NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 10 of 223

ina tafiya, haka kawai nazo na goge shi da koɗaɗɗun kayana marasa tsarki. Shi ne Auwalu ɗan gidan Malam Ladan ya karɓe da cewa ai da ma in dai Ƴaƴan Matsiyacin mutumin nanne me farin gemu haka muke, sam ba mutumci a tare damu sai tsiya, an girkemu a gida anƙi aurarwa sai aikin yawon kwararo da muke yi...". Adawiyya bata ƙarasa min ba nasa hannu na toshe bakinta, domin ba zancen marasa mutuncin nake so naji ta ƙarasa min ba, martanin da ta maida musu nake so naji. Buɗar bakinta sai ce min tayi ai babu abunda tace musu, ita dama abunda yafi mata ciwo kalmar matsiyaci da Auwalu ya kira Baba da ita, Shi kuwa wanda ta buge dama laifinta ne tunda ita taho kai a sunkuye tana sosa ido abu ya faɗa mata a ciki. Takaici ya cikani, naja tsaki ina jin kamar na rufe Adawiyya da duka, ta wannan fannin na rashin bakinta tana bani haushi, sai acuceta tace ba zata rama ba, tafi gane ta bar abun ya dameta ko kuma tace za tayi kuka ahaka ne zata huce, shiyasa duk aka rainata. "amma ke dai kuwa anyi shashasha, wawiya kuma doluwa. Ke yanzu har wannan ƙazamin yaron Auwalu ne zai tsaya yana gasa miki magana kiyi shiru baki mayar masa da wadda taci uwar tasa zafi ba, mtswww wallahi Adawiyya sam baki haɗu ba, ji nake kamar na zubar dake anan na yita dukanki har sai kin daina nunfashi, har ataɓa mutuncin mahaifinmu a taɓa mutuncin gidanmu kuma kija baki kiyi shiru...to naji sunan Auwalu, shi ɗayan wanda unguwar zoma bata gasa masa baki ba wanene shi?". Ta dubeni tana cewa, "kinga Mairo dan Allah mu bar zancen nan. Komai ya wuce kansu suka yiwa ai". Na fizge daga riƙon da ta yi min, "kin san Allah ko ki faɗa min ko kuma na juya gidan Ladan ɗin na jira har shi Auwalun ya dawo, idan yaso shi sai ya faɗa min ɗaya ɗan iskan...". Tasa hannu ta rufe min baki tana zaro ido, har da waige ta gani ko da wani a kusa, murya acan ƙasa tace min, "Mairo ki rufa mana asiri, ɗayan fa ɗan birni ne, ke ba kiga yanda jini ke yawo ajikinsa ba kamar zai tsallo waje ya fito, ina mu ina ja da wannan, Allah kuwa arniyar motar da ya shiga kamar ta ƴan yan kan kai, wannan idan kika ce za kiyi masa rashin kunya ai sai yasa a kama mu, ina jinma ɗan sanda ne dan baƙaƙen ƙaya ne ajikinsa, dan Allah Mairo kiyi haƙuri ki ajiye wannan jin kan naki a gefe, ki wuce muje mu kai saƙon nan mu tafi gida a salama". Ban ƙara tabbatarwa da Adawiyya wawiya bace sai yau, a yau ɗinma yanzu da take ce min wai na ƙyale mutumin dayaci mutuncin mahaifinmu. Idanuna su kai jajur suka kuma yowa waje kamar zasu fito, zuciyata tazo wuya, na kai hannu na maƙuro wuyan Adawiyya nace wallahi ko ta nuna min hanyar da tsinannan mutumin nan yabi ko kuma duk abunda nayi mata ita taja, da taji zafin shaƙar dana yi mata ba shiri tayi min nuni da hannu, na kalla gabanmu in da motar ɗazu dana gani ƙofar gidan Liman ke fa-ke a bakin wani shago. "shi ne da wancan motar?". Ta ɗaga min kai alamar ehh, na tambayeta shi ma Auwalun yana cikin motar?, Tace min ehh tare taga sun shiga, na miƙa mata langar hannuna nace ta riƙe abarta, ta kuma wuce muje, za tayi min turjiyar tafiya na figi hannunta muka wuce, isarmu bakin motar na tsuguna na ɗauki dutse, da ƙarfi na shiga ƙwanƙwasa gilashin motar da yake a zuge yanda za su fi jina su buɗe, babu wanda kake ganowa daga ciki saboda duhunsa, acikin zafin nama aka zuge gilashin. Cikin wata kakkausar murya wanda ke zaune wajen matuƙi yace, "ke wace iriyar mahaukaciya ce za ki zo kina dukan glass ɗin mota da dutse". Ban kalle shi ba, dan gaba ɗaya na tattara hankalina ga leƙen cikin motar, idona babu wanda yake so yay tozali da shi in ba Auwalu ba, Amma shi ma na ba shi amsa da cewar mahaukaciya na gida ya barota. [7/18, 23:19] Halimahz(Anyway): *SIRRIN ƁOYE* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *MissAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *5)* Yinin kwana ɗaya da na karanci Suhail na fahimci shi mutum ne irin Ya Kabiruna, rayuwarsa me sauƙi ce, yana da son mutane, yana da wasa da dariya, ga fuskarsa tamkar ta Ya Kabiru cikin fara'a a kowanne lokaci. Yau Inna Amarya ce da girki, tana kammalawa ta ƙwala mana kira ni da Adawiyya da Jamila akan mu kai karin Kumallo ɗakinsu Ya Kabiru, mu kuma sanar musu na baƙi ne idan bai isa ba wani acikinsu yazo ya ƙara musu. Na ɗauki kwanon koko, Adawiyya kuma ta ɗauki tasar ƙosai sai Jamila ta ɗauki kofuna. A bakin ɗakin muka tsaya muka yi sallama suka amsa sannan muka shiga, daga gefe muka tsuguna kowa ya aje abunda ke hannunsa sannan muka gaishesu gaba ɗaya, Sai dai ni atawa gaisuwar sai dana banbace iyakka inda na isar da ita, dan sai da na kama sunan kowa banda na Jawad, banma kuma lura da yana ɗakin ba ko bai nan, ni dai tunda na hangi Ya Kabiru da Ya Amadu wanda ke daga kwance ma bai tashi ba amma dai ba bacci yake ba, sai Suhail ɗin dake zaune kusa da Ya Kabiru wanda da alamu daga wanka ya fito ya shirya. Jamila ta faɗawa su Ya Amadu saƙon Inna Amarya, Suhail ya murmusa yace,"Allah sarki Inna kuce mata mun gode, Allah ya saka da alkh
🏠