ma ta ba ko?, Hauwa koma dai kece silar barinta gidan nanne? domin yanzu zuciyata ta fara kokonta akan lamarinki?, in har za ki ce min Maryam ta san kina magana to ban san iya tsawon adadin lokutan da ku ka shafe kuna hira ba". Kulu ta zuƙi wani nunfashi kan tace,"a'a Yaya wallahi bata san komai ba, bamu ma taɓa yin doguwar hira da ita ba". Gwaggon ta rumtse idanunta hawaye na silalowa a kumatunta. "ni dama wannan hukuncin da muka yanke na san babu inda zai je muddin muna rayuwa a doron ƙasa, kuma muddin kina kusa da ƴarki, dole wataran gaskiya saita bayyana, ba za ki iya ci gaba da jurewa ba har ƙarshen rayuwa, dole sai kin fallasa ma ta ke ɗin ke kika haifeta, kamar yanda bamu isa mu binne gaskiya ba muce zamu fito da ƙarya...ko ajiya nayi mafarkin Maryam na kan hanyar dawowarta, kuma ajikina ina jin mafarkina zai zama gaskiya. Alhamdulillahi na godewa Allah da zai kansace bana raye Maryam zata san gaskiyar komai, na kuma gode masa da sai bayan raina zata san da cewar bani na haifeta ba, na gode masa da sai bayan raina ne zata ɗanɗani wannan baƙin ciki da takaicin rayuwarta, na kuma godewa Allah da yasa bana raye zata zubar da hawayen da babu me iya tsayar ma ta da shi...Allah na gode maka da zaka ɗauki numfashina a yanzu, Allah na gode maka da ba zaka barni naga hawayen Maryam ba, wannan hawayen da nake jinsu tamkar ɗigar dalma a jikina a duk sanda naga ƙwalla a idonta". muryatarta ta dakushe da matsanancin kukan da yaci ƙarfinta, taci gaba da faɗin,"ni nasan daga ranar da Maryam tasan komai ni kaina saita tsaneni, zata ji haushina, zata ji takaicina fiye da jin takaicin komai, ba don komai ba sai dan ƙunshe ma ta mahaifiya da nayi a wuri ɗaya na hanata raɓarta, har nake hantararta idan ta kusanceta, nake ma ta tsawa a duk sanda suka kasance da juna, na sani, na sani wallahi saita ji haushina...amma dan Allah dan Annabi Kulu ki faɗa ma ta karta ƙullaceni a ranta ta yafe min, ban raba tsakaninta da mahaifiyarta ba saboda biyan buƙatar kaina ba, nayi hakanne dan sama ma ta rayuwa me ƴanci, nayi hakanne dan bana so ta koka a rayuwa, shi yasa na maye gurbin mahaifiyarta Malam kuma ya maye gurbin Mahaifinta da ya ƙi amsarta a san da tazo duniya, domin daga lokacin da ta gane kece kika haifeta, Malam kuma ba shi ne mahaifinta ba, abin da zata fara tambayarki shi ne ina nata mahafin?, waccen amsa za mu bata?, amsar cewa mahaifinta yaƙi karɓarta ya gudu daga gareki shi ne abin da bama so ki sani...amma dan Allah dan Annabi ta yafe min, daidai da rana ɗaya ban taɓa jin cewa ita ɗin ba tawa bace". ta tsagaita da maganar sannan ta ɗauko wasu ɗan kunnen yari da sarƙa na daham ta damƙawa Kulu a hannu. "Hauwa wannan su ne kaɗai kadarar dana mallaka me tsada da daraja, yayin dana mutu Basma ita zata ci gadon komai nawa, to na bawa Maryam wannan halak malak, ki damƙa ma ta a hannunta kice tayi yanda taga dama da shi. kuma kema Kulu sai kinyi haƙuri da ita a san da ta san cewar kece mahaifiyarta, zata ɓauɗe ne ta juya zuwa asalin Maryam ɗinta da ta ke tun farko, Maryam ɗin da babu mahaluƙin da ke iya tausasar zuciyarta a san da ta ke tafarfasa, sai kinyi haƙuri da dukkannin abin da zata aiwatar". daga hakan kuma maganarta ta tsaya cak sai wata shaƙuwa da ta sarƙeta, a wannan daren suka wuce asibiti da ita saboda yanda ƙafarta ta kumbura kamar an hura balan balan, tana tsiyayar da wani irin ruwa me wari, ana zuwa asibitin akace sai an yanke ƙafar, ƴan'uwanta su suka harhaɗo kuɗi Baba ya siyar da rumfar da yake zuba itacensa aka haɗa kuɗi aka biya kuɗin akai ma ta aikin, dama tunda aka yanke tace ita a dawo da ita gida ta mutu a ɗakin aurenta, mutuwa zata yi rayuwarta ta ƙare.
a yau ɗin da aka sallamosu, lokacin da suka gama waya da Kabiru tana fitowa daga banɗaki ta jiyo salatin Yagana da Amarya kafin su fashe da kuka, ta ɗaga labule ta leƙa ɗakin ta tarar ashe Gwaggon ce ta rasu.
ta ke maganarsu ta ƙarshe da ita ta haska ma ta acikin kanta,"Hauwa ƙwarai kina da kyakykyawar zuciya, babu makawa ke ɗin ƴar aljannah ce, domin ba kowa ne zai iya yin sadaukarwar da kika yi ba, ashe ni ba komai nayi ba a cikin sadaukarwar da kike ikirarin nayi miki, lallai ke ɗin ta dabance, ubangiji ya faranta miki...idan Allah ya bayyana Maryam a duk san da gaskiyar da muke ɓoyewa ta bayyana ki faɗa ma ta, tayi haƙuri ta barwa Allah komai, Allah shi kaɗai yasan dalilin da yasa zanen ƙaddararta ya kasance a haka...kuma ki faɗa ma ta wasiyyata agareta ita ce ta ɗauki fansa akan mahaifinta, ko da Allah bai cika min burina akanta na zama lauya ba, tayi shari'a da shi, ta tozarta shi kamar yanda ya tozarta rayuwarku".
*Bayan Kwana Ashirin.*
"ni kuwa Jummai duka kayan Marigayiya ta haɗa ta tafi da su?, dan jiya naga kamar wani fallan atamfarta a kan gado". Yagana ce ke wannan maganar, ni da Adawiyya muna zaune muna fige kaji guda biyun da Baba Mujibu ya kawo aiwa Yagana ferfesu. a karo na biyu maganarta ta sa ke giftawa ta cikin shirun da nai zurfi aciki.
"ikon Allah da