NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 18 of 40

iya ta mutu shashasha mara hankali" Message din qarshe kenan na Nabila daya shigo wayar Yanda kasan zatayi aman wuta saboda bacin rai haka ta shiga neman Layin Nabilan amma yaqi shiga alamar tayi blocking di ta kenan, kiran ta mayar kan Fauziyya ita din ma yaqi shiga, "bakin su daya kenan?" Ta ayyana a zuciyarta. Kwafa tayi idanunta suka kada sukayi jajir ta shiga turawa da Nabilan saqo kamar haka "Ko a mafarki kika ganki tare da Khalil ki tabbatar da kin fara irga kwanakin da suka rage miki a duniya dan ni Umaimah se nayi Ajalinki, idan kuma kina ganin wasa ne kuma kin cika mara kunya ki bari mu hadu" ta tura mata. Ajiye wayar tayi ta hade hannu biyu tareda dora qafa daya kan daya tana girgizawa, jiran Amsar Nabila take amma har aka kwashe kusan awa biyu bata yo reply ba, excuse ta dauka akan bata da lafiya ta tattara kayan ta ta tafi gida lokacin tashin su beyi ba dan ba zata iya ci gaba da zama a gurin. Seda ta kwashe sati tana jinyar zuciyarta akan kishin wanda bema san tana yi ba, Alwashi kala kala taci akan haduwarsu da Nabilan duk randa Allah yasa sukayi ido hudu zasu kwashi yan Kallo kuwa. QARSHEN QAWANCEN UMAIMAH DA NABILA. Watan kusan biyu kenan da faruwar wancan Al'amarin, zuciyarta tayi sanyi hankalin ta ya dawo jikinta har tana jin haushin kanta akan abinda ta aikata. Ita da kanta ta yarda da shirmen da tayi be kamata ba kuma akan wanda be ma san tana yi ba ita a yanzu bata tsammanin ma idan ta ganshi zata gane fuskarsa sabon tsahon lokacin data dauka bata ganshi ba. Tana so ta nemi Nabila ta bata haquri amma wata zuciyar da take saka ta aikata mugun abun ta hanata, gaya mata take ai ba laifi tayi ba kuma ita Nabilan ita ya kamata ta fara neman ta ta bata haquri sannan su shirya da wannan ta shashantar da maganar ta fita akanta. Tayi sabon saurayi a gurin aikinsu, Balarabe Isha, yana aiki a ma'aikatar da take bautar qasa bangaren Finance. Ba yaro bane a qalla zeyi shekara Arba'in sun kuma samu kyakykyawar Fahimta dashi dan har yana zuwa gida hira gurinta sun ma fara shirye shiryen saka manya a maganar. A yanda ya gaya mata Matarsa ce ta rasu yana kuma da yara hudu, dukda yace matar ta rasu amma hakan be hana baqin kishinta motsawa akan Matar da bata ma duniyar gaba daya ba, Sumayya sunanta wannan dalili yasa ta debi karan tsana ta dora akan duk wata me suna Sumayyan. Ko a hanya aka kira sunan in sha Allahu seta bankawa me sunan Harara tayi tsaki. Sauqin da aka samu Balarabe Isah na matuqar qoqari gurin kiyaye duk abinda ze motsa mata da Kishin nata dan yana matuqar sonta da gaske. Ranar wata Juma'a bayan sun taso daga aiki ya dakkota ze kawo ta gida, suna tafe suna hirar su gwanin dadi dan sosai Balarabe yake ririta Umaimah duk wani abu da ze sosa ranta baya yinsa. Suna tafe sun shiga layinsu kenan aka kirashi a waya da yake wayar na ajiye a tsakiyarsu ne karaf Umaimah taga sunan me kiran 'Wife'. Wani qululu daya taso mata ta hadiye ta kalli Balarabe da yayi tsilli tsilli da ido kamar wanda aka qure tace "ka daga mana ba kiranka ake ba" ta fada a dake, sosai take kokawa da abinda yake taso mata, so take ta koyi haquri da dauke kan da kullum ake ce mata bata dashi. Shiru yayi yana aikin rarraba ido ga wayar se qara take dan kiran na katsea wani ya sake shigowa, Tsawa da daka masa akan ya dauki wayar kamar wani danta dan ta kasa riqe bacin ranta, kai Dole ma taci kutumar uban mutumin nan dan ya goge mata hadda iya hadda. Ya yaudareta yace mata matarsa ta mutu nufinsa se ta aureshi sannan zataje ta tarar da wata kome? Ai kuwa da a ranar daga shi har matar sedai suyi kwanan barzahu sedai duk yanda zaayi da ita ayi. Daga inda take tana iya jiyo muryar matar se shagwaba take masa akan tana jiransa fa yazo ya kaita gidan biki ana rana bazata iya fita ta hau Napep ba, Allah sarki Balarabe zufa yake sharewa kota ina yanda kasan wanda ya zauna akan kunama, magana yake so yayi amma ya kasa se kawai ya kashe wayar ya ajiye yana kallon Umaimah data tsura masa ido kamar me nazarin ta inda zata shaqeshi ta aika shi lahira. "Kace mun ta mutu, yanzu daga lahirar ta kiraka kenan?" Ta tambaye shi ido ta akan sa, Balarabe ya hadiye miyau qut saboda yanda tayi bala'in yi masa kwarjini nan ya shiga laluban kalaman da ze kare kansa dasu, dakyar ya iya cewa "Dagaske nake Matata Sumayya ta rasu shekaru uku kenan yanzu, bayan rasuwarta da shekara daya akayi mun madadi da qanwarta da suke uba daya Surayya dukda bana sonta amma haka na karba ko dan saboda Yarana da banida me riqemun su saboda Mahaifiyata ta tsufa bazata iya kula dasu ba, amma ki yarda dani badan ina sonta na aure ba, nayi ne kawai saboda samun mafita, kuma yanzu a shirye nake dana rabu da ita saboda ke" "Sedai ka saketa ka auri uwarka Balarabe, kuma yanda ka cuceni ka bata mun lokaci ka yaudareni kaima Allah yasa ayiwa yarka, wallahi ko kallon sani ka sakeyi mun se na maka rashin mutunchin da bazaka manta dani ba" ta fada cikin Fushi kafin ta bude motar ta fice, badan tana tsoron karta tijara shi a wajen
🏠