r san da ya kai aya idanunta ƙyar suke akan yatsun ƙafarta, hancinta da bakinta na fitar da hucin numfashi na zafi da raɗaɗin da ke tashi daga zuciyarta, babu wani motsi da ta ke kamar wadda ta suma.
Amadu ya zago ta gabanta yaja kujera ya zauna, dubanta yake da irin yacce hawaye ke sintiri saman fuskarta, ya kamo hannunta ya riƙe tare da tambayarta,"mene kuma na kukan?, ki godewa Allah da ya kawoni a gaɓar da ta dace, da banzo ba me kike tunanin zai ƙara faruwa?".
ta ɗago da ido ta kalle shi, acikin birkitacciyar hausarta irinta yare tace da shi,"kace har yanzu Gwaggona bata da lafiya?". ya gyaɗa ma ta kai,"tun a ranar da kika bar gida, sai dai ayau nasan ciwonta yazo ƙarshe, yau zata warke idan idanuwanta su kai tozali da ke".
ta saki wani murmushi me ciwo, a ƙasan ranta tana adu'ar samun sauƙi ga Gwaggonta, amma hawayen nan masu zafi basu bar sintiri a saman fuskarta ba, hawayen jin ɗaci da zafi akan addinin kiristancin da ta rayu acikinsa tsawon watanni takwas, tsawon wata takwas bata sallah! tsawon wata takwas aka katangeta da bautawa ubangijinta da ya halicceta akan tafarkin Annabi Muhammadu(S.A.W), aka cusa ma ta wata aƙidar ƙazamin addini har tai rayuwa acikinsa, wannan shi ne abin da yafi damunta a halin da take ciki, shi yafi ma ta ciwo, zata so ace keta haddinta Kidnappers ɗin nan su kai akan ƙazamin addinin da ta shiga, zata so ace ta mutu ne akan rayuwa da tayi tare da ƙedararrun arna.
zuciyarta tayi wani irin duka, ta lumshe idanuwanta ta mayar da kanta ga jikin gadon tare da rufe ido, tasa hannu ta dafe saitin da ƙahon zuciyarta yake, jin zuciyarta take kamar zata faso ƙirjin nata ta fito saboda irin masifeffen harbawa da ta ke, wata iriyar masifa ce ke azalzalarta akan azzaluman kafiran da suka raineta.
wucewar wasu daƙiƙu ta buɗe ido a zafafe ta zubesu akan Emanuel da ke ma ta kallon sabuwar halitta, ta tsare shi da idanu kamar wacce ke kallon tv, a yanda take kallonsa gaba ɗaya masifa ce ke ƙara cin ranta, ita ba taimakonta yayi ba cutarta yayi, cutarwa mafi muni, da ya san irin abin da zuciyarta ke ayyana mata akansa da baici gaba da tsayuwa anan wurin ba, domin ji take kamar ta kashe shi, da niyyar taimakonta yayi da gaske ba zai biye son azzalumar zuciyarsa da babu ƙaunar Annabi Muhammadu acikinta ba ya shigar da ita cikin addininsu, da cigiyarta zai saka a duniya, duk da ita ba kowa bace, kuma ubanta ba kowan kowa bane, amma hakan ba zai sa a rasa wanda ya santa ba ko ya hana ta koma hannun iyayenta.
shi kuma wannan kallon da ta ke masa sai yayi tunanin ko tana so tayi magana da shi ne, dan duk maganar da suka yi ita da Amadu bai fuskanci me suke cewa ba tunda da hausa ne suke maganar. dan haka yayo tattaki zuwa gabanta ya tsaya tare da buɗe baki yay ma ta sannu, a zafafe ta diro da ƙafafunta ƙasa ta daki ƙirjinsa da duka hannayenta biyu ta damƙi kwalar rigarsa.
a cikin harshen turanci da tasan maganganunta zasu shiga kunnensa da kyau, acikin muryar da ta gaji da kuka take faɗin, "ka cuceni, ƙaton arne ka cuceni, kasa na rayu acikin ƙazanta, kasa na shiga addinin da ba a cikinsa ubangijina ya halicceni ba, kasa na bautawa wanda ba shi ne Allah ba, mugu azzalumi wallahi ba zan yafe maka ba...na tabbata san da ka tsintoni baka ga nayi maka da wadda ta tashi cikin ƙedararrun arna irinka ba, amma saboda zuciyarka azzaluma ce, saita ta ke gaskiyar da idanuwanka suke gani ɓaro ɓaro ka cusani cikin ƙazamin addininku...dama Gwaggona tace ku ɗin azzalumai ne macuta masu bin son zuciyarsu su cuci musulmi...ka riga ka gama dani, tsakanina da kai sai dai Allah ya isa, danni ba kuyi min taimakon komai ba, ba kuyi min gatan komai ba, kuma insha'Allahu ba zaka taɓa samun rabon hasken musulunci ba bare Allah ya yafe maka, haka zaka mutu kana mushiriki makomarka ta zama wutar jahannama". ta ƙarashe zancen tana ɗauke shi da zazzafan marin da ya kai fuskarsa ƙasa,"idan baka bar gabana na daina ganinka ba zan iya ɗaukan komai na rotsa maka, zan iya kai ka lahira, zuciyata na faɗa min na kasheka ne, na kasheka Emanuel".
shi kuwa tsantsar mamaki da al'ajabi ne ya hanashi wani motsi sai bin ta da ido da yake, sam yanda ta ke kalamanta akansa ba haka suke ba, dai-dai da ƙwayar zarra ba shi da niyyar cutar da wani a rayuwarsa balle kuma ya cutar da wadda shi ne silar shigarta halin manta duniyarta ta baya, yes! yasan yayi laifi da bai shigar da cigiyarta ba. dukan tunaninsa kuma yay ket ya katse ganin ta rarumo wani ƙarfe tayo kansa da shi yay saurin kauce ma ta. "ka daina kallona a matsayin waccen matsiyacin sunan da ku ka raɗa min na Gift, ka kalle ni a Mairo, Mairo ƴar gidan Malam Adamu Me Faskare, Mairon da zata aiwatar da kowanne irin haɗari saboda kishin addininta". tayi maganar a san da ta kai hannu ta maƙuri wuyansa, tana kuma ƙoƙarin soka masa ƙarfen aciki, lokacin kuma Amadu ya dawo daga fitar da yayi waje dan karɓo wasu magunguna da aka rubuta ma ta.
ya ƙaraso ciki da sauri yasa hannu yay cilli da ita gefe sannan ya wanketa da mari,