NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 110 of 223

ga lokacin da Emanuel ya bugeni har lokacin da yaje gidan ya sameni, nima na basu labarin abin da ya faru damu a can dajin da aka kaimu, Inna Amarya ta dage akan akaini asibiti a dubani, muka je asibitin Malam Aminu kano akai min gwaje-gwaje, aka tabbatar musu da babu abin da ya taɓa budurcina, babu abin da ya sami lafiyata, sai a sannane kowa nutsuwarsa akaina ta gama dawowa. sai dai a lokacin na shiga wani babban mamaki na tsintar rashin jin daɗin sakamakon a fuskar Inna Amarya, da har ta dage ta tubure akan sai an ƙara gwadawa ko kuma aje wani asibitin, a haka har saida muka je asibiti uku, duk sakamako ɗaya su ke badawa, alamun rashin jin daɗin bayanai ya fito ɓaro ɓaro a saman fuskarta da kuma yanda duk ta ke neman ta rikice, na shiga zuzzurfan tunani akan hakan, dan hatta a maganar da ta faɗa min a ranar uku me ɗaure kai ce, tana kuka ta ke ce min,"ta wani ɓangaren sai naji dama ba'a ganki ba Mairo, saboda ina gudun yanda mutane za su yi ta kallonki, da rabon Suwaiba ba zata shaƙi wannan takaicin ba". ina cikin yanayin da bana iya magana ma kwata kwata a lokacin, shi yasa ban sami damar ɓarar ma ta da abin da zuciyata ta kwararo min ba. haka kurum a yanzu sai nake jin Inna Amarya bata shigewa har cikin zuciyata da wasu sabbin ɗabi'un da nake ganinta da su, sai nake ganin kamar dama can ma tana riƙe dani ne saboda wata manufa tata, to amma duk san da baya ta hasko min cikin kaina, kyakykyawar zamantakewarsu da Gwaggona sai na ture duk wani kokonto a gefe, zuciyata ta koma tuna min wannan Inna Amaryar ce da ta ɗaukeni kamar ƴar cikinta, Inna Amaryar da kullum Gwaggona ke sawa albarka, Inna Amaryar da komai ta rakito na Mairo ne da Gwaggo, to akan me zuciyata zata fara wasi-wasin banza akanta?. "ke tunanin me kike?". na kore mamakin da yay tsalle ya dira a saman fuskata na yacce na karancin maganar da Adawiyya ke faɗamin ƙarya ne, dan fuskarta da yanayin maganartata sun nuna hakan. na ƙaƙalo murmushi nace da ita,"ba komai". sai kuma ta ɗora zancen daga inda ta tsaya,"ni wallahi ma yanzu fargabata a gaba ta ke Mairo, idan aka zo maganar aurenki wannan soki burutsin ya shiga kunnen mijin da za ki aura...shi kansa Suhail ya faɗa min abin da baki sani ba, yace tuntuni yana sonki kuma aurenki zaiyi, yaso ma ace bayan mutuwar nan ayi maganar aurenku, to amma tun da yaji anyi miki fyaɗe yaji ba zai iya ba". nayi wani guntun murmushi me ma'anoni biyu nace da ita,"au Fyaɗenma har anyi min kenan?". tai wani murmushin da zan iya kiransa dana munafurci dan yayi kama da hakan, sannan tace. "to Mairo abin da ake ta cewa kenan, kuma kowa ya yarda". "har da ke kenan?". da nuna alamar rashin gaskiya tace min,"haba in yarda da wannan banzar maganar, sai kace ban san wace ƴar'uwata ba, ni dake fa duk mun san cikin juna, idan gaske ne ai tuni kin faɗa min... ai shi yasa da ake ta cewa wannan hasken da kika yi na me ciki ne naji daɗi da Ya Amadu ya kora bayanin komai, kowa yasan gidan hutun kika faɗa ba hannun wahala ba shi yasa kikai kyan gani, wallahi ban san mun tara maƙiya ba sai a dawowar nan taki...ke baki ji yanda aketa baƙinciki da sauyin rayuwar da kika samu ba, harfa da masu zugani wai na fita harkarki tun da kin iya turanci ni ban iya ba...ni duk ba wannan ba, yanzu ta ya zamu goge baƙin fentin da mutane ke miki kallo da shi?". na sake yin wani murmushin nace,"to ma dai ko me za ai ta faɗa ai ta faɗa, ni ba zai dameni ba, dama tun da na dawo na shiryawa jin waɗannan ƙananun maganganun, dan haka wanda bai faɗa ba ma ya faɗa, wanda yake faɗa kuma yaci gaba da faɗa ni ko a gefen yatsana". da alama maganar da nai ba tai ma ta daɗi ba, taso ace na tashi hankalina ne, dan tun dawowata na gama fahimtar sabuwar zuciyarta, Adawiyya ba irin ta da bace akaina, ta yanzu da banbanci, waccan pure ce, amma wannan cike ta ke da tsatsa. na sauke tunkuyar daga kan murhu ita kuma ta kashe murhun, sannan muka wuce ɗakin Yagana. ta ke min naganar Nafi'u ɗan gidan me unguwa da ya zo da maganar aurena, tana roƙona akan na yarda na amince. "shi kuwa kamar wanda bai san mutuwa ba, sai kace gidanmu neman kai da ni suke, daga mutuwar uwata sai maganar aure, ai ya bari na huce zafin mutuwar tukunna ya tunkare ni yaji idanma zan amince masa, amma ba kai tsaye ya kai maganar wurin manya ba. ko da yake dama yanzu ni sai abin da na dinga gani, tun da jajirtacciyar mahaifiyata me tsayin daka akaina she is no more, i have to be patient akan duk wasu challengies da zan fuskanta". na faɗa ina yafa mayafi ina cewa da Adawiyya ta tashi mu tafi gida, yau gaba ɗaya ban leƙa ba. Yagana ta zabgan harara da jan ƙaramin tsaki. "ai na faɗa miki ki daina samin ɗan banzan turacin naku a cikin magana tun da ba iya shi nayi ba. ke ba ki san ma ni yanzu wannan hausar taki ma ba sonta nake ba, ba yanda na iya ne kawai, kina hausa kaman cin kashi... da kin yi zance kaɗan sai ki fara za da mo da yo, haka kawai ki dinga ƙunshe min kai". murmushi kawai nayi na nufi wajen da nayi sallah ɗazu zan ɗauke ƙaram
🏠