NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 40

saka mata a lefe take shi kuwa yana lafta kudi yana siya yanzu shikenan wata banza zeje ya kaiwa? Abinda ya faru yasa ta manta da batun zuwa yinin Halima gashi babu waya bare su kirata, washe gari da take Lahadi ma a gida ta wuni cur ba um babi um um fuska duk ta kode saboda kuka. Mutanen gidan kuwa babu wanda ya shiga sabgarta gara ma Anty ita ce me leqata har ta kai mata abinci wanda a gurin Umaimah ba gwaninta take mata ba dan data fita zata rakata da harara. Ranar Monday tana da Test dan haka dole ta shirya fita makaranta dukda babu abinda ta karanta saboda wancan satin duk sun qarar dashi a yawon shirin biki, Lahadi da tayi niyyar zama a gida tayi karatun kuma ga yanda abubuwa suka kasance. A tsakar gida ta tarar da Abbansu yana sallamar Anty dake da girki ranar, kallo daya ya mata ya ci gaba da magana da Antyn ko gaisuwar da tayi masa be amsa ba dan tun wacceb ranar ya dena Amsa gaisuwarta haka babu sakin fuska ko yaushe suka hadu harara ce take rabasu. Gaba tayi da niyyar fita ya daka mata tsawa yana tambayarta ina zataje, se ta lumshe Idanunta da suka kawo hawaye ta juyo murya na rawa tace "Makaranta zanje ina da Test yau". Be tanka mata ba haka itama bata motsa daga inda take ba harya yi sallama da Anty kafin kamar baya so yace mata " muje" yayi gaba ta bishi a baya. A motarsa ya kaita har cikin makarantar, tafiyar kurame sukayi dan babu me cewa wani qala se sheshsheqar Kukanta dake tashia hankali duk a sonta na tausayinta yayi tasiri azuciyar Abban saboda sam baya so yagansu a damuwa amma kamar dutse ko ajikinsa. "Qarfe nawa zaku tashi" ya tambayeta yana miqa mata naira dubu, ta karba tace "Qarfe sha biyu ne test din, se kuma ina da practical 2-4pm" "Karki kuskura na rigaki komawa gida, idan kuma ba haka ba zamu gauraya" ya fada a kausashe kafin yaja motar ya fita. Kujera ta samu a gurin ta zauna kawai ta fasa kuka, ita ya zatayi? Ko tausayin abinda ya sameta bazasuji ba kuma se abi a ringa tsangwamarta ana daure mata fuska. A gurin Su Fauziyya da Nabila suka sameta dan daman nan suka saba zama su jira junansu "Umaimah lafiya zaki zauna kina rusa kuka kamar wadda akawa mutuwa jifa har kin fara tarawa kanki mutane ana kallonki" Nabila ta fada tana kama hannunta "Toh ina ruwan wani dani kowa yaji da damuwar sa mana an san abinda yake damuna ne da zaa zo ana kallo na" ta fada cikin kukan. "Kinga tashi mu bar nan, ga Malam Tsalha guntsi fesa can ta taho tun kafin ta debi wani sharrin taje tana yayaki a gari" Fauziyya ta fada ganin wata course mate dinsu Jamila ta nufo gurin, irin masu dan banzan gulma da sa idon nan ce, zance kuwa na kowa a makarantar nan kaji shi a bakinta shi yasa suke ce mata Malam Tsalha. A hanya suka hadu da Rumasa'u da shigowarta kenan suka rankaya cafteria suka samu guri can baya suka zauna anan take basu labarin fasa auranta da Qasim yayi. "Amma gayen nan dan yarfi ne,yanzu akan dan abin nan shine zece ya fasa auranki? koda yake kansa yayiwa dan dai nasan baze taba samun hadaddiyar baby kamar ki ba wallahi dan wahala shi yayi Asara. Seki share hawayenki da kyanki da quruciyarki bazaki rasa mijin aure ba. Kuma duk mutumin ma daya kasa haquri da halinka tun kafin ya aure ka ta yaya zaku zauna dashi bayan aure ki manta dashi kawai" Nabila ta fada. "Amma fa Umaimah kema da laifinki ko nace laifinki ma yafi yawa, kishi ai ba hauka bane amma ke idan naki ya tashi rufe miki ido yake kiyi tayin abu kamar wata me tabin hankali. Jifa yarfin da kika masa ranar a gaban mutane dan Allah, be yi fushi ba ya dauke ki har mukaje gida kina zaginsa shi da iyayensa kika sauka kika kuma qara masa, ina ke kika ce idan ya haifu cikin uwar sa ya je ya auri Siyaman ke ya qyale ki? Gashi kuwa ya nuna miki ya haifu saura ki jira ganin IV auran sa da ita nan gaba kadan" Ruma ta fada iya bakin gaskiyar ta. "Ai ke daman kina baqin ciki da duk wani farin cikin Umaimah a rayuwa ni na dade da sanin kina baqin cikin tarayyarta da Qasim waya sani ma ko da sa hannunki a ciki? Toh Umaimah dai nan gani nan bari duk mugun abin mutum sedai ya koma kansa saboda ke kin rasa mashinshini shiyasa kike farin ciki dan ta rasa nata" Fauziyya ta hayayyaqo mata, seta miqe tsaye itama tana kallo ta tace "Dani dake babu meyiwa wani gorin ya rasa mashinshini dan gara ni ana gani ana yabawa ke fa? Cusa kai kike amma mazan yi suke kamar basu san da wanzuwarki ba. Ita gaskiya daya ce daga qinta kuma se fada, the earlier da kika gane laifinki kika gyara the better. Amma idan kinga zaki ci gaba da zama da maqaryata suna dora ki a keken bera shikenan, nidai har a gurin Allah na fita dan na fada miki gaskiya ruwanki ki gyara ruwanki kiqi amma Umaimah babu Namijin da ze aure ki da wannan mugun HALIN KISHIN naki" Rumasa'u ta qara fada idon ta akan Umaimah da tayi shiru. "Kut baki kike mata na karta auru? Toh wallahi tun wuri Umaimah kisan abinyi dan bamu san irin bakin ta ba, Mune shaida" Nabila ta fada cikin son qara kambama abun. "Ke kika hadu da ita rana tsaka dab haka ke
🏠