e shi ba wai be dinku ba. Sukayi musu sallama suka fice har sun kai qofa ta jiyo muryar Anty Habi tana cewa
"Yata Allah dai ya nuna mana ranar naki auran tunda ita waccen Allazi bokon ta auri littafi bazamu jirata ba, kina kammalawa zamu sha biki abin mu" Anty Habi ta fada tana bin ta da kallo ganin yanda tayi kyau dukda ba wata kwalliya me yawa tayi a fuskar tata ba.
"Lallai kuwa, ita Allazi bokon ai tafi wannan alqibla tunda ita naga alamar har yau bata san Annabi ya faku ba, duk wani saurayin kirki da zatayi seta kore shi da mugun halinta. yanzu da rana irin ta yau kika zo gidan nan da kinga irin diban Albarkar da tayiwa Qasim akan kawai ya gaisa da wata yarinya sanda yaje dakkota daga makaranta. Yarinyar nan saboda ta isa ta zama yar kanta a qofar gidannan ta tsaya mutane na kallonta tana zuba masa tijara ai ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko a basu kudib su ba, Umaimah kibi a sannu dai tunda kin kori samarin qarshe idan kinci sa'a ki qare da me mata biyu ko uku ai" Mama ta fada, se ta juya bakin qofa i da Umaimah ta coge tunda Maman ta fara magana tace
"Kika tsaya ko da magana ne", cikin muryar kuka kuka tace
"Saboda kawai an miki kishiya Mama se ki ringa yimun fata nima na auri me Mata, in sha Allahu mijina ni kadai ze aura daga ni babu qari har abada" taja fuuu tayi waje.
"Hmmm" kawai Mama tace dan lamarin Umaimah kam se Addu'a.
"Oh ni Anya Yaya Malika lamarin Umaimah babu iskokai a ciki kuwa? Kiga dai farin jini irin na yaran gidan nan, tun fa kafin su gama sakandire suke tsaida mazaje amma ace Umaimah har tana shirin gama HND babu wani tsayayye abu kullum watangaririya ake, se an shirya magan rigidi rigidi se wani tsautsayin ya gifta. ita ba mummunar sufa ba bare ace finta sauran sukayi, waccen miskilar ma ta samu tsayayye balle ita me wayayyen kai ace abu ya gagara? Nifa wannan fadan nata ma gani nake bana lafiya bane gaskiya ya kamata mu tashi tsaye" Anty Laure ta fada tana kallon yayar tata.
"Babu wasu iska sedai iskanci Laure kamar baki san wacece Umaimah ba. kuma da like batun tsayayye ai ba samarin me bata dasu ba, kullum zuwa suke amma mugun halinta da baqin kishi na ba gaira babu data dorawa kanta shi yake korar su. Ni damab na deba lissafa kawo mata kudin aure a wani abu, idan ba ji nayi an daurawa Umaimah aure ba shine kadai zan tabbatar da Miji ya tsaya dan a cikin sakanni tana iya tafka wautar da zata sa ace anfasa auranta.
Toh wane gantalalle ne tun be aureta ba zata fara dora masa ciwon kai ya tsaya?
nake gaya miki fa nan tayiwa Qasim cin mutunci ko kare baze ci ba wai kawai dan ya gaisa da abokiyar karatun ta shi kuma junior sace yarinyar tare sukayi secondary wallahi bakiji ba ina sallah a tsakar gidannan ina jiyota Allah Allah nake na idar na fita naci ubanta akayi sa'a yayansu yazo ya faffalla mata mari tayo ciki, ni nayi mamaki ma da har yau basu aiko sun karbi kudin auransu ba" Mama ta fada cikin matuqar takaici.
"Ashsha abu beyi kyau ba amma me yasa take haka ne, ya ilahi ke ace saurayinki baze kula wata mace ba toh inaga anyi aure kuma" Anty Laure ta fada cikin jimami tana juya hannu.
"Kema kya fada dai, shi yasa na dena raba takaici ta da kowa duk abinda tayi wanda ya gani ya gani shikenan fatana dai kullum shine ubangiji ya shiryeta dan dai wannan halin nata ba hali me kyau bane"
"Addu'ar dai kam ita ce amma dai Yaya karki qi ta tawa Allaha binciketa dai qila da sharrin iskar kin san fa daman baa ganewa se abu yayi tsamari baa fata sannan suke bayyana"
"Allah ya rufa asiri" kawai Mama tace mata ta janyo wata hirar dan ita duk wata sabga da zaace ta hada da malamai ba sonta take ba. Balle kuma Umaimah da sarai ta san babu abinda yake damunta, suma mantaqa sukayi amma ai tun tana qanqanuwarta haka take da bala'in kishi wani baze fita ba, idan kuwa abu ne idan bata dashi tofa sedai kowa ya rasa.
Tayi iya qoqarinta gurin canza mata wannan muguwar Dabi'a abin kuma yayi sauqi se a yanzu da shekarun hankali suka zo mata kuma abu ya ke sake ta'azzara, kuma a duk sanda Shedan ya buga mata gangar ta hau bata ji bata gani sedai fatan Allah ya shirya kawai.
UMAIMAH
Suna fita fuskar nan tata a cukule saboda maganar da Maman tayi suka shiga gidan Maman Nana, basu bata lokaci ba ta take mata rigar ta saka. Dinkine akayi mata na dibar Albarka ya fito mata da duk wata sura da take da ita domin kuwa Allah ya mata qira me kyau, tana da wani irin shape da ko mace ta kalleta seta qara kallo ta.
"Yanzu Umaimah da wannan Kayan zaki fita? Wai me yasa kike haka ne, baki san wannan abin da kike cin amanar iyayenki kike ba?
Ya za'ayi ki fito daga gidanku da shigar Mutunchi amma a waje a ganki da wata shiga ta daban? Wallahi ina jiye miki ranar da wani a gidan ku ze san abinda kikeyi nasan se kin gane kurenki wallahi kiyi ta biyewa su Nabila Sani su dai kin san a gida suka samu lasisin yin duk abinda sukeyi sedai su jira Kamun Allah" Rumah ta fada tana qarewa Umaimah dake daukar selfie Kallo. Kayan sun kamata matuqa ga kalar Atamfar data karbi f