NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 40

a kashe abinda ma ya saka yayi aike kenan amma har sannan a kashe. Yana so yaji lafiyarta amma babu hali, haka ya koma gida bacci kansa rabi da rabi yayi, duk juyin da zeyi seta fado masa a rai Addu'arsa Allah ya bata lafiya zuwa safiya kafin ya wuce aiki zw biya ya ga yaya jikinnata. *KHALIL DA UMAIMAH SOYAYYA GAMON JINI* *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 7 Washe gari kuwa kamar yanda Abba ya fada qarfe 8 suka isa gidan Babban Malami Sheik Ali Musa. Sun tarar da Malam yana bada karatun safe, dan haka Abban ya zauna a gurin bayan anyiwa Su Umaimah da Mama iso cikin gidan Malam. Idan kaga yanda ta zabge a dare daya seka yi zaton ta dade tana jinya, akan fuskarta zaka karanci tarin damuwar da take ciki shiyasa koda Mama tace ta shirya zasu fitan batayi musu ba, bazasu fahimceta ba dan haka idan anje gurin suka fada musu bata da wasu Aljanu sa qyaleta ta sarara. Se gurin qarfe tara Malam ya samu shigowa, a sitting room dinsa suka zauna bayan sun sake gaisawa yana kallon Umaimah data jingina da bango ta tafi duniyar tunani yacewa Abba "Lafiya dai Alhaji Sabo naganku da sassafe haka?" "Eh to lafiya ba lafiya ba Akaramakallahu" Abban ya fada kafin ya gyara zaman sa a taqaice ya zayyanowa Malam Ali duk abinda yake faruwa da Umaiman, ya rufe da cewa "Jiya haka nan ta yanke jiki ta fadi shine har yanzu ta ke aikin koke koke babu magana kuma. Shiyasa nace gara muzo tun kafin abu yayi tsamarin da magance shi zeyi wahala". Malam Ali da tun fara maganar Abba yake nazarin Umaimah, shidai a iya sanin da ilimin da yake dashi ta bangaren abinda ya shafi aljanu bega wata alama a tattare da ita ba saboda koda ace Aljanun sun barta kafin su shigo gidan ne indai tana da shafar su seya gane amma dai bari ya sake bincikawa tunda shaqiyancin jinnu kullum qaruwa yake, wani lokacin idan sukayi wani alayen badan qarfin Ayar Allah ba bazasu gane ba. Wani turaren mai ya dauko ya miqawa Mama yace ta shafa mata a goshinta,kunne da kuma qofofin hanci yasan duk inda Aljani ya buya a jikinta idan turaren ya shiga jikinta seya fito, Umaimah kuwa haka ta tsaya Mama ta shafa mata turaren dukda rashin dadinsa amma yata iya, gara a wuce wannan maganar adena qaqabamata iskokai babu gaira babu dalili a barta taji da damuwarta. Karatu Malam din ya yafa yi mata, ya dauki tsahon lokaci yana yi amma ko gezau batayi ba harya gaji dan kansa ya dakata. Wayarsa ya dauka yayi kira, babu dadewa sega wata babbara Mace da zasuyi Sa'a da Maman ta shigo da kaskon wuta da garwashi, karba yayi zata tafi yace ta tsaya. Wani turaren hayaqi ya debo ya zuba ya bata ta ajiye a gaban Umaiman data zura musu ido tana kallon ikon Allah jin hayaqin yasa ta kauda kai, matar ta janyo fuskarta ta dawo da ita saitin Hayaqin, Umaimah ta fara zuga Atishawa saboda sam bata shiri da hayaqi, Mama dake gefe ji tayi kanta ya fara mata wani Yuummm dan daman tunda ta shafa mata maganin nan warinsa yake damunta, miqewa tayi tace "Alhaji bari naje daga waje hayaqin nan ya dameni" ta fice baranda inda iska take kadawa ai kuwa Umaimah bata san sanda ta fashe da dariya ba har seda Abba yai saurin matsawa dan abin yazo masa a bazata. A ranta tace "Allah shi qara, idanni baa tayar mun da Aljanu ba ai gashi nan zaa tsokalo miki naki" "Allah gafarta Malam sunzo ko?" abba ya fada yana raba ido dan fa shi yana da tsoron Aljanu daman, murmushi Malam yayi yace "Aa, shaqiyanci ne irin na dan yau baka gani ba da mahaifiyarta take saboda hayaqin ya koreta kar nata na gado su motsa" "Allah ya rufa asiri" Abba ya fada ya sake rabewa gefe. Har hayaqi yaci ya cinye dai babu Aljanun Umaimah babu dalilinsu, Matar ya umarta da ta sakeyi mata karatun, ta zauna a gabanta ta kama babban dan yatsan hannunta kafin ta fara mata karatu a kunne nan ma dai shiru ba labari. "Gaskiya Alhaji sabo duk wani ilimi da dabara da nake dashi akan al'amarin nan na gwada ka gani kuma, yarinyar nan bata da shafi ko rabar jinnu a tare da ita. Sedai idan wata matsala ta daban ce take damunta da tayi kamanceceniya da matsalar Iska" Malam ya fada yana duban Abba, shima ya gamsu da hakan dan haka ya gyara zama yana cewa "Toh Allah gafarta malam, a yanda mahaifiyarta take fada abin nata yawanci yana tashi ne dalilin Kishi, tana da tsananin Kishi kaga karo uku kenan ana fasa auranta kuma duk ita take jawowa da baqin HALIN KISHIN ta, shin ko akwai wasu Aljanu da suke saka mutum ya zama me tsananin Kishi haka??" "Murmushi Malam yayi kafin yace " Shi Kishi halittace Alhaji Sabo kuma ko wanne dan Adam yana dashi sedai na wani yafi na wani zafi, ko kuma wani yafi wani sanin yanda ze sarrafa kishin nasa. A yanayinta tana da zafin zuciya da sauri
🏠