zamu bincika muji ko kina da mugun baki amma ni ki tambayeta ta sanni ta san asalina, kuma duk wanda ze so Umaimah a cikin ku baya nane dan ni son tsakani da Allah nake mata ina kuma so ta gyaru ta rabauta ba irin naku na son zuciya da sake ingizata zuwa ga Halaka ba" Ruman ta fada a fusace kafin ta juya ta bar gurin, a ranta ta qudurce ko Su ne kadai suka rage da zatayi qawance dasu a rayuwa ta haqura, ita Nabila zata kira Mayya?
Umaimah kuwa zama sukayi a gurin Fauziyya da Nabila na sake yi mata famfo da gaya mata kalam da suke fasa mata kai take ganin takai inda bata kai ba. Basu bar gurin ba seda lokacin shigar su test yayi suka tabbatar da sunyi brain washing nata ta hanyar nuna mata daidai abinda take aikatawa da kuma cewar duk wanda ya rabu da ita shi yayi Asara ba ita ba.
Haka suka shiga test din babu wadda ta karanta komai a cikinsu, daman ita ce me qoqarin da take goyasu to yau itama batayi karatun ba gashi anyi fada da Ruma bare ta basu Amsa. Da suka fito daga practical ma sun so su jata wai suje gidan Halima dan tun safen ta ke musu waya suje ita bata zo yin test din ba se taqi saboda tuna gargadin Abba na dazu, haka suka rabu a get ta kama hanyar gida ita kadai dan Ruma da gaske ta dauki fushi ko sashin da suke bata sake kallo ba.
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)*
*RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW*
*HALIN KISHI*
*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500*
*GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
Free page 3
Sosai take jin ta a takure saboda rashin waya, idan taje makaranta ta dawo sedai ta zauna shiru in ta gaji ta dauki littattafanta ta duba dan har yanzu babu me shiga sabgarta a gidan se Anty ita kuma ba kulata take ba.
Ita bata ga abin da zesa gaba daya su wani dauke mata ba bayan ita abun jaje ya sama kamata yayi ataru a tayata amma duk an tsangwameta hatta da Yayyanta da suke gidan Aure kowa tazo harara da zagi ne yake raba su a cikin wannan yana yi taci sati biyu, sauqin ta ma bata zaman gidan sosai saboda gabatowar jarabawa da zasu fara ta qarshe kusan idan ta fita makaranta takwas se biyar take dawowa.
Tana da buqatar waya saboda harkar karatu wani abun softcopy ne zaa bayar dole seda wayar ko system hakan yasa ta niyyaci tunkarar Abban su da zancen siya mata waya.
Bayan sallar Isha ta same shi a palour sa, sam ta manta da Mama ce da girki seda tayi sallama ta shiga ta tarar da ita tana hadawa Abban shayi, kamar ta juya amma ba hali tunda sun tigada sun ganta haka ta nemi guri ta zauna ta shiga gaishe su kai a qasa.
"Ya akayi Hajia Umai" Abba ya fada cikin sakin fuska ba kamar yanda yake mata tsahon kwanakin ba hakan ya bata kwarin guiwa ta gyara zama tana cewa
"Daman Abba saura sati uku mu fara jarabawa ne, kuma handouts da yawa softcopy ake bamu, bayan nan wani lokacin ina so na danyi browsing babu dama tunda bani da waya"
"Yanzu me kike buqata" Abban ya tambayeta, seda ta kalli Mama da tayi kamar babu ita a gurin kafin tace
"Waya nake so dan Allah Abba ko taka ce ka ringa bani aro in zan duba abu"
"Tawa kuma Aa salon kiyimun jagwalgwalo, bari dai zanyiwa Yayan ku magana se a samo miki ko qarama ce" Abban ya sake fada. Da alama yau yana cikin yanayi me dadi, kamar tace Aa karya saka Yaya Aminu dan tasan da wuya idanze bari a bata sedaita kanne tayi masa godiya kafin ta miqe ta fita. Daga bakin qofa ta labe tareda kasa kunne ilai kuwa ta jiyo Mama tana cewa
"Haba Alhaji, yanzu kai har ka yarda da wannan lambon da tayi kamar ka manta wacece Umaimah shine zaka dauki waya ka bata"
Murmushi Abban yayi yana kallo ta yace
"Malika kenan, takura da tsanani fa baya gyara sedai su qara kangarar da yaro, iya lokacin da aka dauka ai taji a jikinta idan muka ce zamu ci gaba da takureta kuma tun tana biyuwa har zaa iya kaiwa matakin da zata fito da wata sabuqar hanyar da bamu sani ba.
Zan gayawa Babangida ya kawo mata wayar, daman ko batayi magana ba ina da niyyar sawa ya kawo dan jiya ina jinta tana yiwa Nuratu magiyar ta bata aro ta hana ta, amma hakanbaze chanza komai ba, sannan ina me sake tabbatar miki ki kuma jaddada mata idan wata biyun nan ta cika bata tsaida miji ba sadakarta zan bayar"
"Sadaka kuma Alhaji se kace wata wadda ba'a so" Mamanta fada tana zare ido, se ya miqe tsaye yana cewa
"Kun dauka wasa ne kenan? Daman Lawan megadin gidan Alhaji Manniru ya taba nuna sha'awar auranta toh inaga shi zanyiwa magana kawai, Allah ya nuna mana lokaci zaku gani" ya shige dakin sa ya bar Mama tana cewa
"In sha Allahu Allah ze fito mata da miji amma wane irin sadaka da ita abu babu dadin ji haka".
Qirji Umaimah dake labe a bakin qofa ta dafe, a fili ta furta "na shiga uku daman Abba da gaske yake ni ze bayar sadaka?" Saurin barin gurin tayi gudun kar su ganta a ranta tana ayyana irin diban Albarkar da zatayiwa Lawan duk randa suka ha