NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 27 of 40

ya zauce. Tana can tana tunani bata san wayar ta katse ba sega wani kiran ya sake shigowa, ta miqa hannu ta dakkota ta saka a kunne ba tareda tayi magana ba. "Hankalina ya tashi Umaimah, tun jiya nake kiran wayarki a kashe, dazu da safe nazo akace kun tafi Asibiti meya same ki daman baki da Lafiya ne?" Khalil ya jero mata tambayoyin ba tareda tsayawa ba. A maimakon ta bashi amsa sw kawai ta sakar masa sabon kuka me tafe da sheshsheqa, "Yah salam Umaimah ki dena Kuka dan Allah kiyi mun magana ko jikin ne?" Ya fada yanda kasan shima ze fashe da kukan. Lallashinta ya ringayi amma kamar wanda yake qarawa wuta fetur haka ta ringa rusa masa kuka, bata san tsahon lokacin data dauka tana qona masa credit ba dan ta zata ma ya gaji ne ya ajiye wayar ba tareda ya kashe ba se ji tayi yace "Zaki iya fitowa gani a qofar gida". Da mamaki ta cire wayar ta duba, minti Arba'in da hudu ta kwashe tana masa kukan banza ashe tahowa yayi, seta miqe da zumbulelen Hijabin jikinta ta fito ta gani da gaske yake ko wasa ai kuwa ta hango shi a durqushe a qofar gidan suna gaisawa da Abba. Rabewa tayi ta qi qarasawa har seda Abban yazo ze shiga gidan yace mata "Ki bude masa sitting room ku zauna acan" zeta gyada kai ta juya ta dakko muqullin gurin ta bude kafinta leqa tayi masa iso. Kallonta kawai yake kamar wanda ya samu Tv ita ko ta samu guri ta kame fuskar nan a hade kai kace wani mugun saqo ya kawo mata, sallamar Imran dan Anty Saratu ta katse musu shirun da sukayi, ya ajiye Try me daukeda ruwan roba da zobo se gireba a cikin wani dan bowl me kyau. "Sannu nagode yaya sunanka?" Ya fada yana kama hannun yaron, Imran ya bashi amsa kafin ya zura hannu a aljihu ya zaro Yan dari biyar guda hudu ya bashi yace "Maza jeka kasha sweet kaji" yaronya fita da gudunsa yana murna Umaimah ta raka shi da harara. "Umaimah!!!" Ya kira sunanta da wani sauti da ya saka tsigar jiki ta zuba saboda yanda kiran ya shigeta, bata iya amsawa ba illah kyawawan idanunta data dagota zuba masa tana qare masa kallo. Khalil Kyakykyawa ne, irin kyan da kana kallonsa zaka ce wannan yanada kyau. Dukda baqi ne amma hakanbe boye kyansa ba, yana da hanci, ga bakinsa leben qasan yayi ja na saman baqi abinda yake qara matar da yammata akan sa kenan ga kuma wasu irin idanu da Allah yayi masa, koda yaushe ka kalli idonsa kamar mejin bacci, idan kuwa akayi sa'a ya budesu gaba daya akan ka mace ko namiji duk dakiyar ka se kaji wani abu me kama da tsoro ko kwarjininsa ya tsirga maka. "Karki saka na komawa Hajiyata a rabi irin wannan kallo haka" ya fada yana waving hannayensa a gaban fuskarta ganin kamar ma bata gurin tsabar nisan da tayi a tunani. "Oya tell me, meya sameki jiya gaba daya kin daga mun hankali gashi na kasa samunki a waya bare naji ya kike" Kunya ce ta kamata amma ta kanne ta jefeshi da hararar wasa tace "Wayace maka kallonka nakeyi? Me zan kalla mani itama wadda kaje gurin nata rufa ido kawai kayi mata tace tana sonka bawai dan ka hadu ba" ta fada cikin matuqar qarfin danne abinda take ji, so take ta bugi cikinsa taji ya ake ciki sannan taji view dinsa akanta dan bazata zauna a banza da wofi son sa ya kashe ta ba. "Na hadu ko? Thank you for the complement, itama danaje jiya haka ta fada" Yanda tayi da fuska dole ya fashe da dariyar dabe shirya ba, ya fuskanci yarinyar ta folla masa kamar yanda ya fada sonta ba tareda ya sani ba, yana kuma iya karantar tsananin kishinsa a kwayar idanunsa. Dariyar da yayi ta qara qonawa Umaimah rai se kawai ta bude baki ta saka kuka, "Allah ya baki haquri, waike baki san wasa ba komai kuka kamar wata Doll baby" ya fada yana zamowa gabanta. Hijab tasa ta rufe fuska taci gaba da shaqar kukanta, ta tabbata dagaske yana da wata ashe ba Nabila ce zata fara qirga kwanakin ta ba itace lokacin ta yayi. Ganin da yayi dagaske fa take Kukan yasa ya sassauta murya ya shiga bata haquri, "Wasa nake miki, kuma ko jiyan nan da kika ganmu ba dagaske nake miki ba Abokina Mansur na raka duba Maman budurwarsa bata da lafiya shine kwalliyar da kika ga munyi". Dagowa tayi ta kalle shi irin kallon " ka tabbata?" Da ido ya mayar mata da amsar "kiyarda dani" dole tayi qasa da kanta dan bazata iya jurewa kallon cikin idonsa ba, a haka ma tana ji kamar ta mutu saboda shi inaga yana mata wannan kallon me narkar da zuciya. "Nifa bani da budurwa, gashi Hajiya ta takuramun aure take so nayi. Ranar fa da kika je gidan mu shikenan Hajiya ta saka ni a gaba akan ki ita a dole ke budurwa tace. Harfa ta gama gayawa sisters dina nayi mata. Harfa gurin Sister ki taje akan taso tazo nan gidan tayi magana kafin a turo maza dakyar fa na fahimtar da ita ni babu komai tsakanin mu, ta yarda amma ta kafa mun sharadin kafin qarshen shekarar nan dole nayi aure gashi ni ko budurwa bani da ita yanzu bansan yanda zanyi ba, ko kina da qawa ko qanwa data shirya aure ki hada ni da ita? Ni kinga tsoron yammata nake ban taba zuwa nace wa wata ina sonta ba". PROMO PROMO PROMO BEFORE 4K NOW 2500 3968303018 ZAIN
🏠