NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 103 of 223

sakko mishi acikin dabara amma ya kasa saboda tsaresa da idon da nayi, kuma yay ƙasa da kansa kamin ya yunƙura ya miƙe yana me cewa da Adawiyya,"ki kama hannunta ku shiga cikin gida". kafin na ƙara cewa wani abu ya bar wurin, Adawiyya kuma ta rungumeni da sautin kukan da ke ƙara karyar da zuciyata, ni dai na zama kamar gunki, bana ko motsi illa bin bayan Baba da nayi da ido har ya ƙarasa cikin rumfar da ake zama, ta tsakankanin mutanen da ke miƙo masa hannu su na musabaha na ƙara shaida ehh da gaske rayuwarta ta sauya daga ranar yau, don yanda bakinsa ke fitar da amsar kalmomin ta'aziyyar ko na nesa da shi can zai fahimci me bakinsa ke furtawa balle kuma ni da nake kusa-kusa da shi, don haka a lokacin na gama yarda da gaske na rasa Gwaggona, mutuwar nan dai da ke raba tsakanin ɗa da mahaifa ta rabani da uwata da duk duniyar nan bani da tamkarta. tunanina da hangena ya tafi akan ta ya zan shiga gidan na tarar da cewar yanzu fa babu rayuwar Gwaggona a ciki?, ta ya zan zauna acikinsa babu mahaifiyata?, ta ya zan ci gaba da rayuwa a cikinsa babu wannan jarumar macen da idan ta ɗaga hannunta ga ubangiji kamin ta roƙawa kanta ta roƙa min?, ta ya zan rayu a cikinsa babu wannan gwarzuwar macen da ta sadaukar da lokacinta, jininta, jikinta, ƙarfinta, zuciyarta tun daga ranar da na zo duniyar har girmana?, ta ya zan rayu a cikin gidan babu Mahaifiyata abar ƙaunata da bata iya kai abinci bakinta sai ina cikin gidan?, ta ya zan iya rayuwa a cikin gidan babu wannan jajirtacciyar macen da bata samun nutsuwa a duk san da bana cikin gidan?, ta ya zan rayu acikin gidanmu babu Gwaggona, babu Gwaggona da ke hana idanuwanta bacci daga san da na fara rashin lafiya har zuwa samun sauƙina?. take naji ƙwaƙwalwata na karanto min kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un acikin raina. maganar Adawiyya da ke fita cikin matsanancin sheshsheƙar kuka ta gifto ta cikin tunanina. "ki tashi mu shiga Mairo...har yanzu ba'a kai Gwaggo ba amma nasan an gama shiryata, ki tashi muje kuyi sallama da ita, tun da ciwonta ya tsananta ke ta ke ta kira har numfashinta ya tsaya". kukan da ya ci ƙarfinta kuma yasa tai shiru, kamin ta ƙanƙameni sose cikin sautin da ya fi wancan shiga jikina tace,"Mairo ba ki ga komai bane, har yanzu ba ki shiga ko'ina a tashin hankali balle har ki nutse acikinsa, akan gaɓa kawai kike, tashin hankali naga lokacin da kika ɗora idonki akan gawar Gwaggo da babu ƙafa ɗaya". nayi wata zaburar da na kasa sarrafa kaina a wajen miƙewa da jin wannan furucin nata, kamar na jefa ma ta tambayar da ke raina ne sai naji ta bani amsa,"ciwonta da yay tsanani sai da aka yanke ma ta ƙafa saboda kullum kuka ta ke yi da ƙafar, kuma shikenan daga wannan lokacin, daga wannan lokacin muka rasata Mairo, wayyo Allahnmu"... me zan bari ta ƙarasa faɗa min?, babu! ai na tashi na ƙarasa cikin gidan shi yafi min, inje idanuwana su gasgata min abin da har yanzu na ke tantama akansa, dan ba zan gama yarda da cewar Gwaggona ta mutu ba sai naga gawarta da idona. tsoro nake ji da gaske, tsoro nake ji na shiga gida naga gawar Gwaggona, tsoro nake ji na shiga gidanmu naga babu wannan fuskar da ke tarbata da murmushi a duk san da na fita waje na dawo. jan ƙafafuna nake da suka min nauyi na kasa ɗagasu, jina nake tamkar wadda ta faɗo daga wata sama me nisa. kuma tun da na shigo gida ko'ina a jikina sai ya shiga rawa, yayinda nake bin ɗimbin mutanen da ke cike a tsakar gidanmu, wasu na kuka wasu kuma sun zabga tagumi cikin jimami, idona bai ƙara sauka akan kowa ba sai Basma da ke tsakiyar yayyun Gwaggo su na lallashinta da ba ta haƙuri, ita kuma ihu kawai ta ke tana kukan da ke tsuma zuciyar duk wani me saurarensa. "Basma ga Mairo ta dawo". Adawiyya ce ke faɗa ma ta hakan, don haka bata san ta yanda akai ta fizge daga hannun Anty Saude ba tayo kaina da gudu. "Yaya". sunan nawa kawai ta iya faɗa tayi shiru muka rungume juna, ita kuka ta ke da sauti, ni kuma kukan nake babu sauti sai tsiyayar ruwan hawaye kawai. "Basma da gaske ne rayuwarmu ta gama rushewa gaba ɗaya? da gaske ne mun zama marayu?". muryata ta fito cikin rishin kuka da kakkaryewar kowanne harafi. ta gyaɗa min kai tana cewa,"Yaya shikenan bamu da uwa, Gwaggonmu ta mutu ta barmu Yaya. dan Allah kije kice ma ta ta tashi ke nasan zata ji maganarki, tun ɗazu inata cewa ta tashi za ki dawo amma taƙi jina, ta tausayawa maraicin da zamu shiga idan babu ita, wannan kulawar tata Yaya, wannan adu'artata, wannan soyayyartata Yaya duk mun rasa su". na janyeta daga jikina na kama hannunta mu kai ɗakin Gwaggonmu, da dukan fatana na duniya zanje naga akasin abunda nake ta ji tun ɗazu, muna zuwa ƙofar ɗakin naji ƙafafuna sun riƙe saboda kukan da nake ji na tashi acikin ɗakin, Hajiya Laraba wadda take kaka a wurin Yayar Babar Gwaggo ita ke faɗin,"haɗuwarmu ta ƙarshe da ita ranar da taje gidan Inuwa take shaida masa Mairo na fama da ciwon ido kuma halin da suke ciki sai du'ai, ƙila ma har aiki sai anyi ma ta". sai na yaye labulen ɗakin a hankali ina
🏠