NOVEL SHARES -
ika tafi ba ki dawo ba sai da Gwaggo ta mutu, Mairo Gwaggo ta rasu tana ta kiran sunanki, Mairo Gwaggo ta mutu ta tafi ta barmu".
take wata tsawa me tsaida sauti ta buga acikin kan Mairo, zuciyarta ta motsa, ta ture Adawiyya daga jikinta ta ɗauketa da mari. "idan kika kuma cewa Gwaggona ta mutu sai na illataki, zan manta da cewar ubanmu ɗaya nayi miki mummunar illa". sai dai kuma me?, kafin ta kai ga ɗaga ƙafa ta taka dan ƙarasawa gida maganar Lukman da ke tabbatarwa da Amadu mutuwar Gwaggo tai sanadiyar zubewarta a wajen.
*_Dan Allah ina barar adu'a daga bakunanku masu albarka akan samun nasara da sa'a akan jarabawata, da kuma wani al'amari dana saka a gaba...na gode muku, Allah ya amsa mana baki ɗaya._*
*Comment&Share.*
[7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE*
*©️Halimahz*
*Anyway@arewabooks*
*HalimaAnyway@Wattpad*
*Halimahz@Bakandamiyahikaya*
_Ina ƴan kasuwan da ke da buƙatar a tallata masu kasuwancinsu cikin littafinmu domin ƙara samun customers?, a sanka a san sana'arka, zamu tallata maku hajarku cikin farashi mai rahusa, ku dai ku tuntuɓi wannan number 08024976578(whatsapp only) kai tsaye, mai talla a ko da yaushe shi ke da riba._
*28)*
"innaillahi wa'inna ilaihi raji'un". gaba ɗaya suka faɗa su na duƙawa gaban Mairo, Amadu na ɗago da kanta da ya daki wani dutse a wurin gefen goshinta ya fashe, kuma tuni ta suma, nan da nan sai rabin dandazon jama'ar da ke wurin zaman makomin suka yo wurin anata salati, Baba da ya ƙaraso wurin cikin saurin da za'a iya kirashi da gudu ya shiga raɓawa ta jama'ar da suka yi ma ta rumfa har ya samu ya kutso ciki zuwa gaban Mairo da ke shimfiɗe a ƙasa. me zai yi?, gaba ɗaya ya rasa taƙamemen me yake ji acikin zuciyarsa, abu biyu ya haɗe masa a lokaci ɗaya baƙin ciki da farin ciki, sai dai baƙin cikin ya rinjayi farin cikin, dan ya tabbata yay rashin da ba zai taɓa maye gurbinsa ba a rayuwa a dai auren mace kamar Suwaiba tun bayan Hajara.
yay ƙarfin halin tattaro sauran kuzarin da ya rage masa yasa hannu ya ɗagota zuwa jikinsa. "ai ba tsayawa zaku yi ba, Lukuman maza ka samo ruwa". yay maganar yana me duban Lukman ɗin, sannan ya dubi Amadu yace da shi,"ai na ka samota?". "Baba maganar bata yanzu bace magana ce me tsayi". ya ba shi amsar zuciyarsa na wani irin harbi.
Malam yay ajiyar zuciya kawai, ya karɓi ruwan da ke hannun Lukman wanda ya kawo a yanzu ya yayyafa ma ta a fuska, duk da haka bata farka ba sai da ya shafa ma ta ruwan a fuska da wuyanta kamin nan taja wani dogon numfashi. wannan dogon numfashin da ta ja da ke nuni da cewar tana raye shi ya wanzar da ƙullutun baƙin ciki a zuciyar Adawiyya, wadda ke duƙe daga gefen Mairo tana aikin kukan munafurci tun a san da Mairon ta zube, dan ihun da taita zabgawa ne ma yajawo hankalin mutane kansu, ihun da a wurinta yake na farinciki da dukkan fatanta na duniya ace mutuwa ce itama tayi awon gaba da ita, don gani ta ke idan har ita da Mairo zasu ci gaba da rayuwa to zata yi rayuwa tagayyararriya me cike da ƙunci, dan ta tabbata saita rasa duk wata walwalarta, saboda tun da tai ido huɗu da canjin halittar da Mairo ta samu taji duniyarta tayi duhu cike da feshin baƙin ciki tamkar aman dalma. har zuciyarta ke ingizata akan ta caka ma ta kibiyar da idanuwanta suka gani a ƙasa, ta yanda babu mai lura da hakan, kuma alokacin da ta ke ƙoƙarin aikata hakan sai Allah ya kawo Mu'azzam, wanda shi ne yaje ya sanarwa da Baba cewar Mairo ce ta dawo kuma ta faɗi ta suma.
zuciyar Adawiyya ta wani tarwatse in to atoms, gaba ɗaya ji ta ke duniyarta ta gama rikicewa, tayi wani duhu tayi baƙiƙƙirin, ba haka taso ba, sam ba haka taso ba, taso ace tabi bayan uwarta, dan a yanzu abin da ta ke ji game da Mairo yafi ƙarfin ta kira shi da haushi ko kishi, baƙin ciki ne tsurarsa da kuma zallar ƙiyayya.
amma ko a yanzu ma gani ta ke kamar fatanta zai cika, tunda nunfashi kawai ta ke babu motsi kuma idanuwa a rufe, bin ƙirjin Mairon ta ke da ido ta yanda yake nuna fitar numfashinta da sauri-sauri, acikin tunaninta lissafin yanda zata ga bayan Mairo da gaske take, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta ba zata taɓa bari Mairo tafi ta ba, ta tabbata yanda ta fita komai a yanzu to samari zasu daina tururuwar da suke akanta su koma kan Mairon. Suhail ɗin da ta gama mallake zuciyarsa da asiri?, Masarautar da ta ƙwallafa ran shigarta a matsayin sirika!...tai saurin girgiza kai, sam bata shirya rasa abubuwan da ta ƙwallafa rai akai ba, kaf tsarinta babu lissafin cewa Mairo zata fita da koma menene a duniyar nan, ita zata kasance a sama Mairo kuma a ƙasa a ko da yaushe. sai gashi tun ba'aje ko'ina ba lissafin nata na neman tarwatsewa, ta rumtse ido tare da cizon leɓenta na ƙasa tana girgiza kai.
"Baba nah". muryar Mairo da ta fito cikin shashsheƙar kuka ta gifta acikin tunaninta, ta baro daga waccen duniyar gaibun da ta shiga ta dawo duniyar zahiri.
"Alhamdulillah, Sannu Mairo". Baba yace dani yana mai dubana da idanun tausayawa, na lura so yake ya goge ƙwallar da ke neman