atarta dole ma ta fuzgi hankalinka ka kalleta.
"Sedai idan ke zakije ki fada, ni wuce muje ga me Napep din nan an samo" Umaimah ta fada ko a jikin ta tana zura wayarta a jaka daidai sanda Nana data aika ta taro musu dan sahu ta dawo, haka Rumah ta bita a baya cike da Takaicin halin qawar tata, badan gudun abinda kaje ka dawo ba wallahi seta fadawa Mama wannan muguwar dabi'ar data koya a gurin su Nabila.
Da sam ba haka take ba, da wuya kaga Umaimah ta saka kayan daya bayyana surar ta dan ba tarbiyyar gidan su bace amma shigar su Poly tunda ta hadu da sababbin qawaye irinsu Halima Mailafiya, Fannah Babagana, Nabila Sani se Fauziyya Kura, Izawaqa Mansur da ita Rumasa'u da daman tun Secondary suke tare . acikin su Ruma ce me sanyin Hali ba kuma tayin irin abinda sukeyi.
Nabila da Fauziyya sun fi kowa budadden ido a cikin su bayan Ruma sune mafiya kusanci da Umaimah kumasu suke qara dorata akan duk wani bigire mara kyau kasancewarta me saurin yarda da sakewa da mutane, gashi ita a rayuwarta tana jin maganar qawa kusan sama data kowa.
Tun tana dardar idan zaayi bikin qawar su aka fitar da Anko su suke kawo Style dinda zaayi na zamani na rashi mutunchi tace baza abarta ta saka a gida ba su suka kawo mata dabarar kin sakawar ta bari seta fito waje, dan a Auran Fannah ma dinki biyu aka mata. Wanda ta saka ta fito daga gida daban haka bayan sunje gurin bikin ta cire ta canza wani.
Rumasa'u na matuqar baqin ciki da wannan dabi'a tasu kuma duk ta yanda zata fahimtar da Umaimah cewar tsakanin ta dasu akwai Banbanci na tarbiyya da mutunchi taqi ta ji, sabo da shaquwar da take tsakaninsu tun yarinta ita tasaka ta kasa fita daga cikin group din nasu amma duk da haka kullum cikin yi musu Nasiha take bata damuwa da kyara da hantara da kiranta bagidajiya da sukeyi ita dai fatanta su dawo kan Hanya.
Haka suka kama hanya, suna cikin tafiya Kiran Fauziyya ya shigo wayar Ruma.
"Bawa Umaimah wayar" ta fada bayan data amsa, seta miqa mata tana tabe baki dan yana yin da tayi mata magana ya sa ta tuna da fadan da sukayi shekaran jiya a makaranta akan zasuje sabon gari a saka musu farce da kitson qari duk na shirin bikin, tayi musu nasihar data saba Shine Fauziyyan ta zageta har tana kiranta bagidajiya batayi sanya ba itama ta rama danta fara gajiya da yanda suke maida ita kamar wata bolar su dan kawai tana da haquri shine ashe ita bata wuce ba.
"Umaimah muna Beejay fa, yanzu zaa fara yiwa Lims kwalliya" Fauziyyan ta fada bayan da Umaimah ta karbi wayar,
"Kai haba dai har yanzu shida saura fa"
"Dalla se waccen yar yawar taji kawai ku wuto nan akwai motocin da zasu dauke mu an kusa gama mata ma fa" Fauziyya tayi saurin kwabarta sukayi sallama.
Me Adaidaitan ta gayawa inda ze juya dasu, Ruma ta kalleta tace
"Ban gane ba ina kuma zamuje?"
"Kin fiya matsala wallahi toh saqo zan karba na manta ne se yanzu" ta fada tana tsuke fuska.
Agogon wayar Rumah ta kalla kamar tayi magana kuma tayi shiru, haka suka qarasa tafiyar babu me cewa wani qala har me Adaidaita ya sauke su a bakin gurin kwalliyar.
"Me kuma zamuyi anan kedai nasan ba kwalliya kike ba bare nace" Rumah ta sake fada bayan sun sauka
"Wallahi Rumah kin fiya matsala, bana gaya miki saqo zan karba ba.." Se tayi shiru ganin Nabila ta nufo su fuskar nan tasha kwalliya kamar Aljana se karairaya take dinki ta irin na jikin Umaimah amma sam be mata kyau ba saboda jikin ba iri daya ba, siririya ce ta gaske ga tsaho tana dashi se ta zama kamar wata bulala.
"Mu shiga ciki an kusa gama mata" ta fada tana kama hannun Rumah dan itace zatayi qorafi, haka suka shiga Reception din, abin takaici Amarya Halima na zaune ashe layi ma bezo kanta ba. Wai wata akeyiwa da an gama se ita.
Hira suka shigayi da daukar Hotuna, Umaimah na daga gefe kadan kadan take saka baki tana danna wayarta da tun suna hanya take ta qoqarin kiran Qasim amma ta kasa samun sa.
Tsaki taja ta kalli Rumah tace "Bani aron wayarki nayi kira please" dan duk cikin clique din nasu ita kadai ta yarda da ita take kuma iya sakata a sabgar samarinta hakan kuma ba shi yake hana idan abin ya motsa mata itama tayi mata horon da ta saba yi ba.
Bugu biyu Qasim ya daga kiran da tayi masa da wayar Rumasa'u, sallama yayi tsabar mamakin abinda yasa ita wayar ta ake ta ce mata not reachable amma gashi kira daya nan ta same shi ya hanata magana. Seda ya maimaita sallama sau uku kafin ta bude baki cikin fushin da yake taso mata tace
"Blocking layina kayi kenan Qasim tunda gashi na same ka da wata wayar"
Qasim kuwa yana jin muryarta daga daya bangaren 'Qit' ya kashe kiran, ta zare wayar daga kunnenta tana dubawa, kashewa yayi da gaske kai lallai yau akwai babban tashin hankali ashe.
Kusan sati kenan tun waccen ranar ya dena kiranta, idan ta kira shi farko farko ze amsa amma yanayin da ya koma yi mata magana a dake ba kamar yanda suka saba bane daga baya ma seta kira ta qaraci ringing di ta baze daga ba toh abin ya qaru jiya zuwa yau ma kwatakwata bata shiga shine yanzu ze qara mata da