NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 38 of 40

juyawa dakinsa. Umaimah ta dingisa ta dauki wayarta ta shige daki, seda ta wanko qafar a Bandaki kafin ta zauna kan gadonta tana sauke ajiyar zuciya fa ruwan kadan ne ya dan zubar mata, yanda abin yazo mata a bazata ne ya sakata sakin tukunyar ta fake da hakan ne kawai saboda ta samu mafita gashi kuma Allah ya fiddata. Number Khalil ta danna zata kira sega kiran sa ya shigo cikin azama ta daga tareda fashe wa da kuka kamar wadda aka cewa Mamanta ta mutu. Be ce mata qala ba ya barta tayi iya yinta, abinda ya ringa qarawa kukan nata qaimi shirun da yayi mata, ta saba idan tana so ta daga masa hankalo kawai zata kirashi ta fasa kuka shi kuma ya ringa lallashi da banbaki kenan har se tayi shiru amma yau yana jinta yai buris da ita dan kanta tayi shiru kafin tace "Wai me nayi maka Khalil kake Azabtar dani haka? Kasan yanda nake ji kuwa? Ko so kake se zuciyata ta buga na mutu sannan zaka yarda da sonka ya gama yi mun illah?" Daga bangaren Khalil dake zaune a office dinsa ya rufe ido ya dafe kansa da hannu daya, shi kadai yasan wahalar daya sha daga jiya zuwa yau saboda rashin magana da ita, gaza jure ganin tana kira baya dagawa yayi abinda ya saka ya kashe wayar gaba daya kenan daga baya kuma ya kunna ya sakata a cikin drawer kawai dan juriyarsa ta kusa qarewa. Yanzun da take wannan kukan jinsa yake kamar ana masa yayyafin ruwan zafi, ita take kukan shi yake jin zafin abin a ransa amma yaya zeyi? Umaimah bata dace dashi ba. Dole ta qarfin tuwo ya yakiceta daga ransa in har yana neman zaman lafiya a rayuwarsa amma yaga abin da kamar wuya dan ji yakeyi wutar son ta tana qara ruruwa a zuciyar sa a maimakon tayi qasa. "Khalil Khalil kana jina kayi shiru" Umaimah ta fada abinda ya dawo dashi daga tunanin daya tafi kenan, gyaran murya yayi yana jin wani na taso masa akan abinda yake shirin aikatawa amma yasan shine kadai gatan da zeyi musu daga shi har ita, "Umaimah duk wannan drama da kike yi ta mecece wai? Kin manta irin zagin da kikayi mun jiya da irin kalaman da kika gaya mun? Kefa kika fada da bakinki babu ke babu ni na fita daga sabgarki to me kuma kike so nayi miki yanzu?" "Duk abinda na fada maka bacin rai ne ya saka, kasan yanda nake sonka nake kishinka wallahi Khalil idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na kashe kaina tsabar baqin ciki kuma duk abinda na fada maka ba daga zuciyata bane kawai raina ne ya baci amma ba da gaske nake ba" Umaimah tayi saurin katse shi. Se yayi wani dan murmushi kafin yace "Bacin rai se ya saka hankali ya gushe kuma? Sannan Kishi ya rufe miki ido kin kasa banbance yan uwana da sauran Mata, idan kinyi haka akan yar uwata ta jini da babu aure a tsakanina da ita Umaimah me ze faru kuma duk randa kika ganni da wata daban, kinga komai yana iya faruwa kenan. Bazan iya saka rayuwata a cikin matsala ba, zan aureki ne saboda ki yi daidai da tsarina ina sonki ina kuma samun farin ciki a gurinki bansan wannan rashin hankali shi kike kira da kishin da kika ce kina dashi ba, a ban aureki ba kin zage ni saboda wata kinga kuwa idan mu kayi aure tsaf zaki iya neman rayuwata dalilin wannan baqin HALIN KISHIn, Se yanzu na gano ainihin abinda ya saka sauran samarinki fasawa nima Allah ne ya soni da rahama ya kawo faruwar hakan da qila watarana ina bacvi sedai kawai na farka na ganni a lahira dalilin abinda bansan mafarinsa". "Allah ya tsareni da kashe ka, ina sonla Khalil dana rasa ka gara na rasa raina, dagaske zanyi fito na fito da duk wadda tace zata shiga tsakanina da kai amma bazan taba bari wani abu ya shafi lafiyarka ba, zan kareka da iya kar kulawata, zan baka farin ciki har qarshen rayuwata saboda kai din kaine Rayuwata" Umaimah ta fada tana fashewa da wani sabon kukan daya ke jinsa har cikin ransa, so yake yace tayi haquri ta dena amma ya rigada yayi making mind di sa akan tarayyarsu ba kuma ya son wani abu da ze karya masa lago, ko wannan doguwar maganar da suke yi ji yake kamar ze rasa qarfin guiwarsa. "Wallahi Khalil ina sonka, idan kace zaka barni rayuwata zata shiga cikin garari, zan iya rasa raina idanka rabu dani saboda na rigada na saddaqar maka da ruhina. Nayi maka alqawari zan zama me maka biyayya bazan taba tsallake umarninka ba, bazan sake tayar maka da hankali akan wani abu ba zan shanye komai saboda farin cikinka koda hakan yana nufin yankewar numfashi na saboda na sani wata rana kishinka ze iya zama ajalina" Umaimata sake fada cikin wani irin kuka me tsuma zuciya da ya saka jikin Khalil daukar rawa, a maimakon ya samu nutsuwa da kalamanta sema qara shiga rudu da tashin hankali yakeyi, tabbas yana son Umaimah ko yace yana Qaunarta, amma ita a nata bangaren wannan ya zarce Love sedai a kirashi da Obsession. "Umaimah ki dena kuka haka, kiyi haquri amma bana tunanin zamu rayu tare, wannan tsananin kishinda kike dashi a kaina ze iya zamar mana tangarda a cikin rayuwar auranmu saboda a kullum zuciyarki zata ringa raya miki abubuwan da ba haka suke ba, kinga kuma ke yanda kike handling bacin rai, bana so muyi abinda wata rana za mu
🏠