NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 105 of 223

with this cheap price:* *MTN DATA PACKAGE* 500MB@===200 1GB@=====300 2GB@=====600 3GB@====900 5GB@====1,500 10GB@===2,600 15GB@===3850 20GB@===5000 40GB@===9900 Dial *460*260# to check Data balance. *Validity 1 month* *Airtel,9mobile and Glo also available.* *Whatsapp OR Call 08066268951* *Comment&Share.* [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._ *29)* nabi ɗakin asibitin da nake ciki a kwance da kallo ɗaya, kafin na haɗe murfin idona na maida na rufe, wasu tafasassun hawaye kuma suka shiga bi ta gefen idona, a yayin da hoton lokacin da aka ɗauki gawar Gwaggona aka fita da ita ya shiga haskawa a idanuna, maganar Baba Mujibu da ke faɗin an tafi kaita itama ta kutso cikin hoton, na buɗe idanuna a zabure na saukesu akan Basma da ke gefena a zaune, tana goge hawayen fuskarta a hankali. zuciya da ruhi suka ƙara tabbatar min da Gwaggona ta rasu, kuma ni da Basma mun zama marayu, bamu da kowa sai Baba. na mayar da idona na rufe ina ambaton kalamar innalillahi wa'inna ilahi raji'un, faɗa nake ina ƙara maimaita yayin da zuciyata kuma ke min wani irin zafi. kafin can kuma naji shigar wani sanyayyan ƙamshin turare acikin hancina, sannan wani sanyayyan hannu me taushi ya shiga cikin nawa, ban dai buɗe idon nawa ba, sai zuciyata da ke bugawa fat fat. "musulmi na ƙwarai me cikakken imani shi ne wanda ya yarda da Allah ɗaya ne, me bayarwa kuma ya karɓa, wanda ke yin dukkan yanda yaso akan bayinsa, a gare shi muke kuma gare shi zamu koma, gaba ɗayanmu da muke rayuwa cikin ƙunci ko jin daɗi cikin jiran mutuwa muke...saboda haka kiyi haƙuri, ki zama me tawassali ki zama me dangana, ki kuma bi Gwaggo da adu'a domin ita tafi buƙata daga gareki, ba wannan kukan ba, yanzu ne lokacin da za ki nunawa Gwaggonki ƙaunar na kike ikirarin kina ma ta da gaske, ta hanyar yi ma ta adu'a da roƙa ma ta gafarar ubangiji". muryar nan me zurfi da kauri ta shiga kunnena da wannan tausasan kalaman nasihar tasa, muryar nan ta Ya Kabiruna da ko mutuwa nayi na dawo zan shaidata, ada ina jin kamar Baba ne kawai ya rage min, ashe ina da Ya Kabiru wanda nasan duk tsanani yana tare dani, duk da ban kalle shi ba amma shi ma nasan kukan yake yi ƙarfin hali da dakiya kawai yake yana faɗin wannan maganar. na buɗe baki cikin murya da ke harɗewa da kuka nace,"Ya Kabiru kaga Gwaggona ta tafi ta barni ko, Mahaifiyata me tsananin so na, me kowa me komai ya amsa abarsa, shikenan yanzu bani da Uwa sai dai na kalli ta wasu". idona a rufe su ke nayi maganar, a jikina naji san da yasa hannu ya goge hawayensa sannan yace da ni. "ban isa na hanaki kuka ba domin nima haka nayi a san da na rasa tawa mahaifiyar, amma zan roƙeki da Allah da Annabi karki ƙara min magana da wannan sautin idan har ba so kike zuciyata ta tarwatse ba, kukanki na kar ya zuciyata, yana raunanata, bana son kukanki Mairo, bana sonsa ko kaɗan...". ya damƙe hannuna da ke cikin nasa, ni kuma na buɗe idanuwana na yunƙura na miƙe zaune, na samu na tsayar da hawayena tukunna na tsayar da idona akansa, cikin ƙwayar idonsa, kan fuskarsa, akansa da girmansa da cikar haibarsa suka cika min ido. gaba ɗaya ya sauya kamar ba shi ba, kamar ba Ya Kabiruna, ya ƙara yin kyau dan hasken har cika min ido yake, yanayin tashin hankalin da nake ciki ne kawai zai hanani fassara abin da nakeji a ga me da shi. shi ma ɗin tun a sanda na ɗora idona a nasa ni yake kallo, ban san me yake tunani ba, amma kallon da yake min kallo ne na kamar wanda yaga sabuwar halitta a gabansa. na sauke kaina ƙasa ina motsa yatsun hannuna, murya a hankali nace,"kuma mutuwar bata tashi ɗaukanta ba sai a san da na dawo, ko ta bari mu gana da ita tsawon lokaci bama tare, ai da saita bari muyi sallama". magana nake cikin ƙarfin halin riƙe kukan da ke neman kubce min. a tunaninta ya san komai, bata san daga ɓatan nata har ciwon Gwaggon duk bai sani ba, mutuwar ma banda ya kira Kulu yaji tana kuka ba zai sani ba, ba wai kuma dan ta sanar masa ba, a jikinsa yaji wannan kukan nata da kuma jiyo hayaniya ta cikin wayar ya tabbatar masa da babu lafiya, hakan yasa ba shiri ya yanki ticket ya taho, kuma da zuwansa tun a hanya aka shaida masa Gwaggo ta mutu, kuma a cikin gida da ya shigo yake jin su na batun ciwon nata wai har da ƙafa ma saida aka yanke ma ta saboda wani ruwa me wari da ke fitowa, Adawiyya kuma ta tare shi da albishir ɗin wai Mairo ta dawo, ta dawo daga ina?, alokaci ɗaya yaywa zuciyarsa da ita Adawiyyan tambayar mamaki kwance a fuskarsa, sai yaji tana sanar masa da abin da zuciyarsa da gangar jikinsa suka kasa ɗauka, har sai da ya sami tabbacin hakan daga bakin Am
🏠