NOVEL SHARES -
wannan wulaqancin ai kuwa ze san da ita yake zance.
Wayar ta mayarwa da Rumah ta qara harde qafa akan Kujera tana kadasu, a ranta ayyana irin tijarar da zata masa duk randa ya huce ya kawo kansa take. Ita badan ma tana son yazo ya mayar da ita gida ba ai ba zata kirashi ba amma shi kenan.
Basu bar gurin kwalliya ba dai qarshe seda akayi sallar Magriba ko kafin su Isa Gurin Kamun ma takwas saura dan da tafiya daga gurin kwalliyar zuwa can. Ruma kamar zatayi kuka, ita ba kanta ma takeji ba dan a gida ta fada daman zasu iya kaiwa Zuwa Takwas haka kuma an barta amma Umaimah take jiwa dan yanda Mama ta ringa jaddada mata kar tayi Magriba awaje idan ba haka ba zata hadu da Abban su tasan akwai abinda ta aikata da ya saka ake horata.
Sun tarar da Anties din Amarya da daman tun suna gurin kwalliya ake doka mata waya, wata daga ciki ta tare su da wani mulmulallan Ashar tana cewa
"Banda tsabar iskanci Kamu ba dinner ba ki tafi ki share guri kiyi zamanki har takwas uban waye ze zauna yana jiranki? Kwalliyar da kika bata kudi kikayi ta tashi a banza dan rabin mutane sun kama gabansu su kansu dangin mijin naki gasu can har sun fito zasu tafi dakyar aka lallabasu suka zauna shegiya kuma baki kyau bama"
Amarya Halima ta tura baki dan daman tasan se Anty Mara tayi masifa dan tafi kowa fada a cikin Anties din nata, haka suka rankaya suka shiga Yammata na take mata baya. Amarya na zama a kujerarta Rumah ta zagaya aka musu hoto kafin ta rada mata a kunne ta tafi se gobe zata zo gidansu daurin aure da yini. Da sauri ta qarasa inda Su Umaimah suka zauna tana ce mata
"Kije kuyi sallama da Halima mu tafi Umaimah takwas fa keda aka ce kar kiyi magriba a waje".
"Kuje ina haba malama kema ba inda zakije nemi guri ki zauna yanzu fa zaa fara biki ki wani ce ku tafi baza ku tafin ba" Fannah ta fada tana qoqarin zaunar da ita seta turje tana cewa
"Barni Fannah tafiya zamuyi Umaimah muje dan Allah dare na dada yi".
"In zaki tafi ga hanya nan ban riqe ki ba amma ni kam se naga kwal uwar daka, daga zuwan mu kice mu tafi ba wannan maganar" tana rufe baki kiran Mama ya shigo wayarta data ajiye akan Table
"Kin gani ko gashi nan Mama tana kiranki kar ki jawa kanki wani Fadan ki tashi kawai mu tafi" Rumah ta fada a rikice kamar ita ce tayi laifin
"Ai se kiyi, kona koma yanzu ko ban koma ba duk daya fada ne sena sha shi toh in zaki zauna ki zauna idan kuma tafiya ce a sauka lafiya" ta bata amsa tana kashe wayarta gaba daya dan tasan Mama yanzu idanta dosa mata kira ba haqura zatayi ba, kuma dai laifi ne dai ta rigada tayi tunda kafin Magriba akace ta dawo gashi har isha ta wuce bata komaba.
©️2️⃣0️⃣2️⃣3️⃣
*DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*MARUBUCIYAR*
*WATA KISHIYAR*👹🥰
*And now*
*HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE*
*KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*
*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SE A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA*
*07061838488*
*A BIYA A KARANTA*
Free page 2
Biki yayi biki, an raqashe anci an sha yammata sunyi rawa, Umaimah bata an kare da lokaci ba seda aka tashi ta kunna waya lokacin qarfe goma harda rabi tayi, daga gurin zuwa gidansu kuwa taci kusan Minti talatin a qiyasi dai sha daya ce zata kaita gida lallai kam yau ta taro Match me zafi dan tasan ma kafin taje tuni an kulle gida.
A motar Mijin Fannah suka tafi da yake hanyar su daya, ita bayin daren ne yafi daga mata hankali ba, Aa Abayar data saka da zata fito ta barota a gidan Maman Nana saboda bazata shiga jakarta ba kuma batayi zaton zasuyi dare har haka ba.
Cikin taraddadin abinda zata tarar suka sauketa a qofar gidan su, jiki a sabule ta sauka tana gyara yafen dan babban mayafin data samu sukayi musanye da Fannah ko ta dan qara rufe jikinta. A darare ta qarasa jikin qaramar qofar Get din da niyyar bugawa dan tasan dai an kulle se taji takun takalma a bayan ta.
A mugun zabure ta matsa, Abbane, da torchlight a hannunsa saboda an dauke wuta yayi mata kallo daya kafin ya saka muqulli ya bude gidan ya shiga ba tareda ya ce mata komai ba haka ta bishi zugui zugui a baya, ganin yayi kamar ma besan da wanzuwarta ba yasa ta kwasa da saurin gaske tayi ciki tana qara godewa Allah da ya saka babu hasken Nepa kuma be haska jikinta da fitilar hannunsa ba balle yaga irin shigar da tayi.
Dan dama daman da ta sake ji dayaga dawowarta ba ita kadai ba dan seda Fannah ta fito ta bude mata murfin motar da ya samu matsala, yanzu da ace saurayi ne ya ajiyeta a daren nan tana ga kawai tsirenta za suyi su huta.
Dakinsu ta fada tana sauke numfashi, bata tsaya ba seda ta tube kayan ta jefa can cikin wardrobe kafin tayi maza ta fada bandaki ta watsa ruwa tareda Alwala. Tayi mamakin ganin harta idar da sallah babu wanda ya biyo sahunta, amma tasan tarko ne. Tana jin yunwa haka nan ta haye gado ta kwanta, tunda dai ta shigo gidan zance ya qare duk wacce zaayi ayi da safe ai.
Washe gari ta kama Asabar, yanda taga babu wanda ko a fuska ya nuna mata tayi laifi jiyan ya fara daga mata ha