imah ba macen aure ba. Macen da zata iya tsayawa a gabanka ta gaya maka duk maganar datazo baki ta ba tareda tayi shayi ko taga qimarka ba ai ba matar aure bace, dukda ma dai ta fada da bakinta babu ita babu ni Allah yasa hakan shi yafi Alkhairi, ki shiga ciki idan Abba yana nan kiyi mun sallama dashi dan Allah tunda wuri gara mu sama ma kanmu sauqi Allah ya hada kowa da rabonsa" Khalil da yau zuciyar yan maza ta motsa masa ya fada daidai sanda ya tsaya kofar gidan su Umaiman.
Ido kawai Nuratu ta saka masa tasan gaskiyar sa ya fada amma bata fatan yar uwarta ta rasa nagartaccen Namiji irinsa, shi kadai ne take tunanin ze iya chanza Umaiman gashi tun ba'aje ko ina ba shima ya sare da halinta yana zancen fasa aure.
Bude baki tayi dakyar tace "Kayi haquri Khalil nasan halin Umaimah sam idan ranta ya baci bata sanin me take fada..."
"Ranta ya baci da akayi mata me? Saboda na gaisa da yar uwata? Yayata ce fa uban mu daya. Haka kwanaki tayi mun saboda Jalila ta kirani twin sister na, ta ringa zagina har tana kirana da Mazina ci. A lokacin nayi mata uzuri a lokacin amma banda Yayi da babu wani abu da bata sani a kaina ba. Yan uwana mata babu wadda ban gaya mata sunanta na nuna mata hotunansu ta yanda ko a hanya suka hadu zata gane su ba.
Saboda gudun bacin ran Umaimah na chanza layin da nake harkokin kasuwancina dasu. Ba dan ina tsoro ta ba, kamar uwar data haifeni duk sanda ta raya mata zata ce nabata wayata tayi bincike ban taba nuna mata rashin jin dadi akan hakan ba ko babu komai waya sirfi ce nima ina da sirrikana da ya kamata ni kadai nasan dasu amma ko mai da ko ina na bata damar shiga ta duba a wayata, hakan ne ya bata damar da zata tsaya ta zageni duk a sunan kishi? Kishi ko hauka? To nidai na haqura taje kawai Allah ya bata wanda ze iya da halinta" Khalil yayi saurin katse Nuratun a fusace dan ransa qara baci yake yi duk idan ya tuna maganganun data yaba masa.
Bude baki tayi da niyyar sake magana ya bude motar yana cewa "kije dan Allah, ki bar Abban ma duk randa na sake biyowa nan haka nazo. Ki bawa Mama haquri nasan babu dadin amma hakan shi kadai ne abinda ze sama mun maslaha dukda ina son Umaimah amma bazan iya auranta ba, a waje tayi mun haka inaga na aureta na kai cikin gidana kinga wannan kome tayi ni na siya da kudina".
Jiki a mace Nuratu ta fita daga motar daidai sanda Adaidaita ya tsaya a qofar gidan Umaimah ta fito daga ciki, kallo daya tayi musu daga Nuratun har Khalil din kafin ta maida ido ta kan Nuratu tace "kuma da kika shiga motarsa ke kadai Allah ya isa bazan yafe ba, idan ma Amana aka ci mutum yaje shida Allah" ta sake fada tana kallon Khalil kafin fuuu ta shige gida. Murmushin zallar takaici Khalil ya saki, ya fara hasashen yarinyar nan bata da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa ko kuma dai saitin kanta na gocewa ne lokaci lokaci.
koma dai yaya shidai he is done with anything concerning Umaimah, yana sonta amma dole ya haqura da ita dan beyi zaton Rigima da Hayaniyarta da Nasir ya ke fada ba ya kai haka. Koda yake ya so ya rufe shi ne amma banda haka ai kaitsaye kawai kamata yayi yace masa tana da matsalar saiti.
Gata dai mace har mace amma babu cikakken hankali Allah kenan me yanda yaso.
Haka ya juya Asibiti bangarorin zuciyarsa na mahawara da juna, tabbas yana son ta so me tsanani amma menene amfanin soyyar da babu kwanciyar hankali da girmamawa a cikinta. Idan ya tuna yanda take riritashi tana lelen sa idan suna yar dadi se yaji kamar baze iya rabuwa da ita ba, amma abinda tayi masa dazun ya saka shakku a zuciyarsa game da auranta.
Tayi kishi da yan uwansa na jini inaga kuma duk randa tsautsayi yasa ta ganshi da wata, bama wannan ba ita rayuwa bata da tabbas. Har zuciyarsa bashida burin ajiye mace sama da daya musamman ace Allah ya cika masa burinsa ya bashi mace irinta amma babu wanda yasan gobe, idan qaddarar sa ta auran mace sama da dayan ce fa yaya zasu kaya?
Yanda yanzu kullum ya kunna radio labarai ne marasa dadi akan mata sun kashe mijin ko sun kashe kishiyar toh maganin kar ayi kar a fara, indai soyayyace ze roqi Allahn daya saka masa ita a zuciyarsa ya cire masa ita kuma ze ci gaba dayi mata fatan Alkhairi ubangiji ya rage mata abinda yake damunta a zuciya amma tabbas baze siyawa kansa tashin hankali da kudinsa ba amma ta yaya ze tunkari Hajiya da wannan magana yanda take son Umaimah kamar ta goyata?
Bama wannan ba, gaba daya fa auransu befi sati hudu masu zuwa ba anya idan yace ze fasa yaya iyayenta zasuji dan shi su yafi tausayawa, mutanen kirki, Mamanta ta dauke shi kamar dan cikinta basu boye masa komai akan Umaimah ba tun fara zuwansa gurinta dan hatta da takaddun Asibitin gwajin kwakwalwa da aka mata seda Abba ya nuna masa amma sam shi be fahimci Al'amarin ba, be taba zata haka abin nata yake ba se yanzu da tafiya take qara nisa daman hausawa sunce Hali zanen dutse ashe lokaci take jira ta fara zayyano masa su, toh koma dai menene ze jira a sallami Hajiya ta koma gida kafin yaje mata da wannan maganar.
A can gidan su Umaimah kuwa rigim