NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 40

Taf ta cika mata bowl da farfesun Naman rago daya ji kayan qamshi yawun Umaimah har tsinkewa yake, "Ki duba fridge a dakina ki debi Zobo, akwai biredi akan Dining se ki hada tunda shinkafar bata sauka ba" Antyn ta sake fada tana kallonta. "Nagode" ta fada a fili ta juyaa ranta kuwa cewa tayi "Dole in sha ai tunda da kudin ubanmu kike hada sana'ar dama base kin gaya munba" Ta wuce dakinnata ta bid Frizer da take zuba zobon siyarwa a jarkoki suke sunyi sanyi sosai dan wasu har sunfara qanqara, yaron daya ke daukar mata ne ma be qaraso ba da tuni yanzu qila an gama wawason sa saboda yanda takeyin sa da kyau ga dadi sosai ake rububinsa. Daki Umaimah ta baje, tana zama aka kawo wuta tayi Hamdala ta kunna Fankar sama data qasa ta shiga dangwalar Romon tana ci da biredi gefe ga L and Z dinta ta cika kofi tana kurba duniya sabuwa ga iskar fanka ta ko ina, bata ji shigowar Mama ba se maganar ta taji a kanta tana cewa "Kwarai da gaske, baki dafa ba amma kece farkon ci koh? Toh idan kin gama kije ki gyaramun daki" Maman ta fada tana qare mata kallo. Ajiyar zuciya tasaki dan a zatonta fada maman zata mata tace toh, seda ta qoshi ta kora da zobonta me sanyi ta huta kafin ta tafi dakin maman. A palour ta tarar da ita da wata baquwa sun baje kuloli masu kyau suna dubawa da alama talla ta kawo mata dan se koda mata su take, gaishe da baquwar tayi ta shige ciki ta fara gyarowa, tana jiyo baquwar tana cewa Maman "Hajiya na zata saiti bibbiyu zaki dauka tunda yan matan naki biyu ne ko" "Aa yanzu dai dayan zan dauka ita wannan da saura idan lokaci yayi a siya" Maman ta bata amsa "Ai kuwa da kin siya kin huta dan kinsan kullum qara kudi kayan suke abinda ka siya dubu daya yau gobe idan kika koma se kiji daya da dari biyar koma dubu biyu, wannan hauhawar fara shi dai Allah ya mana maganin sa" matar ta sake fada. Murmushi Mama tayi tace "Yanzu dai bari na dauki na dayar da nayi niyya ita ce me garanti, wannan kinsan sau nawa ina mata tarin kayan kitchen? Da takaici ya isheni fitar dasu nayi na rabawa yan uwanta wasu na biki dasu duk randa Allah yasa ta tsayar da hankalinta ta fitar da Miji a kaita da abinda ya sawwaqa" "Allah dai ya rufa asiri, in sha Allahu ma tareda yar uwarta zaki saka su a Lalle". Baki Umaimah ta tunzura gaba, wayasani ma ko irin wadannan maganganun da maman take a kanta ne suka hana mijin tsayuwa ita kullum me laifi ce a idon Maman, Allah dai ya yanke mata ta tafi itama kowa ya huta a sannan zaa gane amfaninta ai. Haka ta gyaro dakin ta wanke Bandaki tsaf lokacin matar sun gama ta wuce se Maman ita kadai tana waya da wanda yake kawo mata Manja daga Kudu da yake tana siyar da Manja da Mangyada, hannun kujera ta nema ta zauna tana jiranta harta gama. "Ya akayi?" maman ta tambayeta, "Na gama gyara ciki saura nan" "Toh bismillah mana ko na hana kine" Maman ta sake fada, seta miqe ta shiga tattare kwalayen tace "Ina zaa ajiye wadannan kayan toh" "Saka su can dakin" Maman ta nuna mata dayan dakinta data mayar dashi na aje shirgi Wanda da Su Umaimah suke ciki kafin Yayyensu suyi aure su koma dakin da suka bari na tsakar gidan. Bude dakin tayi ta shigar dasu, "Mama duk kayan can Yaya Nuratu zaa jibgawa su? Toh Allah yasa dai ta samu gidan da ze dauka koda yake ma gidan quaters ne ai kin ma san yanda suke sedai idan an a tafi dasu a dawo da wasu a san dai kin mata kaya da yawa kawai" Umaiman ta fada tana kade kujeru, da kallo kawai Maman take binta, a ranta tana nema mata shiriya daga gurin Allah dan lamarin nata kullum qara gaba yake. Bata damu da shirun da Maman tayi ba taci gaba da cewa "Qilama ni da bakya ta tawa na fita samun babban gida, kinga lokacin ai a tasheki a tsaye ki rasa yanda zakiyi" "Allah baze hanani yanda zanyi ba dan ubanki keda bakinki sam besan abinda ze fada ba, fita ki bani guri na fasa gyaran daman idan baki yi niyyar abu ba se kin san yanda kika jangwalo aka ce ki barshi" Maman ta fada kamar zata kai mata duka, Dariya ta sheqe da ita ta shiga cewa "Haba Hajiyar mu easy mana, nifa wasa nake miki. Yo ko yanzu aka ce a fito Hajiya ai a shirye kike Allah dai ya bar manake Hajjaju". Ganin da Mama tayi tana neman mayar da ita wata abin tsokana yasa ita ta bar mata dakin ta koma tsakar gida inda inuwa ta dan fara sauka suka shiga hira da Anty Saratu. Umaimah ko tas ta gyara dakin ta goge ta saka qamshi, tada zafin nama idan ta saka kanta ta iya aiki sosai dan wannan horon Mama ne duk yaranta seda ta tabbatar da ta horasu yanda duk inda sukaje bazata ji kunya ba, daman Umaimace me son jiki a ciki, amma idan ta tashi yin aikin kuma zatayi shi dakyau. Dakinsu ta koma ta kwanta kafin rana tayi tana so taje kitso, tana hawa kan gadon wayarta dake jikin chaji ta fara qara, kamar bazata daga ba se kuma ta janyo ta ta amsa kiran ba tareda tayi magana ba. "Amincin Allah ya tabbata a gareki" Aka fada da muryar da tanaji ta gane waye, murmushi ne ya kufce mata, "Tareda kai, ina fatan kaje gida lafiya?" Ta bashi amsa. "Ban sani
🏠