke tsaye, na miƙa hannu na amsa ledar kaza da youguht ɗin da ya siyo min, na ɗago kai zan masa godiya ya matse hancina yaja, nai ƴar ƙara ina kama hannunsa zan cire daga hancin nawa. sai ya kawo goshinsa ya ɗan doki nawa goshin,"kin wani ƙunshe a gidan Yagana, kin bar mutane anan da kewarki". nace da shi,"to ba sai ka bi sahuna ba Ya Kabiru, ai sai kaje kaga ko lafiya tun da kasan safiya nayi nake tahowa nan". yace,"tabɗi! Yaganar nace min me hannun ɓera zanje gidanta, ai ba zan sake komawa ba saita neme ni da kanta". na ƙyalƙyale da dariya na juya ina bawa Kulu labarin diramar Ya Kabiru da Yagana, ya siyo ma ta dambun nama ya kai ma ta ya ɗiba sai cewa tai yaje da halinsa, ita bata san hannun ɓera gare shi ba da bata ce ya siyo ma ta ba, amma ai gwara da ya nuna ma ta halin ɓerayen da yake da shi, gaba ta dinga kaffa-kaffa da kayanta idan ya shigo gidan, yanzuma dan Allah ya tashi ya fita kafin ta nemi kayan jama'ar da aka bata ajiya ta rasa, ya barta da tsilla tsilla, ita duk ta ƙagu ma ya koma ƙauyen da ya fito. Da daddare baya
🏠