ana juya maganar wane kakar Kishi ne da har zesa a fasa auran Mace.
"Ba zasu iya tsayawa akan mace guda daya ba se sunyi biye biye ni kuma bazan jure hakan ace Mijin da zan aura yana kula wata mace a waje bayan ni ba shine idan nayi magana suke zabar dasu fasa amma ni na dauka hakan lokaci na ne beyi ba, duk ranar da Mijin aurena yazo zanyi".
"Basu dace dake bane shiyasa Allah yake kawo dalilai na rabuwarku saboda ke rabo na ce" Khalil ya bata amsa cikin tabbatarwa, kamar tana gabansa ta sunkuyar da kai cikin qaramin sauti tace
"Allah yasa".
Haka suka ringa aikawa da junansu dadadan kalamai masu sanyaya zuciya har suka gaji sukayi bacci zuciyar Umainah fes tana jin kamar an saka Hypo an wanke mata ita. Baccinta na ranar kuwa cike yake Mafarkai masu dadi na gata sunyi aure da Khalil har sun haifi kyawawan yara suna rayuwa cikin jin dadi da kwanciyar hankali.
*MAFARIN SOYAYYAR UMAIMAH DA KHALIL (QADDARARSU)*
Yanda ta farka washe garin ranar cikin walwala da farin ciki ya bawa kowa Mamaki banda Mama da tasan za'a rina saboda tun a daren da Abban ya shaida mata sunan wanda yazo gurin Umaiman ta tuna da dramer su ta kwanaki ta kuma gane shine dai yaron da yazo jiya da Magriba.
Fatan Alkhairi tayi musu da fata Allah yasa qarshen damuwarta kenan danta yaba danutsuwa da hankalin yaron,tana kumada kyakykyawan yaqini na cewar Umaiman zata samu kulawa da jin dadi a gurinsa.
A cikin sati daya daya biyo baya abubuwa sun chanza sosai wanda suka hada da dawowar walwalar kowa na gidan saboda Farin ciki ko akasin haka na gidan ya ta'allaqa da Umaimah ne, a yanzu kuwa babu wanda ya kaita walwala da farin ciki, saboda yanda a kullum take samun sabuwar kulawa da tattali daga Sabon Habibin nata Khalil.
Wannan dalilin yasa ko da satiya zagayo suka manta da batun zuwan su Aminu Kano yin cika makon Gwajin kwakwalwar da za'ayi mata har seda Dr Kabiru ya kira yayi wa Abba tuni ya kuna sanar masa da sakamakon gurinsu sun fito, yana jira a kawo wancan dinne yayi Nazarin su gaba daya hakan yasa dole suka je Asibitin akayi dukda Umaimah bata so ba, toh daman ita tasan matsalarta kuma ga magani ta samu ina dalilin da zaa ringa kaita ana soka mata qarafuna a kai.
Sakamako ukun duk da suka fito sun nuna cikakkiyar lafiya da kwakwalwarta take dashi, bata taredada wani ciwo ko damuwa illah irin saqon gaggawa na tashin hankali da take aikawa da kwakwalwar tata nema yake neman ya jawo mata ciwon damuwa wanda a gwajin qarshe ma babu alamar hakan dan haka Dr Kabiru yayi mata gargadi sosai tareda bata shawarwari akan ta kula da lafiyar ta dan itace gaba da komai.
BAYAN WATA UKU
A cikin wannan lokacin abubuwa da dama sun faru na jin dadi ciki kuwa harda tsayar da ranar auran Umajmah da Khalil da akayi. Watan su daya da fara soyayya Mahaifiyarsa tazo da kanta suka gana da Mama ta jadda mata irin so da qaunar da sukeyiwa Umaiman, sosai Maman taji dadi ta kuma godewa Allah daya azurya Umaimah da samun suruka ta gari me kuma qaunarta, ba'a rufa sati ba iyayensa maza sukaje da kudin aure da saka ranar su watanni biyar masu zuwa kamar yanda Khalil dinda Umaimah suka tsara wanda yayi daidai da saka ra ar Nuratu da Angonta Dr Sabi'u.
Rikici da hauragiyar Umaimah ya zama tarihi dan tun daga declarationna soyayyartada Khalil wani abu na rashin jin dadi be sake faruwa ba, Khalil na matuqar taka tsantsan da duk wani abu daze bata mata rai har ya kai ga motsawar Matsalarta dan a lokacin da yaje gaishe da Abban ta be rufe shi ba, yayi masa kyakykyawan bayani game da Umaimah da HALIN KISHIN ta.
Hatta da Gurin Malami da Asibi da aka kaita seda ya gaya masa ya kuma Nuna masa takaddun Asibiti da suka nuna shaidar lafiyarta.
"Umaimah yarinyace da duk wanda ya zauna da ita ze sota, banda halinta na rashin sanin yanda zata sarrafa kanta acikin Fushi bata da wata matsala. Nasan zakaji matuqar dadin zama da ita idan har ka kiyaye duk wani abu da ze janyo motsawar rikicinta saboda idan tana son abu, tana kula dashi ne da dukka rayuwarta" Kalaman Abba da ya riqe kenan yake kuma amfani dasu.
Shi da kansa ya shaida Umaimah tana sonsa har wani lokacin ya kanyi mamakin tsakanin shi da ita waya fi wani son wani atsakanin su. Yanda take riritashi da tattalinsa yana saka shi yaji kamar yafi kowanne Namiji sa'a a rayuwarsa, yana yawan hasaso yanda rayuwar auransu zata kasance. Irin soyayyar da zasu shimfida me tsafta, yayan da zasu haifa a kullum ya zauna shiru lissafinsa kenan.
A farko farko ne ma suka fara samun sabani wanda tunda yayi wa tufkar hanci komai ya koma musu daidai. Abinda ya faru wata rana ya dakkota daga gidan Yayarta Nasiba, suna tafe a hanya Abokiyar tagwaitakarsa Jalila da yayi sabin Numberta da 'Rabin jiki' ta kirashi'.
Tunda Umaimah ta kyalla ido taga kiran wayar yanayinta ya chanza daga murmushin da takeyi zuwa fuskar bacin ran da yayi mata dirar mikiya lokaci daya.
Har ya kammala wayar sa ya ajiye be lura da yanayinta ba seda ya kashe wayar yake ce mata "Kinji Jalila ko, wai mata wayonku yayi muku