nan" tana gama fada ta shige daki tana ci gaba da matsar hawaye.
Nuratu dake nata hawayen a zuciyarta tana dana sanin sanarwa da Maman, amma tasan dole zata ji, kuma ita a nata dabarar ta fada mata da wuri ne saboda idan da yanda zaayiwa tufkar hanci ayi se gashi ta sake lalata al'amarin.
"Indai junin mutum munafunci dason ya hadani da uwata sedai abinsa ya qare masa in sha Allahu badai aga bayana ba sedai mutum yaga nasa, kuma aure na babu fashi duk baqin cikin mutum" Umaimah da basu san da tsayuwarta ba ta fada tana jijjiga jiki irin na tsabar fitsara da rashin kunya, Aminu ne ya yunqura kafin ya tarar da ita ta kwas ada gudu ta koma dakinsu harda sakawa qofa sakata dan tasan a yanda ya zaburo tabbas ya riqeta toh ko be kasheta ba se tayi dogon Suma.
Zama tayi akan gadonta gaba daya kuma seta rasa sukuni, hawayen da ta gani a fuskar Mama sun daga mata hankali dan ita ba jahila bace ba kuma mahaukaciya bace tasan illar da hakan ze yi mata wai me yasa a kullum itace sanadin Kukan Mama?
Bama ita kadai ba duk wanda ya tashi qorafi a gidan akanta ta fita zakka a cikin su goma sha uku da aka haifa a gidan.
Iya qoqari kuma tanayi gurin kaucewa duk abinda zaace tayi ba daidai ba amma sau tari ma tsokanarya akeyi idan ta maida martani kuma ace tayi laifi, ko kuma su dauki damuwar data shafeta su dorawa kansu kamar yanzu da wannan munafukar Yaya Nuratu taje ta fadi qarya da gaskiya ita sam bataga abin tayar da hankali a ciki ba. Aure ita ce me auren nan ko maza ashirin suka fasa auranta mijin tane bezo ba hakan kuma baze hana shi zuwa ba sannan maganar Khalil da tace ta fasa wasa takeyi bacin raine kawai yasa shima kuma tasan haka ne idan an barsu daga nan zuwa dare ma zasu shirya kansu amma shine Mama zata dauki damuwa har tana zubda hawayenta.
Tsaki taja tareda gyara kwanciya, tana so ta koma dakin ta bata haquri amma tasan muddin wancan zalimun na gidan ta kai kanta mahallaka ne gara ta bari se ya tafi, haka ta ringa juyi a gado hankalin ta sam yaqi kwanciya, yanzu fa idan Maman tana can tana ci gaba da kuka ai se tashin hankulan su mata yawa, ga abindatake ciki ga Hawayen uwa ita ina zata saka ranta?
Miqewa tayi ta bude qofar,gara taje idan ma kashe ta Aminu zeyi sedai yayi din amma seta je gurin Maman, tana zare sakatar kuwa ta jishi yana yiwa Anty sallama, dakatawa tayi har tajiyo qarar bude qofar fita kafin tayi wuf ta shige dakin Maman
Nuratu na durqushe gabanta tana ci gaba da bata baki bayan Aminu ya gama nasa ya tafi ta shiga, kallon banza suka aikawa juna kafin ta tattare fuska tana kallon Mama tace
"Yanzu Mama kawai dan anzo an gaya miki qarya da gaskiya shine zaki ringa zubda hawayenki a kaina bayan kinsan abinda hakan ze iya janyo mun? Duk fa qaryace kawai baqin ciki ake mun dan an ga na samu wanda nake so yake sona anga kwana biyu muna zamab lafiya dake babu wani abu shine ake so a hada mu"ta qarasa tana Harara Nuratu da ta dauke kai dan yanzu tayiwa Maman Alqawarin bazata sake biye mata suyi fada ba amma badan haka ba seta sake gurje bakin yarinyar nan ta nuna mata banbancin dake tsakaninsu.
"Idan daidai kikeyi Umaimah kin sani in ma akasin haka ne duka keta shafa, babu abinda yayi mun zafi da sabgarki duk yanda kika ga dama kiyi ba kuma zan sake bata raina akan abinda ya shafe ki ba in Allah ya yarda. Na kuma godewa Allah da ya saka bake kadai na haifa ba kinga idan kin sakani baqin ciki ina da wasunki da zasu sakani farin ciki dan haka kije kiyi duk yanda kimaga yayi miki rayuwarki ce ba tawa ba" tana gama fada ta miqe ta shige bandaki ta barta a tsaye dan daman tuni Nuratu ta fice itama daga dakin.
Jiki a sanyaye ta koma dakinsu, kan gadonta ta kwanta tana tunani. ita da kanta ta san tana jawo mutane da yawa ciwon kai amma ya zatayi haka Allah ya halicce ta bata da ikon canza kanta (kodai kika mayar da kanki ba). Wayarta ta janyo ta shiga neman layin Khalil, badai duk akan auransa ne Mama take wadannan maganganun ba bari ta kirashi, da dai tayi alqawarin se tayi sati bata amsa wayar sa ba idan ma yazo gida bazata fita ba amma yanzu saboda farin cikin Mama da kanta zata kira shi ta bashi haquri, ita azo kawai ma ayi abinda za'yi idan ta kama wannan Juma'ar ma a daura musu aure kawai idan yaso duk randa aka a
Shirya ayi bikin shikenan dai ta wuce gorin Mama da tsoron ko wanne lokaci ana iya fasa auran ta.
Tana can tunani wayar dake ta faman ringin ta katse, sake kira tayi nan ma baa dauka ba seda ta jera masa kira goma amma ko daya be daga ba na qarshe ma rejecting yayi kafin aka kashe wayar ma gaba dayanta kamar yanda Computer ta sanar mata sanda ta sake kira
Tayi sororo da waya a hannu tana kallo, tunda take dashi bata zaton ta taba masa kira biyu, duk sanda ta kirashi kome yake ze dakata ya kirata dan baya dagawa sedai ya kashe ya kira, ba qaramin abu yakeyi ba da ze saka ya kasa daga wayarta.
Idan ma yana da wani uzuri me muhimmanci tun kafin lokacin yana sanar mata dan kar ta kira bata same shi ba amma shine yau tayi masa missedcalls 10 be daga ba b