NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 11 of 223

airi, muna mata sannu da aiki". Adawiyya da Jamila suka amsa da to atare, zamu fita muryar Ya Amadu ta sauka a kunnuwanmu "ba'a koma makaranta bane yau?". Ya tambayemu cikin kakkausar murya, tare muka haɗa baki wajen ba shi amsa da ehh an koma. "to uban me kuke yi da baku shirya ba har ƙarfe bakwai, kunfi so kullum ku sai kun makara, to kamin na fito ku shirya ku bar gidan nan". Cikin sauri dukanmu muka fito, ni da Adawiyya kuma harda rige-rigen shiga bayi yin wanka, sai dai kamin ta kai ga sa ƙafa tuni na faɗa naja ƙauren langa-langa na rufe inata mata dariya, ita kuma tana min aikin masifar saura na zauna. Tare mukayi karin kumallo da Innata, sai dai mu ba irin wanda ta yiwa ƴan gidan suka ci bane saboda tasan bana son koko duk da bawai sha ne gaba ɗaya ba nayi ba, idan nasha ne ya kan sani amai wasu lokutan, ya kuma zamana saina jigata in dai nayi. A kuɗin da mahaifiyarta ta aiko mata da shi jiya, Dama wannan aiken duk sati saita yi musu shi kowacce dake gidan aurenta, shayi ne ruwan bunu da biredi da ƙwai ta bawa Saleh ya siyo mata, bamu ci wainar ƙwan ba ita wannan a kwanon abincina na makaranta ta saka min. Na gama shiryawa cikin sabbin uniform ɗin da Baba ya karɓo mana daga ɗinki daren jiya, na kuma goya sabuwar jakata na zauna ina saka sabon kambas ɗina, Adawiyya ta shigo wadda tuni ta gama nata shirin, ta gaida Inna sannan tace min,"kiyi sauri fa mu fita ga Ya Amadu can ya shigo". Ina zaro ido waje nace ma ta, "haba?". "wallahi sun shigo su na ɗakin Inna suna gaisheta, ki sauri kamin su ƙaraso nan". duk kazar kazar ɗina yau babu shi, wajen ɗaure igiyar takalmin ne ya ɓatan lokaci, ina zaune inata fama da ɗaure igiga Ya Kabiru yayi sallama ɗakin sannan yasa kai y shigo, yace da Inna za'a shigo gaisheta, nan da nan kuwa muka ɗan kimtsa wurin muka shimfiɗa tabarma sannan yay musu iso suka shigo, sai da Inna tayi musu nuni da tabarma kana suka zauna, cikin girmamawa da ladabi duk suka gaidata, da zasu tafi Suhail ya fiddo kuɗi cikin aljihu sabbi ya ajiye mata a gefe, duk yanda tayi akan ya ɗauke yaƙi yace a'a, ta kuwa yi musu godiya sosai tare da sanya albarka. Acikin kuɗin Inna Amarya ta bamu kuɗin makaranta kowannenmu naira ɗari ni da Adawiyya, tayi min adu'a kana na fito na nufi ɗakin Gwaggo, Ko dana shiga ɗakin zaune na sameta bisa darduma ƙafafunta a miƙe ta zuba tagumi, da alamu dai tunda ta idar da sallar asuba bata miƙe daga wurin ba. Irin wannan yanayi shi ne matuƙar ƙololuwar yanayi dana tsani tsintar ganinta aciki, yana damuna yana kuma tada min da hankali, saita zauna tayi shiru ta zuba tagumi, wani lokacinma ko da kayi mata magana da ido kawai zata bika ta baka amsa da hannu. Ƙafafuna a sanyaye na ƙarasa wurita na zauna, na kuma zare mata tagumin, sannan ta farga da shigowar tawa, na rungumeta tarin hawaye na cika min idanu, Muryata na rawa nace, "me ya sami Gwaggona? Me aka mata? Waya taɓa min ita? Meke damunta?". Na ƙarasa maganar ina fashewa da kuka a hankali tare da daɗa manna kaina a ƙirjinta, ina jin tausayin mahaifiyar tawa na ƙaruwa a raina fiye dana ko yaushe. "ke ni ban san shirmen banza, mene da sanyin safiyar nan za ki sakani gaba da kuka, kina nufin makarantar ce ba za kije ba?". Maganar ta-ke da ƙoƙarin kawar da damuwar dake tare da ita, da kuma ɓoye wani abu da bata so na fahimta, sai dai kuma ta makaro dan tuni na fahimci wannan manyan idanun nata irin nawa hawaye suka.yi, idan saɓanin haka kuma to tabbas kwana suka yi basu runtsa ba, cikin biyu dai dole anyi ɗaya, wanda kuma hakan ya ƙara ɗaga min hankali kawai saina fashe da kuka mai sauti, itama kuma sai kukan nawa ya ɗaga nata hankalin tasa hannu ta kewayeni ajikinta, haɓarta bisa kaina, kukana ne kawai ke fita a ɗakin sai bugun zuciyarta dake sauka a kunnena, na rage kukan da nake sai shashsheƙa, na kuma buɗa baki cikin muryar kuka na kuma jera mata wancan tambayoyin da nayi mata. Nauyayyar ajiyar zuciya naji ta sauke tare da faɗin,"Girmanki Mairo". Nayi saurin ɗago kaina na dubeta, idanunta na kallon wani gefe can daban. "Gwaggo me girman nawa yayi? Ko ba kya sonsa ne?". Bata bani amsa ba har saida ta rufe ido ta buɗe kana tace,"idan nace bana son girmanki Mairo ai na shiga lamarin ubangiji, Ina dai tsoronsa ne". "to saboda me Gwaggo?". "saboda bana so kiyi min nisa, ina sonki ina ƙaunarki, burina a kullum shi ne naga na buɗe ido na ganki a kusa sa dani, ina jin muryarki, ina ganin kai da komowarki, a taƙaice dai Mairo ina so ne kiyi rayuwa ta har mutuwa a kusa dani. To amma sai dai aure ƙanen mutuwa dole zai rabani dake, zai nisanta tsakaninmu, Nan da shekaru biyu zuwa uku nasan Malam zai ce zai aurar da ke, kin gama wayon da zaki karanci rayuwa cikin lokaci ƙalilan...". Ban bari ta ƙarasa ba nasa hannu na rufe mata baki, saboda yanda naji muryarta tayi rauni har tana Neman sarƙewa, nasa hannu na rufe mata ido saboda ruwan hawayen da suka taru su koma. "Gwaggo dole zan girma tunda Allah shi ke da halittarmu, amma sai dai nayi miki alƙawarin girmana b
🏠