yawa yake, ni kuwa Mairo kamar da ke nake magana ko?". muryata a sanyaye nace ma ta,"Yagana ta gama ɗiba duka, waɗanda kika gani nawa ne na ɗauka". ta kuma cewa,"Ya rasulillahi, to ke me za ki yi dasu?, ina za ki kai kayan Suwaiba ajikinki Mairo duk da kin ciko ba kamar da ba, magana ta Allah ki fito da su a bayar sadaƙa ba a aje su mutu a banza ba". bance ma ta komai ba, dan yanzu ni magana sam ba ƙaunar yinta nake ba, Allah kaɗai yasan halin da nake ciki na irin faɗuwar gaban da nake yi a kullum, ga mutuwar uwata da bata sakeni ba.
ta kuma cewa,"ni kuwa gashi bana so ina yiwa mutum magana yay sautin mahaukaciya da ni, ke kuma gashi sararki ce Mairo, Kabiru ya goga miki fentin rashin kyautawar nan, alhalin ba abu me kyau bane kuke yi, ni wallah ma nayi zaton zaman gidan arnan ba surarki kawai ya sauya ba har da halinki, ashe hali na nan sai ma ƙara gaba gaba da yake, ko da yake dama me hali ba ya fasa halinsa". Adawiyya tace da ita,"Yagana ke kuma gaki da magana, ki barta taji da abin da ke damunta, Uwarta ce fa rasu amma kinbi kin kwazazzafeta. kaya idan ta ɗauka mene aciki, ba kayan Babarta bane, su zata dinga gani suna ɗebe ma ta kewa".
tace da ita,"uwar sawa da iyawa ai ba da ke nai magana ba, dan haka ki rufe min baki...kuma da kin gama aikin ki miƙe ki tafi gidanku dan ba nemanki nake ba, inaji jiya Uwarki na faɗin wai na riƙeki ina hanaki zuwa ki tayata aiki, da yake ita bata da godiyar Allah, duk sauran ƴaƴan da ke gabanta suke ma ta hidamar basu isheta ba sai ke ɗaya da ike wurina kike zuwa ita kuma ba ƙaunar hakan ta ke ba, to Allahn da yake sona ya dawo min da ɗiyar albarka, sai ta jiƙaki ta cinye".
daga dukkan alama Adawiyya ta ƙulu da maganartata, ni dai jinsu kawai nake, kafin na bata amsar da ta takura min da tambaya akai wai kayan Gwaggon har kala nawa na ɗiba.
"Yagana babu fa yawa, kala uku ne, sai wannan dungun atamfar da bata ɗinka ba Baba ya bamu kuɗi muka kaiwa Shamsiyya ta ɗinka mana ni da Basma". "to ai shikenan, su ma sai ki kai a rage miki ɗinkakkun tun da nasan sunyi miki yawa". "haka zan ke saka su ba sai na rage ba". "to hakan ma ba laifi ai tunda ke ba jin shawara kike ba, ita dai Allah ya jiƙanta...ke kuma ya sauya miki halin kafiyarki". na amsa da,"Amin".
ta kuma cewa,"shi Liman ɗin me yace a ga me da sallolin da suka bar kanki?". Ya Salam, na rasa kunnen Yagana wane irin kunne ne, da ace yanda bakinta ke da magana haka kunnenta ke da ji da magana ɗaya ta gamsar ba sai ka ƙara ba. a gabanta fa Liman yace,"Ai a Musulunci an ɗauke alƙalamin rubuta lada ko zunubi ga mutane 3. 1- Yaro sai ya balaga. 2-Mai bacci har sai ya farka. 3-Da mahaukaci har sai ya warke.
Kuma shi irin wanda yay ciwona na mantuwa ana sanya irinsu ne a fannin mahaukata tun da dai ba shi da hankali. Kuma duk abin da ya aikata na lada a yanayin ba za a rubuta masa ba, haka ma na zunubi ba za'a rubuta masa ba, Yana farkawa zai ɗora ne daga inda yabari a farko, duk abinda ya faru a tsakanin nan ba zai rama su ba". kuma a sanda yay shiru da bayanin nasa ita ta karɓe da Kabbara, amma yanzu tana ƙara tambayata ya akai.
tare da Adawiyya muka ɗora sanwar dahuwar kazar, dama tun bayan sadaƙar ukun Gwaggo na tattaro kayana na dawo gidan Yagana, dan bana jin zan iya ci gaba da zaman gidan duk da cewar akwai Inna Amarya, gidan gaba ɗaya ba daɗinsa nake ji ba, saboda Basma ma tabi bayan su Anty Ma'u gidan da ta ke zaune a can kano, Ya Kabiru ma kuma yana ikirarin zai koma a sati na gaba, su Adawiyya ma komawa zasu yi dan hutunsu ya ƙare, ni kuma Ya Amadu yace ba zan bisu ba na zauna anan za'a nema min wata private school ɗin naci gaba da zuwa, Ya Kabiru yace kuɗin makaranta ko ya kai dubu ɗari ne akaini zai biya, tun da har yanzu duk ban manta da karatuna ba, komai yana kaina.
dan har yanzu ma hausar bakina kamar bata cikakkiyar bahaushiya ba, maganarmu da Ya Kabiru da Ya Amadu ma yanzu da turanci muke yi, hatta Kulu ma wadda nayi matuƙar mamakin hakan daga gareta, ta iya turanci sosai dan idan tana yi ma zaka rantse wata baturiyar ce, naso kuma nayi ma ta wasu tarin tambayoyi akanta da suka tarar min akai, to amma ba ayanzu ba, nafi so mu gama sabo da ita tukunna.
"wai da gaske ne shekaranjiya Suhail yazo miki gaisuwa?". maganar Adawiyya ta shigo cikin tunanin da nake, nace ma ta,"umm sun zo, ai yana da matuƙar kirki". da ace na kalli fuskarta a lokacin da zanga abin da ban taɓa gani a fuskarta ba a gama dani, to amma maganar da ta biyo bayan amsa ma ta ɗin da nayi shi yasa ni waigowa na dubeta babu shiri. "nima ya min gaisuwa, har yake ce min wai ai har fyaɗe ma anyi miki, ba ki ji yanda maganar ta sosa min rai ba har ƙwalla sai da nayi. kuma na tambaye shi aina yaji zancen yace ai maganar ma ta gama baza garin bichi, kuma ya za'ai ma nace masa ban san maganar da ta fito daga cikin gidanmu ba". ban san san da na haɗiye wani baƙin yawu a maƙoshina ba, wani babban abu ya tokare a ƙirjina, na tafi tunanin san da Ya Amadu ke zayyanawa su Baba labarin komai tun da