ya hauta da faɗa yana balbaleta da rashin dacewar abinda ta ke yunƙurin aikatawa.
"mahaukaciyr banza da wofi, muna farinciki da ganinki ashe ke da dabbanci kika dawo, to dan ubanki ki kashe shi ɗin kiga idan ke za'a barki da rai, ki gani idan shi zai wuce wuta".
ta wani ja doguwar ajiyar zuciya ta yarfar da hannun Amadu da ke riƙe da ita, a zafafe ta shiga magana,"ya za'ai ya dake ni kuma kace ba zanyi kuka ba...tsawon fa watanni takwas kenan ya rabani da bautawa mahaliccina, ya dulmiyar da tsaftacceiyar duniyata zuwa tasu ƙazama, to na rantse Ya Amadu idan baka matsa ka bani wuri ba zan haɗa hukuncin har da kai".
ya santa, ya san wace Mairo sarai, irin Gwaggonta ce masu zafin rai, masu aiwatar da abun da suka faɗa, masu tsayawa akan ra'ayinsu, shi kansa ya sani sanyin Mairo ya soma ne daga lokacin da Baba yay ma ta wata nasiha me ratsa jiki, kuma kowa yay mamakin wannan sauyawar zafin ran nata, zafin kan da idan tanayi zaka rantse kana hasko irin turirin da ke fita ta saman kanta, kuma zaka ji zafinsa ajikinka idan ta fitar da iskar baki.
dan haka ya dubi Emanuel yace da shi,"Sir kayi haƙuri ka tafi kawai, mun gode sosai da taimakon da kayi ma ta". Emanuel ya juya ya fice, bai fita dan jin tsoron abin da zata aikata ba, ya fita ne saboda yanda yake jin kansa a irin yanayin da ta ke jin kanta, shi ma kansa tafasa yake, numfashinsa kuma na fitar da turirin zafi, zai aiwatar da abinda yafi nata muni, idan ta sha a nono to shi ma wannan zafin ran yasha shi a nono na tsawon shekara uku ciff, kuma zafin ran da zai rantse yaci uwar nata, to sa'a ɗaya kawai taci, shi ma da shi ne wasu suka yi sanadin shigarsa addinin musulunci zai yi fiye da hakan dan shi ma me kishin addininsa ne, kuma taci daraja, darajar Amadu.
sai da Amadu ya tabbatar zuwa yanzu Emanuel ya bar asibitin sannan ya dubi Mairo da ke duƙe a ƙasa tana rusa uban kuka, ya doka ma ta uwar tsawa akan ta miƙe su tafi, amma ko gezau ba tayi ba, wannan tsoron nasa da shakkarsa ta manta da su, ji ta ke sama ta ke shi ayau.
ganin zata masa taurin kai kuma tana neman tara musu jama'a ya fizgi hannunta ya miƙar ɗa ita tsaye, ya jata suka fita tana aikin turjiya da ihun kuka ita akan ya barta, ya ƙyaleta ta fara zuwa taci uban waɗancan kafiran, amma inaa bai saketa ba har suka shiga mota zuwa tasha, anan ma taso zille masa dan kwasa tayi da gudu zata koma shi ma yabi bayan nata a guje yasa jamaa suka riƙo masa ita, ya kuma ɓalli reshen bishiya yace,"wallahi ko ki nutsu ko kuma nayi miki dukan mutuwa a wurin nan". ba dan furucinsa yasa ta haƙura ba, ta haƙura ne saboda Gwaggonta kawai, zuciyarta yanzu Gwaggonta ta ke da muradin gani, amma ko ba yanzu ba sai kafiran da suka riƙeta sun gane bala'i suka ɗaukarwa kansu.
tunda suka shigo motar babu wanda yay magana a cikinsu har suka iso cikin garin kano, ai anan ma saita kuma birkicewa Amadu, da suka zo wucewa ta wajen wani store ta kalli kanta a cikin glass ɗin store ɗin.
"Ya Amadu bana son kaina na tsani kaina, gaba ɗaya ƙyamatar kaina nake, dan Allah kafin mu tafi ka kaini wurin da za'a sabule min wannan dattin dana kwaso a gidansu, ko da kuwa da wuta ne, ni ba zan koma gida da dattin fatar arna ba, Gwaggona ma ba zata so ganina a haka ba".
kshi ma sai a yanzu ya kula da Sarƙar cross ɗin da ke wuyanta, dan haka ya fizgota gabansa ya cire sarƙar ya jefar, ita kuma ya matse bakinta yay ma ta nuni da kan titi yace,"kinga wannan ƙaton titin, to ni me iya jefaki kansa ne mota tabi ta kanki dan ubanki, cikin ƴaƴa goma sha biyar da an rasaki ba komai bane".
ta san zai iya aikatawar tunda ya faɗa, saboda haka ta nutsu ta saita kanta. lokacin da su ka shigo garin bichi, layin gidansu, ƙofar gidansu, gidan Malam Adamu me faskare, idanuwansu suka yi tozali da abun da ya ɗaure kawunan kowannensu, dandazon mutanen da tunaninsu ya kasa sarrafa kansa. lokaci ɗaya kuma suka saki hannun juna, jikinsu ya saki, ƙafafunsu suka gaza ci gaba da ɗaukansu, suka hango Baba ya fito daga cikin gida yana goge hawaye, kuka yake, tabbas idanunsa kuka suke, suka ɗago kai a tare suka dubi junansu. Mairo tasa hannu ta dafe kanta da taji yana neman rabewa, ta rufe idanuwanta ta buɗe, sannan cikin kakkaryewar harafi tace,"Ya Amadu waɗancan mutanen fa?, kuma me Baba yake wa Kuka?". kan ya buɗa baki yace wani abu zuwan Adawiyya wajen ya sanar da su abunda yake faruwa. sun fito daga layin gidan Yagana ta hango Amadu, sai dai bata taɓa tsammanin Mairo bace a tare da shi har sai da ta zo dab dasu, nan ma kuma sai da tai da gaske sannan ta iya shaida Mairon da kamar sake halittarta akai, ta ke taji wani abu ya tokare ma ta a ƙahon zuci, da ƙyar ta iya haɗiye wani ƙullutun abu da ya tsaya a maƙogoronta, sannan ta ƙaraso gabansu, ta fasa ihun da ta ke jin kamar tayi hauka saboda baƙin cikin ganin sauyawar da Mairo tayi da kuma dawowarta, amma sai tayi pretending ihun akan tashin hankalin da gidansu ke ciki, ta faɗa jikin Mairo ta rungumeta tana fashewa da wani makirin kuka, "Mairo! Mairo ina k