NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 34 of 40

a ce sosai ta sarqe tsakaninta da Nuratu dan tsayawa tayi daga cikin Gareji Nuratu na shiga ta hau kanta da kokawa itama batayi wata wata ba kuwa ta zage suka fara kwasar dambe dan a zuciye take da lamarin Umaiman, tayaya zatayiwa kanta asarar miji kamar Khalil wanda tasan muddin ta rasa shi bazata maida kamar sa ba sannan rantsuwar Abba ta bada ita sadaka ta tabbata kenan. Dambe sukeyi haiqan har cikin gida sosai kuma Nuratun ta zage tana jibgar Umaimah dan ko a qirar jiki zubinsu ba daya bane. Nuratu doguwa ce me garin jiki dan ta ninka Umaiman da tsabar tsaurin ido ne ma ya sakata cukumarta da dambe. Sosai ta lallasata, dan takaicin shekara da shekaru ta samu dama tana sauke mata shi yau akayi sa'a babu kowa a gidan dan suna fita ba dadewa akayi rasuwa a bayan layi dab haka su Mama da Antyn sun tafi Jana'iza se Salis ne kadai a gidan Dan Anty na biyu da suke sa'anni da Umaiman, shi kuwa yana leqowa daga dakinsu yaga abinda yake faruwa ya koma ciki harda turo qofa. Yaya Aminu ne yaje gidan, tundaga waje yake jiyo ihu da kururuwar Umaiman tana zagin Nuratu a ransa yace "abin ya motsa kenan, ai kuwa yau zaki ci ubanki daman ina da cikin ki ai" se ya juya ya koma motarsa. Dorinar da yake ajiyewa saboda horon yaran sa idan ta kama ya dakko har wani murmushi yake yana hasaso irin dukan da ze mata kafin su Mama su dawo dan sunyi waya ta gaya masa sunje jana'iza amma gasu nan zuwa. Yana shiga kuwa beyi wata wata ya shiga sakar musu duka kan me uwa da wabi saboda yanayin daya tarar dasu gaba daya kowacce jikinta na buqatar ya gaya mata. A zabure kuwa suka rabu kowacce ta hau sosa jiki dan dukan ya shige su musamman da daman rabi kaya rabi tsirara suke dan tun a Get aka tuge Hijabai da dambe yayi dambe kuwa aka ringa farke farken kaya. "Ashe baku da mutunchi a cikin gidan kuke mana kokawa se kace wasu yan tasha?" Ya fada a fusace yana kallon yanda kan ko wacce yayi buzubuzu kamar sababbin kamu se sosa inda ya tsula musu bulala suke, jikin bango suka maqale kowa tana sosa jiki, ya sake kallon Nuratu yace "Harda ke ina miki kallon me hankali ashe zama da ita yasa kema kin koyi hauka ko? Uban me ya hada ku fada?" Ya daka mata tsawa, se Umaimah ta fashe da kuka tace "Wallahi Yaya babu abinda nayi mata kawai ta hau ni da duka..." Bulalar ya kai mata duka da ita tayi azamar gocewa ta fada dakinsu da gudu tana masa Allah ya isa a zuciya. Kan Nuratu ya juya ya shiga surfa mata masifa uffan batace ba har yayi shiru dan kansa kafin ta miqe ta shige dakin Mama dan tasan idan ta shiga nasu Umaimah na ciki tabbas fada be qare ba shi kuwa Yaya Aminu samun su zeyi kamar jakai ya lafta. Baafi minti sha biyar ba kuwa su Maman suka dawo, Aminu ne ya fada musu abinda yazo ya tarar se a sannan Salil ya fito daga daki yace "Umaimah ce da laifi dan ta riga Yaya Nuratu shigowa ta labe a bakin qofa se ji nayi sun kaure da dambe". "Ai ko baka fada ba daman nasan itace da tsokana amma itama Nuratu da laifinta akan me zata biye mata har suyi dambe se kace wasu qananan yara" Maman ta fada. "Ki qyale su Allah ya taimaki wata yarinya ta sake mana dambe a gida wallahi se jikinta ya gaya mata dan se nayiwa mutum mugun duka a gidannan" Aminu ya fada, daki Mama ta wuce yabi bayanta bayan sun gaisa da Anty. Nuratu na ganin Maman ta saka kuka, babu bata lokaci ta zayyane mata duk yanda akayi a Asibiti da abinda Khalil ya gaya mata a hanya harda dalilin yin damben nasu. "Ai shikenan" Mama data gama saurarenta ta fada tana miqewa tsaye, Allah kadai yasan abinda taji a zuciyarta se kuma wanda Ubangiji ya jarabta da fitinanniyar yarinya irin tata. "Ai kuwa sena ci ubanta yau a gidan nan, kuma bata isa ba a wannan karon ta sake lalata magana tunda naga abinnata ya zamana tsantsar iskanci tana da buqatar a dawo da ita kan hanya" Aminu ya fada afusace yana miqewa shima se Mama tayi saurin dakatar dashi da cewa "Karka kuskura ka taba ta, baka ji abinda akace bane shima yaron yace ya fasa toh ka barta zaman gidan nan ne ko gata gashinan. Kuma kar naji zancen a bakin wani koda mahaifin ku ne kuwa, idan sunzo da kansu sun janye a lokacin ya sani. Amma Umaimah koh idan har ta bata wannan auran bazata maida kamarsa ba" ta qarasa maganar cikin rawar murya tareda daga kanta sama a qoqarin ta na dakatar da hawayenta daga zubowa dan daman daga yanayin muryarta suka gane kuka ne yake neman zuwar mata abinda ya qara sanyayawa Aminu da Nuratu jiki. "Dan Allah Mama karkiyi kuka, kin sani hawayen ki masifa ne a tattare da ita addu'ar dai ita zaki ci gaba dayi mata in sha Allahu wata rana se labari" Aminu ya fada sedai kamar me jira kuwa kukan ya kwace mata tace "Na gaji, nagaji Aminu da halin qanwarku. Kullun ta Allah da zullumin ta nake kwana nake tashi a raina, yanzu idan aka fasa auran nan karo na hudu fa kenan me kake zato mutane zace a kanta? Ni kadai nasan irin qunci da baqin cikin nake fama dashi akan lamarin auranta yanzu ina murna yan satittika suka rage ta tafi shine ta ja gwalo abinda ze saka a fasa ko ai shike
🏠