NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 40

yawa wallahi. Tana gidan Mijinta amma duk idan tana da buqatar kudi se taci tudu biyu, mijinta yayi mata nima nayi mata dan Allah ba wayo bane wannan? Koda yake nima dai na kusa ajiye tawa matar dole a ringa daga mun qafa tunda yanzu inda uzurin da zanyi da Kudi" ya qarasa yana kallon fuskar jin harya gama maganar bata ce komai ba. Umaimah kuwa wani irin daci ne ya taso mata kamar zatayi amai saboda tsabar dacin da maganganunsa sukayi mata. Ya iya duban tsabar idanunta yake gaya mata tsohuwar budurwarsa ta kirashi tana neman kudi a hannunsa babu kunya babu tsoron Allah, "Kinyi shiru, lafiya dai naga fuskarki ta chanza" ya fada yana qare mata kallo ganin yanda ta hade fuskar tam har wani ja ja yaga fuskar tayi. A fusace ta bude baki tace "Toh ni ina ruwana can ta shafe ku kaida ita, amma dai ka sani yanda kake magana da matar wani kaima se Allah ya sakawa mijinta anyi da taka. Ita kuma ballagaza mara kamun kai tana gidan wani tana waya da tsohon saurayi zataje ta tarar da Allah, wai Rabin jiki idan ma gangar jikince kai ka sani ai baka burge ba tunda har ka bari wani ya aureta idan kuma da auranta kuka hadu kake neman ta ma duk matsalar kuce ba tawa ba" ta qarasa a mugun fusace kamar zata kai masa mari. Gefen hanya ya gangara ya faka motar ya tsaya kawai yana kallonta dan gaba daya ya rasa mamakin kalamanta zeyi ko kuwa tsoron yanda ta birkice gaba daya tana jifansa da maganganu zeyi? "Wato ga mahaukaciya tana magana ka sakani gaba kana kallona ba? Ai wallahi bansan haka kake ba Khalil kuma ka bani mamaki, ka rasa wa zakayi tarayya da ita se matar aure to wallahi kaida Allah za kuma kaga sakayy....." "Shut up Umaimah ya isheki" ya daka mata tsawar da ta sakat yin shiru ba tareda ta shirya ba. Cigaba yayi da cewa "Kina hankalin ki kuwa kin san me kike fada? Wai ma dakata duk akan me kike wadannan maganganun har kina nema ki jefeni da abinda bana fatan Allah ya jarabceni da aikatawa ba. Bari kiji, ni mace idanba yar gidanmu ba babu abinda yake hada ni da ita balle har muyi magana a waya kece mace ta farko a tsahon rayuwata da wata doguwar magana me muhimmanci ta shiga tsakanin mu. Idan kuma duk saboda Jalila kike wannan babatun" ya dauki wayar ya shiga whatsapp ya kirata video call tana dagawa yace "Ina gayawa yayarki banason mace ta fiya qiba shine na kira mata ke video call taga yanda kika saki jiki kika zama shirgegiya waye za'a cewa ke qanwata ce ya yarda" ya fada cikin tsokana. Daga cikin wayar ta amsa da cewar "Wallahi Khalil ka raina ni, minti daya fa ba kadan bane amma ka ringa cewa ni qanwarkace karma ka saka ta yarda wallahi nice Hassana ni nake gaba da kai kulkum se Hajiya ta raba mana Musun nan amma kaki ka dena cemun qanwarka". "Gata ki fada mata toh amma dai bazan taba yarda ba nine Hassan ke kuma Usaina kawai muje a haka" ya fada yana juya wayar saitin Umaimah da tayi sak tun sanda ya ambaci sunan Jalilan, a sanyaye suka gaisa ko ba'a fada ba kamannin sa dake fuskar Jalilan sun isa su gasgata alaqar jini da take a tsakaninsu. Tsokanar ta ta ri gayi Umaimah na dan murmushi tana satar Kallon Khalil daya zuba mata ido kawai a ransa yana tunani. "Nice Hassanarsa nasan ya ce miki shine Hassan ko, son girma irin na Khalil qila ya gaya miki ya girmi Jamila ma to Yayar muce ita amma ni na karbi qanqantar na bar muku girman kinji Matar Yaya, ki kula mana dashi da kyau" Jalilan ta fada bayan da suka gama gaisawa. Janta take da hira amma ta kasa sakewa, qarshe sukayi sallama ta miqawa Khalil wayar,karba yayi ya kashe still yana kallonta yace "Ko dan gaba karki sake jifana da irin zargin da kika darsa a zuciyarki kuma banyi tsammanin haka daga gare ki ba amma nayi miki uzuri a yanzu ya wuce" kafin ya tada motar suka cigaba da tafiya. "Amma ai kaine ka saka abinda zesa nayi zargi akai, bakaga da sunan da kayi saving number ba ai da sunanta ka saka ko Sister zan gane ammaka saka wani rabin jiki" ta fada tana tura baki dan ba wai hakan ya saka ta naba'a bane, dukda jikinta yayi sanyi da abinda ta aikata din ta kuma ji kunya dan sam ta manta da sunan Hassanar sa kenan Jalila dan tun a wayarsu ta farko ya gaya mata duk sunayen yan uwansa ciki daya da kuma Jamila wadda ita kadai ce suka Uba daya Mamanta ta rasu itama a hannun Hajiyar su ta tashi. Shiru ya mata har ya kaita gida basu sake cewa komai ba dan sosai ransa ya sosu da abinda tayin, yanzu ace ma da wata can yake waya ba Jalilan bace beyi zaton zata iya masa magana da irin lafazin da tayi amfani dasu ba sam basu dace ba, amma yayi mata uzuri tunda karo na farko ne. Umaimah na faman bata rai ta sauka daga motar, a cukulece tayi masa sallama har tayi gaba kuma se ta dawo shidai yana tsaye yana mamakin sabon halin nata na yau tace "Kuma dai gaskiya ka canza sunan da kayi saving number in dai ba kana so zuciya ta ta buga ba idan ina ganin sunan a wayar ka" tana gama fada ta shige gida ta barshi zaune cikin mota yana tunani. Shikam yau abubuwan nata daure masa kai sukeyi, wannan shine Kishin da take fada daman?
🏠