NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 40

data fuskanci gaba daya ma bata mata lokaci sukeyi tunda babu wanda ya yarda da maganar a fito ayi aure wasu ma sedai su sako wata maganar banzar nan take kuwa zata qarewa mutum tanadi kafin ta dannawa lambarsa block, gaba daya ma ita ta fita sabgar samari yanzu, inda take dan samun nutsuwa ganin Abba be tada maganar ba, amma a tsorace take dan tasan yana iya mata dirar mikiya a koda yaushe gashi har yanzu bata samu tsayayye ba, a cikin haka Me neman auran Nuratu ya turo da saka rana shekara daya yayi daidai da kammala karatun Likitancinta haka itama Umaimah lokacin ta kammala Bautar qasa. A daren ranar da Abba ya tara su ya shaida musu tare ze hada ya aurar dasu ita da Nuratu ba qaramin dadi taji ba, ta tabbatar da yardar Allah shekarar nan bazat cika ba seta samu wanda zasu daidaita su kuma daddale da maganar aure. Akace wai ana zatom kura tayi lafiya ashe da sauran zawo, ranar wata Asabar babu aiki, tana kwance a dakinsu suna Voice call dasu Nabila mutanen Lagos acan suke bautar qasar su. Sun samu guri suna tsula tsiyarsu babu me ce musu su gyara sedai fatan shiriyar Allah kawai. "Ke qawata ina ta so na miki magana se na manta ina guy din nan kuna haduwa kuwa idan kinje gidan Anty Hajiyayye" Nabila ta fada daga can bangaren, Kwanciya Umaimah ta gyara bayan data zura Earpiece a wayar tace mata "Wane mutumi kuma, kefa a rayuwarki baki da zance sena samari kodan baki dasu ne se Allah" "Karki nemi ki gaya mun magana malama daman kinsan ance wani jinkiri Alkhairi ne toh da alama nima nawa jinkirin ze zama Alkhairin" Nabila ta fada tana fari da ido, se Umaimah tace "Toh ina jinki meya faru yanzu?" "Last week bana fada miki munje Birthday partyn wani corper da muke service guri daya ba a wani Restaurant akayi, kawai in gaya miki se gashi mun hadu da Guy din nan na office din Sir Nasir. Oh my God Umaimah kinganshi kuwa yanda ya hade cikin wasu J and T wallahi da farko ban ma gane shine ba kawai naji ya qara tafiya da imanina seda muka matsa kusa na ga fuskarsa na gane shine ashe. Akayi Sa'a cikin wadanda muke tare kawai naji wani Ya kira Sunansa *Architect Khalil Umar Bayero* bansan sanda na saki ihun murna ba, Maims daga yanayin kayan jikinsa da abincin da sukayi order kadai kinsan akwai chanji a hannuna, se daya bude baki yayi magana gaba daya ya qarasa kwance mun kai kinji Husky Voice dinsa Umaimah? Kinga wata arniyar mota daya tuqa suka bar gurin? Na rantse i can die for that guy yayi mun to the core shine daidai mijin da nake ta jira na samu, ga kyau ga aji a yayan banki ashe basaja kawai yake yi a Kano yana yawo akan Lifan". Tunda Nabila ta fara magana ta fuskanci akan wa takeyi taji wani irin duhu ya fara mamaye mata idanu, gaba daya ma dena fuskantar ta tayi tana jinta ne amma sam bata gane me take cewa idanunta kawai hasko mata Khalil suke yanayiwa Nabilan wannan tsadaddan murmushin nasa daya saka ta fara tunanin mutum ne ko Aljani? "Umaimah kina jina kuwa kin barni se magana nake kinyi shiru" Nabilan ta fada jin shirun yayi yawa. Bata san ya akayi ba se jin bakinta kawai tayi yana furta "Daga yau Nabila babu ni babu ke, idan kuma kika sake kika qara yi mun magana na rantse da Allah se naci kutumar ubanki, yar iska kwartuwa mebin mazan mutane" tana gama fadar haka qit ta kashe wayar tayi wurgi da ita ta hadu da bango nan take ta tarwatse. Hannu biyu ta dora akai ta fasa ihun daya saka nuratu wuntsulowa daga kan gado dan tuni tayi suman zaune tun sanda Umaiman ta fara korawa Nabila warning. "Meya faru? Akan waye? Sune tambayoyin da Nuratu takewa kanta da bata da me bata amsarsu se Umaimah dake birgima tana zunduma ihu a qasa kamar wadda ta hau iskokai. *DAGA ALQALAMIN MARYAM FAROUK* *(UMMU-MAHEER)* *MARUBUCIYAR* *WATA KISHIYAR🥰👹 (ALKHAIRI CE KO SHARRI)* *RUBUTACCIYAR QADDARAH AND NOW* *HALIN KISHI* *HALIN KISHI LITTAFIN KUDI NE NAIRA 500* *GA DUK ME SO ZE TURA DA 500 ZUWA ASUSUN* *8142548705* *OPAY DIGITAL SERVICE* *MARYAM UMAR FAROUK* *SE A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA 07061838488* Free page 5 Da gudu Nuratu ta fita kiran Mama ganin yanda Umaiman take ihu tana birgima kawai wadda ta hau iska. "Nuratu leqa ki kira Malam Sadi ko Auwalu suyi mata ruqiyya, mun shiga uku a ina kuma Umaimah ta kwaso iskoki" Mama data shiga dakin zani a hannu Anty na take mata baya ta fada suka shiga qoqarin riqeta amma ina se zillewa take tana ihu da kururuwa haka Malam Sadi ya same su ya shigo da dogon carbin sa ya samu guri ya zauna daga gefe ya su riqeta, qarfi suka hada su ukun suka mata muguwar dannan shi ko ya shiga karanto Ayoyin ruqiyya yana tofeta daga i da yake zaune. Banda Kukan baqin ciki babu abinda Umaimah takeyi, wannan shine duka biyu, ga abinda yake damunta sannan anzo an wani danne ta ana mata ruqiyya se kace tace musu iskokai takeyi. Ganin da Malam Sadi yayi ta dena bige bigen se kuka ya saka shi cewa su saketa kowa taja gefe tana numfashi kamar wanda sukayi gudun famfalaqi, se ya cewa Nuratu ta samo garwashin wuta, fit
🏠