arya kafin ya yarda ya amince da abin da ya faru kamar a mafarki.
kuma wai Inna Amarya faɗa masa ta ke sun ɓoye masa ne gudun kar ya shiga tashin hankali acan har yace zai taho, Mutuwar Gwaggo ta da ke shi, amma ɓatan Mairo ya shafe kaso 99 na cikin dukan, banda ana cikin jimamin mutuwa da babu abin da zai hana shi zazzagin Amadu inta kama ma harda duka ya haɗa masa, Allah ne da kullum sai sunyi waya da shi amma bai taɓa nuna masa da alamar wata matsala da ke faruwa acikin gidan ba, ɓatan ɗan Mutum! ɓatan ma kuma na Maironsa!, kuma kowa yake rayuwa hankali kwance, sam shi baima yarda da batunsu na cewar har hukuma ma tayi iya nata wajen binciken nemanta ba, ya ƙaryata hakan, ya ƙaryata hakan daga bakin Amadu da ya kusa kaiwa naushi a san da yake rantse masa, har a ƙarshe suka fusata dukansu.
kafin ya taho asibitin sai da yaywa Sadiya da Ƙawarta dukan mutuwa, yaji su ne san da suke tattaunawar wai Mairo da kanta ta ɓata ba saceta akayi ba, yawon iskanci ta tafi, Adawiyya ta karɓe zancen nasu da cewar,"nima haka nake zato dan duk wanda ya kalli Mairo sai ya zargi wani abu dan batayi kama da wadda ta ɓata ba, ai wanda ya ɓace a firgice yake dawowa ,kun tuna Sahura ƙanwar su Zailani?, ita ai kamarma haukacewa tayi, amma ita fa ras da ita, na rantse ma aka bibiya ciki gareta dan irin wannan hasken da tai bana lafiya bane, dana rungumeta ma wani irin wari na dinƙa ji irin na gidan karuwai". shirunta ya haɗe da naushin da Kabiru ya baiwa bakinta har sai da haƙori ɗaya ya fara lilo, bai yi wata wata ba ya shiga fatali da su gaba ɗaya, ƙwallo yake da Adawiyya tun daga Zaure har cikin tsakar gida, da ƙyar aka ƙwacesu daga hannunsa, babu yanda ba'ai ba ya faɗi me suka aikata ba yace su tsumayi dawowarsa bai gama da su ba.
ya cije laɓensa na ƙasa da ƙarfi, tsakanin Amadu da Kulu wa ya kamata yafi jin haushi ne?, ya wani jijjiga kai a hankali kafin ya ɗago ya dubeta yace,"ina yi mana ta'aziyya". na amsa masa da kai kawai, shiru kuma ya gimla, kafin wucewar wasu daƙiƙu na ƙara cewa da shi,"ya akai nazo nan?". ya bani amsa da, "nima san da na dawo akace an kawo ki asibiti, kin yi dogon suma ana tsoron ma Allah sa ba haɗiyar zuciya kika yi ba...Hajiya Hinde tana daga waje, taje alwala". nai wani guntun murmushin da ya tsaya iyaka laɓɓana, zanso ace haɗiyar zuciyar nai nabi bayan Gwaggona, dan gani nake kamar ba zan iya wannan rayuwar babu ita ba, gani nake a yanzu duniyata zata sauya ne ta shiga cikin tsananin ƙunci, gani nake kamar wani babban al'amari me cike da ruɗani na shirin tunkaro ni, gani nake tamkar watan zubar da hawayena ne ya tsaya, ji nake kaman na rasa dukkan gatana.
a wannan daren ƙarfe goma saura muka koma gida, na shigo ciki bayan munyi sallama da Ya Kabiru, Hajiya Hinde na biye damu, muka ratsa ta cunkoson matan da har yanzu basu ragu ba, kaman gidan da ake shirin yin biki, dan ƴan'uwan Gwaggo da Ƴan'uwa Baba yawancinsu duk sun hallara, haka ma ƴan'uwan Inna Amarya ƙwansu da kwarkwatarsu. idanun kowa akanmu cike da tausayawa muka shige ɗakin Gwaggo, tunda na shiga sai mutuwar tata ta dawo min sabuwa, Gwaggona yau ta wuni a makwancinta sai mu kaɗai zamu ci gaba da rayuwa a wannan ɗakin, na ƙyalla idona kan gadonta, idanuna ita suke hasko min a kwance tana baccin nan nata wanda da safe ne kaɗai ta ke samun damar yinsa, dan raya dare ta ke tana ibada bata bacci, idan da rana nace ta kwanta ta huta sai tace min a'a, ai ba zata iya baccin da nutsuwa ba, hankalinta akaina yake.
na ƙarasa ƙafafuna na rawa na ɗauki filonta da zanin rufarta na rungume a ƙirjina, wani sabon hawaye na daban masu ɗumin gaske suka shiga malalo min, a yanzu kam na gama tabbatarwa Gwaggo tayi mana nisan zango.
ban san da shigowar wani cikin ɗakin ba, sai ji nai Inna Amarya ta kamoni ta miƙar dani tsaye, wacce sam na manta da ita, itama idanunta sun kaɗa sunyi jazur da alama har yanzu ita ma kukan nata bai gama tsayawa ba. "kije Babanku na kiranki". ta faɗa tana kama hannuna muka nufa ƙofa, har lokacin ban ajiye filo da zanin rufar Gwaggo ba, a tsakar gida muka same shi inda yake cewa a wuce damu ɗakinsa mu kwana acan, shi kansa Baban tausayinsa nake ji, dan yana tsananin son matarsa, amma a yau mutuwar nan da bata barin wani dan wani yaji daɗi ta raba shi da matarsa kamar yanda ta rabamu da ita.
na juya na riƙo hannun Basma ƴar'uwata da idan na kalleta nake jin zuciyata ta kuma tsinkewa da tausayin kanmu a dalilin rashin mahaifiyarmu. Mama Hadiza ita ta zauna damu a ɗakin tana ta lallashinmu da bamu haƙuri, kowa yazo ce min yake na daina yi ma ta kuka nayi ma ta adu'a, kuma duk yanda naso na tsayar da kukan saina ji wani sabo ya ƙara tahowa, Basma ma harta fini haƙuri da dangana, dan ita zuwa yanzu ta bar yin kukan sai ma idan taga inayi ne ta ke tausata.
Baba ya dawo ɗakin ya tasamu a gaba muka ci abinci, dan kowa nata fama damu muci abinci munƙi ci, haka na dinƙa tura abincin babu wani ɗanɗano, sai da ya tabbatar munci da yawa sannan ya ƙyalemu yace za