NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 40

ba, da kin so kiji aike zaki kirani ba se yanzu dana kira zaki tambayeni ba" Khalil ya fada daga dayan bangaren, "Thats remind me, a ina ka samu number na?" Umaimah ta fada tana gyara kwanciyarta da kyau akan Gadon, "Baqauya kawai, wayace miki har yanzu ana tambayar ina aka samu number budurwa ne" "Ni ba baqauyiya bace" ta fada a sakalce tana tura baki, akan me zece mata baqauya, ita da take yar tsakiyar birni bama shi dan bayan badala ba. "Toh yi haquri yar birni" ya fada yana dariyar yanda tayi maganar kafin yaci gaba da cewa, "Dadin tuqina ya saka kin manta da folder credentials dinki, kinga da a commercial car ne da yanzu se ki tafi gidan redio cigiyan wanda ya tsinta". Dafa baki Umaimah tayi tana tashi zaune tace "Subhanallahi, wallahi na manta shaf kuma ban lura ba. Dase nazo daukar wani abun sannan ne zan ga babu su" "Daman kinji tuqin babban Driver ina zaki tuna" ya sake fada cikin sigar tsokana, seta mayar masa da cewar "Babu wani nan, bayan nama fika iya tuqin kanayi a hankali kamar me tsoron hanya" "Oh haka kike ce? Toh next time idan mun hadu za'a gwada se muga wanda yafi wani iyawa" "Allah ya kaimu zan kuwa baka mamaki" ta fada cikin tabbatarwa bayan a zahiri inda ake takawa ma mota tayi tafiya bata sani ba, ba kuma dan babu inda zata koya ba Aa koda basu da Mota a gida banda ta Abbansu amma Yayyenta mata masu aure kowacce nada motar hawa, ita dan karambanin nan ma yasa ta hau bata taba ba tafi gane ta kame a kujera a jata. Hira suka danyi kafin ya mata sallama da cewar idan ya samu dama zuwa dare ze kawo mata, idan kuma bezo yau ba se dai zuwa Litinin dan washe garin juma'a zeyi tafiya zuwa Dutse akwai aikin da sujeyi acan kuma se ranar Lahadi ze dawo. Wannan waya da sukayi ba qaramin nishadi ta saka Umaimah ba, ta ringa walwala, su kansu mutanen gidan seda suka ringa tambayarta Albishir din me ta samu da take farin ciki haka sedai tayi murmushi tace babu komai. Be kawo mata a daren ba, ai kuwa baqin ciki ya mata dirar mikiya ya shafe walwalar data wuni a ciki dan tun magriba ta fesa wanka dukda batayi kwalliya ba amma ta saka kaya da suka qara haska tah tayi fes, shiru har akayi isha babu shi babu kiran wayarsa tun tana zuba ido qarshe se jiyo radion da Abba ya kunna tayi a tsakar gida ana wani shirin siyasa da yake ji qarfe Goman dare. Ita kadai ta ringa zuga tsaki tana juyi a gado, kamar ta kirashi amma in ta tuna daman ya gaya mata ba lallai yazo a yau din ba se ta Kanne, yanzu har se ranar litinin zata sake ganinsa kenan? Wannan abu ya mata ciwo da yawa. Haka ta cinye weekend gashi ko a waya be kirata ba, sundai yi magana ta whatsapp ta saka status ya duba suka gaisa daga nan be sake ce mata komai ba. Ranar Litinin bayan magriba suna zaune a tsakar gida wani yaro ya shiga "Wai ana sallama da Umaimah a qofar gida" yaron ya fada, se tayi tsam daga abinda takeyi ta kalle shi. Wane dan rainin hankalin ne ze aiko sallama da ita? Tasan dai duk masu zuwa gunta se sun kirata a waya shi wane isashshen ne haka da ze aiko ba tareda tasan da zuwan sa ba. "Kaje kace ba ta nan" ta fada se Mama tayi saurin dakatar dashi tana hararta tace "Je ka tambayo wane ne kace tana zuwa" "Mama fa ni bamuyi da kowa ze zo gurina ba kawai se a aiko kice ace ina zuwa indai mutumin kirki ne ai seya fara sanar dani kafin yazo" ta fada kamar zatayi kuka dan tasan tabbas baze wuce irin yan yawar samarin nan masu bi gida gida suna sallama da yammata ba. Banza Mama ta mata taci gaba da lazumin da takeyi, sega sallamar yaron ya sake dawo yace "wai Khalil ne, kuma yace sauri yake yi kizo ki karba saqon". "Khalil?" Ta fada a fili tana kallon yaron kamar shi ze bata amsa kafin ta shiga qarewa kanta kallon, Zani ne da T shirt a jikinta tunda tayi wanka da La'asar ta sakasu se qaurin manja takeyi saboda suyar wainar fulawa take a lokacin. Miqewa tayi ta nufi daki, Mama da tunda akace Khalil ta zuba mata ido tana so ta tuno ina ta taba jin Umaimah ta ambaci sunan tana tunanin Umaiman ta fito ta chanza kayan jikinta zuwa baqar doguqar riga ta yafa mayafinta, "Mama bari na karbo, credentials dina na manta ranar a makaranta shine ya kawo min" ta fice da sauri. Su biyu ta gani tsaye jikin mota sunsha kwalliya kamar masu zuwa gurin daurin aure, "Allah yaso ki kin fito, yanzu na ke shirin neman wani yaron na bashi ya kai miki se fa dana ce wancan ya gaya miki sauri nakeyi" Ya fada bayan data gaishe su, harar wasa tayi masa kafin tace "Sauri zuwa ina? Kun wani sha shadda kamar masu zuwa tambayar aure" "Kin canka daidai tambayar aurana zamu je, saurin da nakeyi kenan saboda baban yari yar qarfe 8 yace muzo kinga be kamata tun yanzu na fara sabawa sirikina lokaci ba" Khalil ya fada yana miqa mata Folder da kuma wata farar leda me dan girma. Idan tace tayi suman wucin gadi batayi qarya ba dan daga can sama ta ringa jin muryarsa yana ce mata "Ki karba mana, kin tsaya kina kallona karki sa na rage kyau kafin naje gurin Amaryata". 'Innalillahi wa'inna ilaih
🏠