NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 107 of 223

i tafi gidan Yagana a can zasu kwana su da ƴan'uwan Gwaggo na nesa da suka zo, mu tashi cikin dare muyi sallah muyi ma ta adu'a da samun dacewa da Rahma ubangiji, duk da cewar shi ba ya kokoton Suwaiba ƴar aljannah ce, muka amsa masa da to, bayan fitarsa babu jimawa sai ga Kulu ta shigo, ta shiga tsakiyarmu ta zauna sannan ta kwanto da kanmu jikin kafaɗunta, kusan kowa na gidan yayi bacci a lokacin. ita ma da tata dasashshiyar muryar da ta sha kuka ta ƙoshi ta ke ce mana, "ba ku kaɗai aka yiwa mutuwa ba har da ni, nima na rasa ƴar'uwar da ta fi min ƴan'uwana da suka kasa riƙeni a lokacin da na shiga cikin tsanani, haƙiƙa ba zan taɓa mantawa da alkhairin Gwaggonku a gareni ba, saboda haka ina mana ta'aziyya gabaki ɗayanmu...sannnan kar ku taɓa saka cewa a ranku rashinta zai sa ku zama marayu, kuna dani, zan maye muku gurbin Gwaggonku, zan tsaya tsayin daka wajen ganin cewar na zame muku Uwa ta gari, zan kwantanta kamar yanda Gwaggonku ta ke dan nasan ba zan taɓa zama irinta ba gaba ɗaya ba, domin ita ta dabance". ta shafo kaina tana ɗago da fuskata na dubeta, bata taɓa kiran sunana ba, kuma ko a yanzuma da yanayinta suka nuna maganar da za tayi tawa ce shi ma bata faɗi sunana ba, illa iyaka kafeni da ido da tayi masu cike da tarin ruwan hawaye acikinsu tace,"Gwaggonki har ta rasu sunanki ta ke ta ambata, tana binki da tarin adu'oin da baki bai isa ya faɗi adadinsu ba, har numfashinta ya ɗauke faɗa ta ke Allah yayiwa rayuwarki albarka, Allah ubangiji ya shiga dukkan lamuranki, Allah ya dafa miki, ya tsareki daga dukkan sharrin masu sharri, ubangiji yasa kiyi kyakykyawan ƙarshe, ubangiji ya bayyanaki cikin amincinsa ya dawo da ke gida...adu'ar da ta dinƙa yi muku kenan kafin yankewar numfashinta, saboda haka ku sha re hawayenku Gwaggo bata cancanci mu dinga yi ma ta kuka ba, fa ce mu bita da tarin adu'oin da ke cikin kanmu". ta ƙarasa maganar harafan bakinta na karyewa, tana saka hannu wajen share mana hawaye, amma inaa nawa sai suka ƙi tsayawa, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina na kuma fashewa da sabon kukan da nake yi babu ƙaƙƙautawa, domin har yanzu na kasa amincewa raina Gwaggona ta rasu, komai ganinsa nake kamar a mafarki, Kulu haƙuri ta ke ta bani da dukkan wasu kalamai da ta san zasu sa zuciyata tayi sanyi, da karatun alƙur'anin da ta kama a bakinta cikin ƙira'arta me daɗin sauraro, da wannane bacci ɓarawo ya saceni. Kulu kam wannan daren ba ta yi bacci ba, Basma da Mairo na kwance akan cinyoyinta, tausayinta kanta da su na sukar kowanne lungu da saƙo na zuciyarta, tana mai taraddadin abin da zai iya faruwa bayan gama zaman makokin Gwaggo. a lokacinne ƙwaƙwalwarta ta shiga tariyo ma ta da zantukan da suka shafe yinin dare su na yi da Gwaggon kamin ta rasu, ganin ciwonta ya tsananta tana ta faɗa ma ta cewar ita ta tabbata lokacinta yayi mutuwa tunkararta ta ke, kuma Gwaggon ta roƙeta akan ta faɗa ma ta asalinta wanda tun haɗuwarsu bata taɓa tambayarta ba. a sannan ta kwashe dukkan tarihin rayuwarta da na ahalinta ta bayyanawa Gwaggon, ta shaida ma ta abin da bata sani ba na cewar Kabiru ya san komai, Gwaggon tayi mamaki da jin hakan, don duk da cewar da ƙyar ta ke iya magana hakan bai sa muryarta ta fito tar ba a sanda ta tambayeta,"ya akayi Kabiru ya san komai Hauwa'u?". "Yaya akwai ranar da muke ɗakin Malam ni da ke muna tattaunawa akan yanda za'ai na koma cikin ahalina, ku kuma kuci gaba da riƙe Mairo, to da na fito lokacin na tarar da Kabiru a tsaye wanda ya fito daga banɗaki, yanayinsa kuma ya tabbatar min da ya ji dukkan zancen da muke, shi yasa ko a lokacin dana ji cewar zai wuce karatu can ethiopia nasa shi bincika min yanda labarina ya ke yanzu a cikin ahalina...kuma Yaya ita kanta Hussaina ta san da ina yin magana". Gwaggo ta dubeta a firgice da ɗunbin mamaki, mamaki me haɗe da tsoron da ya fallasa firgitar da zuciyarta tayi, ta zabura ta yunƙura zata miƙe amma ta kasa saboda tsananin azabar ciwon da ƙafarta keyi ma ta. tashin hankali a muryata tace da ita,"ya akai Maryam ta san kina magana?, ta ya ya Hauwa?, duk ta yanda naso na ɓoye komai ashe ke kin kasa wannan dauriyar da kika ce min za ki iya". Kulun ta shiga girgiza ma ta kai tana faɗin,"wallahi ba haka bane Yaya, kamawa tayi yasa dolen nayi ma ta magana a lokacin...saboda na tsinci agogon da na san a masarautarmu ne kaɗai ake sa shi, ko da na tambayeta sai ta ke shaida min Suhail ne ya bata, shi yasa na buɗi baki na zaburar da ita akan tai sauri ta dawo, idan mu'amalarta da shi tai nisa zai iya ganowa cewa ita jininmu ce, idanunsa na ƙyallawa kan azurfar hannunta shikenan komai ya bayyana, ni kuma ban shiryawa su san cewa har yanzu ina ƙasar nan ba, dan bana fata ko da gawata ta ƙara shiga masarautar bichi, kuma bana fatan na ƙara yin ido huɗu da Didi, duk da cewar ita ɗin Ƴar'uwata ce, amma ta kasa karɓar ƙaddarar da ta shato mana layi ni da Hassana muka biyota ta kawomu cikin ƙasar nan". "to amma dai ba kiyi wata maganar da zata fahimtar da ita Sirrin da ake Ɓoye
🏠