i? Ai shikenan ki bari Alhajin ya fito baki hada abin karyawa ba zakiyi bayani" Mama data sake fitowa cikin shirin fita ta fada tana kallonta.
Tsintsiya ta dauko ta fara sharar kamar mara laka a jiki ba tareda ta tankawa Maman ba daidai lokacin Anty Saratu ta fito daga dakinta suka gaisa da Maman ta juya tana kallon Umaimah tace
"Aa, Umaimah ce da shara yau kuma ina su Arman tun dazu fa naji motsin shigowarsu, nima yau baccine yafi qarfina wallahi se yanzu na samu na miqe"
"Na basu markaden qosai sukai, bari naje Yusuf na jirana a waje Rabi'a aka kai Asibiti haihuwa yanzu Yaya ta kira take gayamun babu kowa a wajenta" (Rabi'a yar yayarta ce da suke uba daya).
"Toh se kin dawo Allah ya raba, idanan gama abin karyawa a biyo ku dashi" Anty ta fada tayi hanyar kitchen tana ci gaba da cewa
"Bari toh na dora ruwan kunun kafin su kawo markaden, Allah ma ya taimaka ruwa be sauka ba jiya yanda aka baje itacen nan a waje da yau mun gayawa aya zaqinta".
Har Maman taje qaramar qofar fita daga gidan ta juyo tace " Saratu karki kama mata aikin nan, ita zatayi komai zuwa anjima idan ban dawo da wuri ba ki bata abinda za'a dafa na rana tayi" ta juya ta fice daga gidan.
Hawayen takaici ne suka zubowa Umaimah wato da wannan uban aikin za'a horata kenan? Ai wallahi gara kullum a yi mata bulala goma akan wannan uban shara da wanke wanken gidanga qarin girki da itace, ina zata tsoma ranta wai? Ba'a bar mutum yaji da abinda ya dame shi ba za'a rikito masa da wani bala'in.
"Halan wani laifin kika mata ko Umaimah?" Antyta fada taba kallo ta amma yanda kasan da dutse tayi magana haka tayi,bata damu ba ta shiga hada murhu ta dora ruwan zafi kafin ta dakko qullin kunun ta shiga damawa daidai sanda Almajiran suka kawo markadan qosan, Wanke wanken tace suyi, sega Abba ya fito daga dakinsa da waya a kunnensa.
"Kai kuje abinku idan an gama abinci ku dawo ku dauka, daga yau kun bar aikin nan har zuwa sanda za'a ce ku ci gaba" Ya fada yana kallon su Nazifin, suka tsame hannu daga kumfar da suka kada tareda daurayewa kafin suka fice daga gidan.
"Wai Alhaji ya haka ne? Ya zaka hana su yin wanke wanken bayan kasan aikinsu ne yanzu waye zeyi?" Anty ta fada bayan data dakata daga buga qullin qosan da takeyi.
Ba kiji Abinda Malika tace bane da zata fita? Ga wadda zatayi nan. Kema ki tashi daga wannan aikin kije ki hadamun ruwan wanka da wuri zan fita" yana gama fada ya juya cikin daki abinsa. Umaimah ta kalla da tayi mutuwar tsaye da tsintsiya a hann, ta fara murnar Allah ya kawo mata dauki dan sharar da takeyi kadai jin bayan ta take kamar ze cire inaga ta kama sauran ayyukan se ga Abba yazo da wannan zancen kuma.
Rau rau tayi da ido tana shirin fashewa da kuka Antyn tayi saurin dakatar da ita da cewa
"Karma kiyi asarar hawayenki bari naje na same shi wannan wane irin abu ne? Itama Maman banda abi ta ina ita ina saka Amarya aikin wahala ku da ya kamata yanzu ku qara hutawa kafin a fara gyaran jiki idan wani abin kikayi ai hanyoyin horo da yawa ba lallai seta wannan hanyar ba. Ina baze ma sabu na ace za'a sakar miki wannan uban aikin ke kadai dole da sake" ta goge hannu ta ta wuce dakin Abban tana ci gaba da mita.
Karon farko da Umaimah taji yau Antyn ta mata abin arziqi dan ko babu komai ta nuna tausayawa akan ta abinda uwa da uban da suka haifeta basu mata ba. Sharar taci gaba dayi tana share hawaye, a kan window ta ajiye wayarta yabda da Khalil ya kira zataji qara amma har sannan bataji ko qarar shigowar saqo ba ga wannan sabon bala'in da taje ciki kuma haka ta qarasa sharar ta kwashe,
Ruwan kunun ya tafasa har sannan kuma Antyn bata dawo ba, tasan halin Abban sarai dan haka sahunta a likafa gara tayi abinda zata iya kafin ya fito ya nemi abin kari, ruwan ta sauke a garin juyewa ya dan zubo mata a qafa saboda gaba daya hankalinta baya kan abinda take yi ta kuwa saki qara ta wancakalar da tukunyar a qasa tana yarfe hannu tareda sosa inda ruwanya zuba.
Daga cikin daki inda Anty da Abban suke dauki ba dadi suka leqo a tare, da sauri ta qaraso gurin tana cewa "meya faru? Badai qonewa kikayi ba?" Umaimah babu bakin magana se kuka take tana yarfe hannu, Anty ta dubi Abba daya ja ya kwafe a a tsaye tace
"Ka gani ko gashi nan haka kawai kun jawo ta qona qafarta, fisabilillahi Alhaji me yasa kake haka? Duk fa abinda Nasiha da Addu'a basuyi maganin sa ba duka ko aikin wahala bazeyi ba. Yanzu gashi nan tun baa je ko ina ba ta qona qafa ta yaya kake zaton zata iya da aikin gidan nan ita kadai? Ko mu din da muke yi ai muna da mataimaka ballantana" ta ci gaba da mita dan itama gwanace a fannin kafin ta debo qulli ta zuba mata akan qafar bayan data tofa mata Addu'a tace
"Tafi ki zauna haka kawai da safiyar nan an jawo miki"
"Ruwan bada yawa ya zuba ba ba? Ko zamuje a duba mata qafar?" Abba ya fada yana kallo ta, se Umaimah ta girgiza kai har sannan tana hawayen tace "Aa Abba baze tashi ba tunda Anty tayi mun tofi, anjima se naje gurin Ya'u me Chemist ya bani magani"
"Allah ya sawwaqe" ya fada tare da