i raji'un' tayi nasarar furtawa a fili kafin ta tafi tamkar zata kifa yayi saurin tarota, a rikice ya shiga jijjigata yana cewa
" Umaimah Umaimah ke Umaimah lafiyar ki kuwa? Mansur shiga gidan na kayi sallama dan Allah muji ko daman bata da lafiya" ya fada ganin tana lumshe ido kamar me shirin tafiya dogon suma.
Abokinsa Mansur daya yi mutuwar tsaye ya zura da gudu zuwa cikin gidab su Umaimah se ganin mutum kawai sukayi, a taqaice ya kalli Nuratu da Salima babbar Yar Anty Saratu yace "kuzo dan Allah" kafin ya juya ya fice,ai gaba daya suka rufa masa baya harda Anty da Maman tunda basu san me ya faru ba.
Hango Umaimah dake riqe a hannun Khalil ya qara daga musu hankali suka isa gurin da sauri, Anty ce ta karbeta Nuratu ta taimaka gurin qara kamota suka riqeta dakyau suna tambayar sa meya faru
"Wallahi Hajiya bamu sani ba, lafiya lau ta fito na miqo mata kayan nan(ya nuna kayan da suka watse a qasa tun daya taro ta kafin yaci gaba da cewa) kawai naga kamar hankalinta baya kaina na sake mata magana se ji kawai mukayi tayi salati ta tafi zata fadi na tareta amma wallahi babu abinda mukayi mata, zaki iya tambayar samarin can dan tunda muka zo suna zaune a gurin" ya qarasa yana nuna mata majalisar su Malam Sadi, kamar kuwa yana jira Malam Sadin ya taso yana cewa
"Ashsha Ashsha mutanenne suka motsa mata ko, daga jin yanda taja dogon salatin nan ina ga gamo tayi ku kamata muje cikin gida" yayi gaba ze shiga gidan Mama data kasa magana ta tareshi da cewa
"Jeka abinka, idan muna da buqatar ka zaa kira ka, Samari mun gode ko ku gaida gida" ta qarasa tana kallonsu Khalil da gaba daya kana kallonsa kasan hankalinsa a tashe yake kafin tabi bayan su Anty da suka shige gida da Umaimah.
Akan babbar tabarmar dake tsakat gidan suka kwantar da ita Nuratu ta shiga daki ta dakko abin auna jini da bugub zuciya ta shiga dubata, ita kuwa Umaimah Abinda take ji yau ya wuce ta dora hannu aka tayi ihu, kukan take amma na zuciya hawaye kadai ke kwaranya a idonta.
"Mama kodai a kirawo Malam Sadin ne ni banga komai daya same ta ba qila abin bana Asibiti bane" Nuratu ta fada tana kallon Mama data zabga tagumi, se ta girgiza mata kai alamar Aa, kafin ta juya ga Umaimah dake Hawaye idonta a rufe ta kira sunan ta tace
"Zo Umaimah, taso ki gaya mun meya same ki" Kamar jira takeyi kuwa ta tashi daga kwanciyar ta fada jikin Maman tareda fashewa da kukan da kana jinsa kasan tundaga qasan zuciyarta yake fitowa.
"Qila gidan su Nabila zeje, dan daman jiya Rumah take cewa ta gansu a hanya sun shigo Kano ashe amma basu kulata ba, qila maganar auran nasu ta kankama da gaske kenan" ta sake rushewa da Kuka kamar Numfashinta ze dauke
Bayanta Mama ta ringa bubbugawa kawai da sigar lallashi gaba daya ranta a jagule yake, dagaske akwai akwai Alamomin Aljanu tattare da Umaimah masu yawa haka wani sa'in tana nuna alamar me motsi a kwakwalwa ya kamata su dauki mataki dan da alama abin kullum gaba yake ba baya ba.
A haka Abba ya shigo ya same su, Nuratu ce ta gaya masa iya abida suka sani da farko yayi kamar ya shareta dan yasan be wuce iskanci ta ne ya motsa ba amma kuma ganin irin kukanda take dole ta baka tausayi, anyi anyi tayi magana taqi, data bude baqi baqin cikin abun yake shaqeta ta kasa magana se sabon kuka ya kufce mata, sun yarda da zancen Malam Sadi na cewar Gamo tayi dan haka suka kwanta da qudurin da sassafe zasu kaita gidan wani babban Malami da Abban suke daukar karatu Asabar da Lahadi.
A bangaren Khalil kuwa kai a kulle suka bar qofar gidan nasu, tsabar yanda ya rikice kasa tuqa motar yayi se Mansur ne ya karba.
"Khalil, dama yarinyar nan nada matsalar Jinnu ne?" Mansur ya katse shirun da sukayi kowa na jimami a zuciyarsa, se Khalil yaja ajiyar zuciya kafin yace
"Wallahi bansani ba. Gaba daya wannan itace haduwa ta da ita ta biyu da mukayi doguwar Magana ban san komai a kanta ba amma naji wannan mutum yana fada qilan ko tana dasu ne"
"Tab ai kuwa da sake dan bazan baka shawarar ka kwasowa kanka shirgin Iska ba, mata masu lafiyar ma yaya aka qare da rigimar su bare kuma gyaran Malam. Tunda dai abu beyi nisa ba gaskiya Dude back out" Mansur ya sake fada daidai sanda yasha kwanar gidan su Budurwar sa, kwalliyar da sukayi zasuje duba Maman Budurwar ne da bata da lafiya.
"Daman matsalar Aljanu tana hana a aure ne maimakon ma kace na nema mata magani, beside mun tabbatar da Aljanu takeyi ko kuma wani health issue ne na daban, kawai ka tayani Addu'ar Allah ya bata lafiya amma maganar na janye ma babu ita dan yanzu na fara Son Umaimah"
"Allah dai ya biya mijin gyaran Malam, se ka koyi ruqiyya saboda tashin dare, dan wallahi Matar Iro Black har kan kwano take hawa, kota kwasa a guje tayi titi, seka shirya yar tsere a layi mutumina" Mansur ya sake fada.
Banza Khalil ya masa har suka qarasa gidan, da farko ma cewa yayi baze shiga ba, seda Mansur din ya nuna bacin rai kafin suka shiga. Yana mata yaya jiki ya fito waje ya baro shi kiwa yana ta sake gwada kiran wayar Umaimah da tun dazu ya jita