NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 40

Idan kuwa haka ne wannan ai shirme takeyi, duk kishin da zesa ka kasa banbance daidai da rashin daidai ai ya zama shirme. Seda suka kwana biyu tana fizge fizgr, sam shi ya manta ma me akayi kawai dayaga take taken ta ya dauki hakan a matsayin yanayi da kowanne dan Adam yana iya riskar kansa a ciki na damuwa ko rashin jin dadin wani abu, ya tambayeta ko da wata matsala ne ta nuna babu komai se kawai ya shareta. Daman lokacin shima ayyuka sun fara masa yawa. Branch office dinsu ya fara aiki kuma shi aka bawa matsayin manager na bangarensu dan haka ayyukansu da yawa. Ga aikin gyaran gidan da ze zauna a ciki wanda yake da yan haya da a ciki suka tashi yana ta aikin gyara da yiwa gidan kwaskwarima saboda tsohon gida ne. Dukda Hajiyan su taso ya zauna a dayan bangaren da basa amfani dashina gidansu wanda yake mallakin Mahaifinsu amma yaqi yace gara dai ya zauna acan din. Dan kanta da taga ya fita a sabgarta ta nemi shiri suka koma daidai, bata haqura ba da naci da mitar tsiya seda tasa ya chanza sunan Jalila daga Rabin Jiko zuwa twinny. Ranar ana yar dadi da kansa ya bata wayar yace ta chanza, bayan ta chanza ta shiga contacts, mesaagesa, hatta da whatsapp dinsa seda ta duba amma babu wani abun azo a gani da zesaka ta tada masifar tata. Abinda ya mugun mata dadi ganin yanda yake qin amsa saqon ni daga number da be sani ba, taga chats daga yammata amma data hau kububuwar fushin fuuu idan ta shiga chat din ta karanta kuma seta sakko ganin babu wani abu a ciki. Saqonnin yammatan ne suke turowa, wasuma sunfi wata da watanni be bude ba se ita data bude su sannan. Bi ta ringayi tana tura musu da "shegiya mayya karki sake yiwa mijina magana" sannan ta bisu da block. Ko a Jikinsa ta qaraci duk abinda zatayi ta gama ta bashi wayar shikenan zaman lafiya ya qara wanzuwa a tsakani tunda ta sake yarda da Khalil din nata ne ita kadai baya cin Amanrta da kowacce mace. Qauna kuwa se abinda yayi gaba aka ci gaba da tsinkar furen soyayya. Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah se gashi Umaimah ta gama service ga kuma shirin aure dan ana maganar saura sati shida biki ne dan har an kawo lefen Nuratu sune suka zo da saka rana sati shidan dan haka na Umaiman ma aka ce idan sunzo da tasu hakan za'a saka. A cikin satin da suka ce zasu kaqo legeTsautsayi ya samu Hajiyar su Khalil ta fadi a bandaki ta samu karaya a hannunta na dama. Anyi mata dori a Asibiti sedai tsorata da tayi lokacin da ta fadin ya saka jininta ya hau dole aka bata gado suna ci gaba da kula da yanayin jikin nata. Kwananta biyu a Asibitin Umaimah suka shirya zuwa dubota, lokacin itama bata jin dadi tana fama da Malaria amma taji sauqi. Da yamma Khalil yazo ya dauke su ita da Nuratu suka tafi Dubiyar. Sun tarar da Dakin cike da yan uwan Khalil bangaren Hajiyarsa da suka zo dubiya suka gaishe su tareda yi mata fatan samun afuwa, Nuratu ta dire ledojin Fruits da suka taho mata dasu Hajiya se saka musu Albarka take tana nuna wa yan uwanta Amaryar Khalil. Sun zauna can Khalil daya fita bayan daya raka su dakin ya dawo, yana zama wata fara kyakykyawa mai matsakaicin tsaho da jiki ta shigo dakin, tana ganin Khalil fuskarta ta fadadada Fara'a tace "Jinin jiki idon ka kenan" "Cikin farin cikin ganinta ya miqe tsaye ya nufeta yana cewa " Dazu da zan fita daga gida naga shigar mota Layin kamar taku amma saboda banji anyi maganar zuwan ki ba shi yasa ban kawo ko ke bace". Wata Ashar Umaimah ta lailayo a zuciyarta ta dire kafin ta dora da cewa "Ranar nan yace Rabin jiki yar uwarsa ce yau kuma Jinin jiki?" Hannu da suka gaisa akan idon ta ya qara ingiza wutar abinda take ji, lokaci daya idonta ya kada yayi jajir taji kamar jiri na neman dibanta daga zaune lokacin da taji wata mata na cewa "Oh wannan qauna da shaquwa ta Khalil da Jamila an girma amma suna nan kamar lokacin yarinta". Miqewa tayi, dakyar take daga qafarta Nuratu tayi qoqarin kama mata hijab amma ina tuni ta fincike tayi waje gaba daya yan dakin suka rakata da ido. "Ko jikin nata ne ya motsa?" Khalil ya fada yana kallon Nuratu, ta gyada kai dakyar tana hadiyar yawu dan ita tasan ba jiki bane sedai idan Baqin HALIN KISHIN nata ne ya motsa, Khalil ya fita da sauri yana cewa "Bari na dubata, idan jikin ne se mu ga likita a nan ya sake dubata" yayi waje da sauri ya bi bayanta. PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAINAB SHU AIBU FCMB KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻 08162859027 AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO S
🏠