wa yanzu ta gama fahintar abinda yake faruwa tana gamawa ta miqa musu wayar.
"Ita rigar wayar fa" Mutumin ya fada da ganinsa irin mara mutunchin nan ne daman, dake gidan tsiwar ya tarar kai tsaye tace masa
"Ai ba shi ya siya mun ba"
Shidai ya kinkimi leda yayi waje suka rakashi da kallon takaici.
"Gara da Allah yasa akayi haka ashe dan qananan mutane ne bamu sani ba gara da Allah ya kiyaye mu hada zuri'a dasu" Baba Abdullahi ya fada.
"Karo na Uku kenan Umaimah karo na Uku, na rantse da girman Allah ku zama sheda,saura wata biyu ta kammala karatun ta, idan har aka kai wannan lokacin bata fitar da tsayayyen miji ba a masallaci zanyi shela duk kuma wanda ya nuna yana son ta zan bashi ita sadaka. Badai juninki rashin mutunchi da rashin jin magana ba toh kici gaba, nidai bazan bari baqin cikin ki ke kadai ya dameni ba tunda haka kika zaba wa rayuwarki shikenan" Abba ya fada cikin kaushin murya
"Aa Alhaji kausasa kalami ba naka bane, Addu'a dai da nasihar ita za'a ci gaba dayi mata amma irin wadannan kalaman su suke sake ta'azzara al'amuran a maimakon a samu sassauci se kaga abu na qara lalace wa. Ke kuma Umaimah ki nutsu, ki sani fa kullum girma kike qarawa ba wai baya kike komawa ba. Me yasa zaace kullum aka tashi kwatancen rashin kirki kece a gaba yanzu jin dadin kine ace an fasa auranki har sau uku cikin abinda be wuci shekara daya da rabi ba?
Toh kar kiga kina samun maneman duniya ta ringa miki kida kina taka rawa. Duk namijin kirkin da ze zo neman auranki aka gaya masa an taba fasawa da wasu har sau uku se ya nemi jin ba'asi kuma bakisan abinda zaa gaya masa ba, ki yiwa Allah ki kama kanki ki san me kikeyi ki qyale zukatan iyayenki su huta" Baba Liman ya saka baki.
Nasiha yaci gaba dayiwa Umaimah dake faman rusa kuka. Bata taba jin baqin cikin fasa auranta da akeyi ba irin na Alqasim dan da gaske take son sa kuma yayi daidai da irin mijin da take mafarkin samu a rayuwarta amma daga faruwar dan wancan abin shine zece ya fasa auranta har ya turo a karbar masa komai nasa da yake gidan su bayan koma menene shine sila ai, akan me ze kula wata mace suna tare bayan yasan Irin HALIN KISHIN ta, sam ba jin Baba Liman din ma take ba harya gama nasihar sa yace ta tashi taje wanda ba haka Yaya Aminu yaso ba, yaso ya mammaketa dan tun jiya Mama ta gaya masa fitar da tayi da sanda ta dawo yaso amma ze bita cikin gidan seya ci ubanta wallahi.
Kuka wiwi ta fita tanayi, sam ta manta da tasu da Mama kai tsaye dakin ta ta wuce ta zube tana ci gana da rusa kuka kai kace mutuwa aka mata. Mama dake sallar walaha ta sallame tace
"Idanna idar na tarar dake a dakinnan Umaimah sena lahira ya fiki jin dadi ki tashi ki fita karki qara mun baqin ciki akan wanda nake ciki"
"Ai wallahi ko kashe ni zakiyi babu inda zanje, gurin wa zanje nayi kuka idan ba dakin uwata ba" Umaimah da har sannan bakinta be mutu ba ta fada tana ci gaba da rusa kukan ,kwafa Maman tayi ta tayar da sallarta, harta idar kuwa tana zaune bata tashin ba tayi kuka kana ganinta kasan daga qasan ranta take kukan nan.
"Mama ya zanyi, kullum ina roqon Allah daya ragemun zafin kishi, wallahi Mama ji nakeyi kamar zuciyata ta kama da wuta idan na ganshi da wata macen, me yasa shi ya kasa kiyaye wa ko ze kula mata me yasa zeyi akan ido na?" Ta fada cikin tsananin kuka.
"Dan ubanki keba musulma bace? Duk girman abinda kike ji idan kika nemi taimakon Allah zakiji sauqin sa, amma seki biyewa zuciya ki zama kamar mahaukaciya kiyi abinda ranko ya raya miki se saga baya kizo kina Nadama toh kici gaba Nadama kuwa yanzu kika daura dambar yinta. Ina jiye miki tsoron gaba Umaimah idan baki canza Hali ba wata rana sekin tsinewa wannan mummunan HALIN KISHIN naki" Mama ta fada tana ficewa daga dakin, ga tausayin Umaimah ga takaicinta.
Ranar haka ta wuni zur tana aikin kuka, idan ta tuna wai fa Qasim ya fasa auranta se tayji duniyar ta mata zafi ita yanzu ina zata kuma samun kamar sa Dan gayu daya iya daukar wanka ga kalamai masu sanyaya zuciya, duk idanta hau zafin ta yasan yanda yake bi ya lallabata, gashi ya mata alqawarin idan ya aureta har mutuwa ita kadai ce matarsa har rabtsuwa ya mata da Alqur'ani amma shine daga dan wannan abin zece ya fasa auranta.
Tunawa tayi da Ibrahim saurayinta na farko da aka yi musu baiko tun tana Aji biyar na secondary, shima fa akan kawai ta mari wata yar iskar Cousin dinsa da take sonsa, suka tareta a islamiyya ita da qawayenta kowa ta mata mari biyu tana dawowa gida da daddare se ji tayi wai Babansa yace baze aureta ba.
Bayan shi se Lagin, koda yake shi daman tafiyar su bazata zo daya ba dan namamajone, daya rabu da tarin tarkacen yan matansa ya gwammace ya fasa auranta bayan har an saka musu rana wata shida yace ya fasa yanzu ga Qasim, a qarshen watannan fa suke zancen saka rana tunda watanni biyu suka rage mata ta kammala HND dinta.
Sun gama tsara komai daidai da gidan da zata zauna ya kaita ta gani wanda aka tsara shi iya tsaruwa kadan ya rage a kammala, kullum cikin tura masa irin kayan da take so ya