NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 40

nkali, tana so ta tafi gidan su Halima Daurin aure tana tsoron abinda tambayar hakan ze janyo mata. Wuraren 11 tana zaune a dakinsu, tsoro take ta fita tsakar gidan su hadu da wani daga cikin Mama ko Abban ga Yunwar data kwana da ita ta hadu da ta safiya tana ta sakudarta. Nuratu Yayarta da take bima ta shiga dakin da farantin qosai da kofin da ta zubo kunun gyada ta nemi gefen gadonta ta zauna tana aikawa da Umaiman harara dan daman tun Asuba data farka ta ganta bata ce mata komai ba sedai idan sun hada ido ta maka mata harara kawai. Ganin qosan da kunu ya qara wutar rura yunwar da take ji amma yanayin fuskar Yaya Nuratun yasa ta kasa ce mata zata ci, gashi babu motsin kowa a tsakar gidan qannensu duk sun tafi Tahfiz bare ta yafito wani ta saka ya debo mata. Ganinfa tana neman illata kanta dan damanita bame jumurin yubwa bace yasa ta yunqura da niyyar ta roqi yayar tata sega sallamar Qaninta. Daga bakin qofar yace " Yaya Umaimah kije inji Abba yana kiranki" ya juya abinsa. Seda cikinta ya bada wani qulululu, ashe ba kyaketa akayi ba jira suke gari ya gama wayewa tas ayi mata taron dangi dan taji shigowar Baba Abdullahi da Yaya Aminu babban Yayansu gidan. "Yaya Nuratu dan Allah ki bani ko kunun ne nasha wallahi banajin zan iya tafiya ma yunwa nake ji" ta fada a marairaice dan gara ta karya bille ta roqeta, bata sani ba ko baa girka da ita ba kar taje garin diba ta qarayin wani laifin. Banza Nuratun ta mata seda ta sake roqonta kafin ta turo mata kwanon qosan da kunun da ko rabi bata ci ba dan tana yi tana duba wani texbook nasu na yan medicine tace mata "Gashinan Mayya se kici ai" "Idan ni mayyace ke ma ai mayyar ce" Umaimah ta fada cikin qunquni ta ja kayan ta fara ci hannu baka hannu kwarya cikin dan lokaci ta cinye tas ta zura dogon Hijab har qasa ta fita tana nanata La'ilaha illah anta subhanaka innikuntu minazzalimin a zuciyarta harta isa qofar Sitting room din Abbansu. Ta shiga da sallama kai a qasa kamar ta Allah ta rabe a bakin qofa tana gaishe su ba tare data bari sun hada ido da kowa a cikin su ba. Yaya Aminu ne ya daka mata tsawa yace "Zaki matso ciki ne kose na zo nan na tattaka ki mara jin magana kawai" "Barta Aminullahi fada da hargagi baya gyara, nasihar dai ita zaa ci gaba har sanda Allah ze sa ta dena abinda takeyi" Taji Muryar Baba Liman Aminin Abbansu ta katse hargagin da Yaya Aminu ya fara yi mata. Wata nutsuwa taji ta dan saukar mata dan ko ba komai akwai me kareta dan baze bari su mata komai ba amma da ta gama saddaqarwa yau kashinta ya bushe dan daga Yaya Aminun har Baba Abdullahi babu me sauqi, Abba kuwa zuba ido zeyi su caskalata babu abinda ya masa zafi. "Ina wayarki take?" Baba Abdullahi ya fada cikin zafin nan nasa, seta daga kai ta kalleshi aranta tana cewa "Toh takunkumi zaa sakamun kenan a hanani fita a karbe mun waya tab aikuwa da sake" "Ba magana ake miki ba?" Aminu ya sake zaburowa, qasa qasa ta harare shi kafin tace "Tana cikin gida" "Kije ki dakkota da duk wani abu da kika san Qasim ya mallaka miki ki kawo nan" Baba Liman ya fada. "Duk abinda tasan nasa ne ko tsinke ne ta hado" wani mutum da sam bata lura da shi a palour bama ya fada se faman girgiza qafa yake kamar ana yaqi, Se ta dago tana kallon shi dason jin qarin bayani, amma yanayin da tagani akan fuskar Abbanta da irin hararar daya watsa mata tasa ta miqe babu shiri. Sabuwar Iphone din da Qasim ya siya mata bayan kawo kudin auran su da kwana biyu ta dakko tana jujjuyawa, to me ya faru me zasuyi da wayar? Kuma ai ce mata aka yi ta dakko duk abinda ya mallaka mata kenan ba wai kwace wayar zaayi ba wani abun ne daban. Tunanin me dame ma Qasim din ya taba siya mata ta shiga yi, shi ba gwanin siyan kaya bane gara dai kayan maqulashe duk zuwa da abinda ze kawo mata. Wardrobe ta bude ta zaro lesina guda biyu daya dinkakke ne dayan baa dinka ba se Atamfa guda daya itama dinkakkiya kayan toshin wannan qaramar sallar da yayi matane, ta saka Atamfar Leshin kuma daman yau tayi niyyar saka shi. Ragowar tarkacen Jaka da takalmi da mayafai ta debo ta hada cikin babbar Leda, ta kalli turarukan dake kan Mudubin su wanda suma a cikin kayan take ta tabe baki a fili tace "Bazan hada dasu ba tunda bansan me zaayi ba" Nuratu dai se kallonta take ta zare cajar wayar daga soket ta hada ta sake fita. A tsakiyar ta dire musu ledar, mutumin dazu ya jata gabansa ya hau duddubawa yana cewa "su kenan dai ko? Ko da yake idan ma da saura zan tambaye shi muji" ya miqe yana sabar ledar Yaya Aminu yayi saurin dakatar dashi da cewa "Dan jira dan Allah" ya saka hannu ta dauki wayar dake saman ledar ya miqa mata yana cewa "Budeta ki goge komai na ciki" Umaimah da tayi mutuwar zaune saboda mamaki ta karbi wayar tana juyawa, tsawa Abba ya daka mata yace "Zakiyi abinda akace ne ko kin tsaya kina kallon mutane". Jiki na rawa ta cire password din wayar ta shiga setting nan take tayi resetting nata komai ya goge. Bayan wayar ta bude ta zaro allura ta zare Sim dinta da rigar wayar dan zu
🏠