NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 26 of 40

tarsa a bakin Clinic din. A dardar suka fito suka bi bayanshi da alama yasan gurin suka ringa ratsa mutane suna wucewa abinda ya dan kwantarwa da Umaimah hankali kenan ganin mutane fes fes masu lafiya babu alamar wata lalurar hauka a taredasu, dagaske dai da akace ba Asibitin mahaukata bane, duk wani me lalura data shafi Kai ko kwakwalwa yana zuwa tana wannan tunanin har suka isa qofar wani office Abban ya kwankwasa. Kamar ana jiransu daman aka bude, Babban Mutum dan kadan ne bazasuyi Sa'anni da Abbaba ya miqe ya tare shi ya bashi hannu da gani akwai kyakykyawar Alaqa a tsanin su. "Mukhtar Mukhtar ashe ana ganin ku daman" Likitan ya sake fada fuska dauke da Murmushi bayan da suka gaisa da Mama, Mukhtar da taji ya kira ya tabbatar mata da Abokinsa na quruciya ne da sukayi makaranta tare ne. "Wallahi fa Dr Kabiru haduwa tayi wuya, rabona da kai fa tun Daurin auran yar gidan Faruk Saleh daga nanaka ce ka bar qasar, se kwananan muka sake jiyo ka" Abban ya fada shima. "Toh ya zaayi, rayuwar se a hankali, zumunchi yayi qaranci, amma lafiya kuwa na ganka tareda Madam da yarinyata, daka kirani fa na zata kawai tsohuwar Aminta ce ta motsa yau zaka kawo mun ziyara" Umaimah Abban ya nuna masa lokaci daya bacin rai na taso masa yace"Ga tanan Dr, duk wani gwaji da akeyi a gane lafiyar kwakwalwar mutum ayi mata. Acaje ta tsaf ta yanda zan san abinyi a gaba". "Subhanallahi ta samu Accident ne ko me" Dr ya fada yana miqewa tsaye, kan Umaimah ya dafa ya shiga duba kwayar idonta yana sake cewa "Ina referral letter da file dinta muga menene matsalar?" "Ba accident tayi ba, abubuwa take yi irin na masu tabin hankali kuma mun kaita Ruqiyya ance na Aljanu bane shiyasa nace bari na kawo ta nan". Dariya Dr Kabiru yayi kafin ya koma kujerar sa yana cewa "Haba Mukhtar wani irin abu takeyi haka da har kake zaton tana da matsala a kwakwalwa?" A taqaice Abban yayi masa bayani, Dr yayi shiru yana saurarensa yana kallonta, yes she looks depressed kana ganinta kasan akwai abinda yake damunta. Seda Abbanya gama tsaf kafin ya kalle shi yace "Ko zaku bamu some minutes nayi magana da daughter may be ni zata gaya mun abinda yake damunta daku ta kasa gaya muku" Miqewa sukayi suka koma wajen office din inda akwai kujeru se a sannan Mama take qorafin Yunwa takeji dan basu karya ba suka fito dan Haka Abbanya fita dubawa ko ze samo musu wani abinda zasu ci. A ciki kuwa cikin lallami da dabara Dr Kabir ya samu Umaimah da yana fara mata tambayoyi ta saka kuka ta fara bashi amsa. Tambayarta yake akanme yake damunta? Wane yanayi take ji a jikinta da sauran abubuwa daya kamata likitan kwakwalwa kamar sa ya tambayi mara lafiyarsa. Sosai mamaki ya qulle masa kai yanda take masa bayanin abinda takeji dangane da kishi akan wanda take so. "Idanna ganshi da wata ko naji yayi maganar mace ji nake kamar zuciyata tana ci da wuta, kawai rayawa nake a raina zan iya kashe ko wacece ta shiga rayuwarsa kuma kome za'ayi mun bazan damu ba indai akan sa ne" Umaimah ta fada hankali kwance ba tareda shakku ko dar a zuciyarta. "Uhm lallai kam akwai matsala" Dr kabir ya fada kafin yayi rubutu a wata takadda ya miqe tsaye yace mata yana zuwa. Waje ya fita inda su Abba suke, a taqaice ya masa bayanin akwai gwajin da zasu mata guda uku, biyu zasuyi mata yanzu dayan kuma sedau suje Aminu Kano dan Injinsu na nan ya samu matsala. Abban yace ya bashi yaje ya biya kudin amma yaqi yace dai su bata abinci taci bari yaje ya gani idan gurin suna aiki. Wasa wasa sega Umaimah a dakin gwajin kwakwalwa, gajin farko general check up ne na kwakwalwa dan a ga ko akwai wani ciwo data samu dalilin buguwa ko faduwa ko kuma an haifeta dashi ba'a sani ba se yanzu yake bayyana. Daga nan kuma akayi mata gwajin tunani. Basu suka bar Dawanau ba se kusan la'asar, har suka isa gida jin kanta take wani gingirin kai yaji inji, dan dayan gwajin se wani satin ma sannan zasu samu saboda se da appointment. Wani lallaba ta Mama harma da sauran yan gidan suka shigayi kafin fitowar sakamakon gwaji tasan matsayinta. Bayan sallar Magriba tana zaune ta jona wayarta da se lokacin ta tuna ashe tun jiyan a kashe take chaji, ta manta shaf data kashe ta jiyan qila shiyasa Khalil be kirata ba ya aiko yaro. Tuno sunansa da tayi nan da nan abinda take ji ya nemi dawo mata sabo, qoqarin kiran sunayen Allah ta shigayi kamar yanda Malam ya gaya mata amma shedan da ya rigada ya samu gurin zama me kyau a zuciyarya ya shiga bijiro mata da wasu tunanikan na banza raya mata yake yanzu fa jiya yaje neman aure gidan su wata qila ma an bashi ita, kai an bashi ma inane Khalil zeje neman aure ace za'a hana shi kawai seta shiga rera kuka mara sauti. Qarar da wayar ta tayi ce ta sakata dagowa, sunan Khalil ta gani yana yawo akai, meya kira kuma ya gaya mata yanzu idan baso yake ya qarasa ta ba? Da so samu ne bazata amsa wayar ba amma ina zuciyarta bazata iya ba, ta rigada ta yarda zuciyarta ta kamu da mummunan Son Khalil, So me tsanani irin wanda ka iya saka me yinsa
🏠