kallonsu, gaba ɗaya cikin ɗakin ƴan'uwan Gwaggona ne sai Inna Amarya da ke can gefe tana nata kuka, idanuwana kuma suka sauka akan gawar Gwaggo da ke a tsakiya an lulluɓeta da wani sabon zanin atamfarta da Wansu yay musu kyauta da sallah ta ɓoye tace insha'Allahu sai bikina zata ɗinka tunda atamfar me tsada ce. wata tsohuwa ƙawar Yagana ta yaye zanin daga fuskarta tana cewa,"Allah sarki kinga har yanzu annurin fuskarta bai gushe ba". Yagana ta rushe da kuka, ni kuma idanuwana suka kasa karɓar Gwaggona da suke gani a matsayin gawa, gangar jikina kuma nema take taƙi amsar mutuwar Gwaggo gaskiya ce. jiri ya kwasheni nayi tangal tangal zan faɗi akai saurin riƙoni, Kulu ce wadda sam ban lura da zamanta ba a bakin ƙofar ɗakin, idanuwanta da farar fatar nan tata sunyi jawur wadda zasu tabbatar maka da taci kuka ne ta ƙoshi, kuma tana cikin yinsa. ta kama ni ta shigar dani ɗakin na duƙe a gaban gawar da har yanzu nake ganin kamar mafarki nake, a yanzu kam idanuwana sun ƙafe, hawayena ya bushe, na kai hannu na yaye duka zanin da ke rufe a jikin Gwaggona, anan na tabbatar da abin da Adawiyya ke faɗa min, ƙwarai ƙafar Gwaggona ta dama ta zama rabi, domin tun daga gwiwarta zuwa ƙasa babu, jikina kuma sai ya mutu gaba ɗaya, Baba Lami ta matso ta ɓanɓare zanin da nake damƙe da shi a hannu ta mayar ta rufe Gwaggona, Yaya Jummai(ƙanwar Gwaggo) kuma tazo ta janyemu gefe ni da Kulu, wacce ke riƙe da ɗaya hannuna tai masa wata damƙa, sai dai inaa, fizgewa nayi daga hannun nata naja ɗuwawu na koma gaban gawar na kamo hannun Gwaggona na riƙe gam, abu ɗaya kawai na sani shi ne babu wani mahaluƙi da ya isa ya fitar da gawar Gwaggona daga gidan nan, cikin ɗakin nan, babu shi, babu kuma wanda ya isa ya raba hannuna da nata, sai dai idan ita mutuwar ce zata zo ta ɗaukeni nima.
ina jiyo Baba Lami na cewa da Kulu,"kiyi haƙuri ki daina kuka, domin ba shi da wani amfani, mutuwa ce Suwaiba tayi kuma kukan ba zai dawo da ita ba, illa ma ya ƙara dagula zuciya da raunana imaninta...dan haka mu bawa zuciyoyi haƙuri mu bita da adu'a ita tafi buƙata a halin yanzu".
ta ke zuciyata ta kuma karyewa, sai kuma murya Baba Mujibu ta shiga kunnena a san da ya ɗaga labule yana faɗin, "Amadu shigo da makarar". jinsu kawai nake, babu wanda idona ke kansa, so kawai nake naga me ƙarfin halin da zai iya zuwa ya ɗauki Gwaggona ya sakata a cikin makarar har yace zai ɗauka. na rantsewa kaina sai dai idan nima numfashin na daina sannan ne za'a iya fita da gawarta daga ɗakin nan, amma ba ina raye ba kuma a kusa da ita.
Baba ya shigo ya tsuguna a gefen kanta, da wata iriyar raunanniyar murya yake faɗin,"Suwaiba na yafe miki, Allah ya yafe miki, halinki na gari ya biki, yasa mutuwa ta zama hutu a gareki, haƙiƙa ke ƴar aljannah ce Suwaiba". sai kuma yay shiru yasa tafukansa ya rufe fuskarsa saboda kukan da ya ci ƙarfinsa. a sannan na kurma wata ƙara da ta cika gidan gaba ɗaya, ba komai ya haddasa hakan ba sai ganin Baba Mujibu da Ya Amadu sun kama Gwaggona sun sakata a cikin makara sun ɗauka za su fita da ita, ban san taya akai suka cire hannuna daga nata ba. inaji ina gani suka fice min da uwata daga ɗakin, su na ikirarin wai zasu kaita wani gidan wanda yake shi ne gidanta na gaskiya. nai wani kukan kura na warce daga riƙon da Anty Jummai tai min nabi bayansu da gudu na danƙo bayan rigar Baba Mujibu, kuka nake ina roƙonsa da dasashshiyar muryata akan,"dan girman Allah Baba Mujibu karka rabani da Gwaggona, ka tausaya min ku ajiye min ita, na yarda na amince ta mutu amma dan darajar Allah ku bar min gawarta na dinga gani ina rage raɗaɗin zafin rasata". gunjin kukana da na Basma dana Kulu ne kawai ke tashi acikin gidan, Inna Zulai ce kawai tayi ƙarfin halin iya zuwa ta janyeni sannan suka iya samun damar fita da gawarta. _"Mairo ina sonki, a duk duniya bayan iyayena duk wani bawa ko wani abu da nake so to ya biyo bayanki, dan Allah ki rage zafin rai kinji, ki koyi haƙuri, ki zama me haƙuri da tawassali a rayuwarki, kuma a duk wani hali da za ki shiga na tsanani a rayuwarki ki riƙe Allah...saboda haka ki bar kuka dan Babanku ya siyawa Adawiyya da Sadiya kaya babu ke, tun da kika ga yayi haka ba shi da kuɗinne, kiyi haƙuri kinji ko, zan ɗauki waccen kwallar tawa na siyar na cika da kuɗin gurina kema na siyo miki kayan da za ki fitar suna da su, kema ba za'a barki a baya ba, muddin ina raye Mairo ba zan taɓa bari ki koka akan wani abu ba, sai dai idan ta Allah ce ta kasance dani, ko kuma nayi iya fafutukar samu na rasa"._ wannan maganar ta Gwaggo a can kwanakin baya ita ta haska a cikin kaina, kuma daga wannan kallon da na yiwa ƙofa naga shigowar Ya Aminu yana ajiye buta yana faɗin,"ehh har anyi ma ta sallah ma gasu can sun tafi". daga nan ban ƙara sanin inda kaina yake ba sai farkawa nayi na ganni a gadon asibiti.
*Assalamu Alaikum*
jama'a na tallatamuku hajarmu ta online/offline business ɗina wanda zan ringa sayar muku da data ta mtn a sassauƙan farashi Kamar haka*
*I sell MTN data