NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 40

a ta debo masa ya ciro wani qullin magani daga Aljihunsa yana kallonsu yace "A samo abu a rufa mata se ku fita daga waje, idan kuma zaku iya shaqar hayaqin maganin ku tsaya tunda sunqi magana gara a sakasu ta dole" ya qarasa yana barbada magani a kaskon nan take suka fara jera Atishaqa saboda wani yajida maqaqi da suka taso lokaci daya suka nemi su shaqe su, shi kansa tarin yake ba shiri aka fara rige rigen fita daga dakin harda Umaimah da damanita ba shiri take da hayaqi ba. "Ku riqota karku bari ta fita" Malam Sadi ya fada ganin ta nufi qofa Nuratu ta matsa da niyyar riqeta ta hankadevta tana cewa "Dallah kyaleni ni lafiyata qalau babu wasu Aljanu da nakeyi, abu ne ya same ni ku barni nayi kukana ko zanji sanyi kun wani dakko shi bayan ma ko Ruqiyyar be iya ba" tana gama fada ta zaka kai tayi waje ta barsu da baki bude. "Hajiya baku san sharrin Jinnu ba qarya ce irin tasu kawai sunji magani ne shine zasu fake suce itace da kun kamota ta shaqi hayaqin nan da kansu zasu bar jikinta yanzun nan" Malam Sadi ya sake fada. Se Mama ta daga masa hannu tana cewa "Kaje kawai mungode, Nuratu fita da hayaqin ki kashe a bude winduna iska ta shigo" tayi waje itama. Umaimah ko can kan Dandamalin qofar dakin Mama ta samu ta zauna taci gaba da rusa kukan da bata san ko na menene ba, idan ta tuna wai Nabila taga Khalil kuma tana sonsa ji take kamar tayita buga kanta a bango har se ya fashe ta dena tuna abin. "Zo Umaimah" Mama ta fada a tausashe kafin ta shige uwar dakinta ta zauna bakin gado tana jiran Umaimah, ita fa wannan lamari ya fara bata tsori, a yanda take abubuwa tabbas duk wanda ya gani zece shafar Aljanu ne amma kamar yanda tace lafiyarta qalau itama ta yarda da hakan bari tazo taji menene dan gaskiya idan ba Aljanu ba qila toh yarinyar nan nada tabin kwakwalwa basu gane ba. "Meya sameki kike ihu haka gaba daya kin rikitamu?" Maman ta sake fada a tausashe tana kallon Umaimah dake jera Ajiyar zuciya kamar zata shide, wannan tambaya da Mama tayi mata ta sake fama mata ciwon aiko ta fashe da gunjin kuka tana riqe kai Mama dai se ido dan abin ya fara tsoratata. Seda tayi me isarta ta tsagaita tace "Nabila ce, wai..wai tana son Khalil" "Waye Khalil?" Maman ta sake tambayarta, seda taja numfashi ta dan ja baya daga gaban maman kafin tace "Wani ne, a makaranta ta taba ganinsa, shine yanzu suka hadu a Lagos kuma wai tana son sa auransa zatayi" ta qarasa tana fashewa da sabon kuka kalmar auran data fada tana mata ciwo. Mama da taji bacin rai ya mata dirar mikiya saboda ko kusa kalaman ta babu na hankali a ciki bata ma fahimci me take nufi ba, daga Nabila taga wani tana so zata aure shi se ya zama dalilin da zata ri ga wa mutane irin wannan Haukan a gida, cikin kaushin murya tace mata "Kinsan ni ba sa'ar wasan ki bace da zaki zauna kina gaya mun shirme, zaki fada mun dalilin kukan ko sena saba miki yanzun nan" "Wallahi Mama gaskiya na fada miki, wai son sa take yi ni Kuma bana so, akan me duk mazan duniya zata ce shi take so? Wallahi baze aure ta ba sedai ta tafi can ta samu wani" "Saboda uwarsa ce ke ko ubansa? Meye ma hadinki dashi da shiga sharafin rayuwarsa?" Mamanta sake fada cikin bacin rai kamar zata kai mata duka, se Umaimah ta miqe tana ci gaba da kukan tace "Bani da hadi dashi amma wallahi baze aureta ba sedai ya tafi can ya nemi wata matar badai ita ba, haka kawai ya aure ta na ringa ganin shine mijinta ai bazey...." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta yasa tayi shiru, tsawa ta daka mata tana nuna mata hanya tace "fita daga nan fitinanniyar yarinya da bata qaunar a zauna lafiya. Tsabar neman masifa ina ruwanki da sabgar ta? Kiji da kanki mana ko kuwa baqin ciki kike mata ta samu miji ke kina zaune kin rasa? To kici gaba karki fasa daga mana hankali a gidan nan dan ubanki idan kika kaini bango ni kaina bansan abinda zan miki ba Umaimah". Fada sosai Mama ta ringayi dan abin ba qaramin qona mata rai yayi ba, tama kasa gane kan dalilin wannan rashin hankali amma shikenna zatayi maganinta ne. Umaimah kuwa har dare tana ta ciwon rai, idan abin ya ciwo ta ta zura kanta cikin pillow ta fasa ihu dan Mama ta ce wallahi ta sake jin muryarta seta mata dukan mutuwa a gidan, tasan kuma zata aikata dan haka ta qule a daki tasha kukanta ita kadai, tambayar da takeyiwa kanta data rasa amsa shine wai duk wannan abin da takeyi a wanne dalili me? Meye hadinta da Khalil din da har taje jin wannan zazzafan Kishin akansa? Ko kuwa kishin nata ya burunqasa ne ya zama akan kowa da komai ma yinsa take? Toh ita dai koma yaya ne tana kishin *Khalil*, kishi me tsanani da bata zaton ta taba yiwa wata halitta shi. Washe garin ranar data fita aiki ta nemi qaramar waya ta dora layinta akai tunda waccen ta tashi daga aiki. Messages din Nabila ne suka ringa shigowa na martani akan abinda Umaiman ta fada mata, ta kuma sake jaddada mata se tayi soyayya da Khalil, "Idan ma sonsa kike sedai kuwa Son nan ya kashe ki dan wannan karon yafi qarfin ki, kina ji kina gani zamuyi aure sedai ki hadiyi zuc
🏠