da a fusace tana kallonta, har Fauziyyan ta bude baki zata bata amsa Umaimah ta dakatar dasu tana cewa
"Malamai ya ishe ku zaku fara halin naku kamar kaji, ke kuma sauka daga titi kafin ya rage miki farashi" ta qarasa tana kamo Nabila gefe saboda hango Khalil daya fafaro mashin dinsa kamar ze tashi sama.
"Wannan kamar guy din nan na office din Sir Nasir" Nabila ta fada tana binsa da kallo se Umaimah ta gyada kai tace
"Tabbas shine, daman ina ta tunanin ina na san fuskar sa ashe saurayin Nabila ne" ta fada da sigar wasa.
Baki Nabilan ta tabe tace
"Wallahi ya hadu kawai dai matsakar sa rashin chanji, kome yazoyi nan oho qila gidan su wani abokin nasa yazo" tayi tambaya ta bawa kanta amsa duk ita kadai se Umaimah ta nuna mata gidan su tana cewa
"Kinga gidan su can, ko zaki shiga ki gaida surukarki"
"Aa kakan surukata banason wulaqanci" daga haka suka ci gaba da tafiya har ta raka su bakin get din layin kuwa babu wanda yace musu tafi ku mutu dukda ga Maza nan samari da magidanta suna ta qoqarin Shiga masallaci dan an kira sallah kota kansu basu bi ba. A bakin Get din tayi musu sallama ta juya.
A qofar masallacin taga Khalil yana alwala ya bita da kallo ta galla masa harara se ya sakar mata murmushi ba shiri ta dafe qirji jin zuciyarta ta buga da qarfi kamar wadda ta tsorata. A haka ta shiga gidan faran faran kamar wadda aka biyo saboda yanda taji gaba daya zuciyarta na tsere kanta har wani sarawa yakeyi.
"Ke lafiyar kuwa kika fadowa mutane babu ko sallama" Maman Asad ta fada tana qare mata kallo, se Umaimah ta kalleta tace
"Inaga Gamo nayi, wani mutum na gani, kai ba mutum bane Aljanine" ta fada kamar me tantamar abin
"Idan ma rauhanine zaki gani ai, saboda baku da hankali da magribar nan haka kuka kwashi qafa kuka fita, ni sam bana son wadannan qawayen naki gaba daya basu da nutsuwa har gara gara Halima a cikin su daman amma wadannan biyun bansan wadda tafi wata rashin hankali a cikin su ba"
"daga abin arziqi kuma shine zaki zagesu yan gidan mu nawa suka haihu basuje musu barka ba seke, daman mantawa nayi baa miki abun kirki dama basu zo ba" Umaimah ta fada tana zumbura baki,
"Da suka zo din uwar me na qaru da zuwan nasu fitsararriya? Ki shiga hankalinki idan ba haka ba kuma sena hadaki da Abba ina daman an raba ki dasu kinqi ji ko? Shikenan" Hajiyayye ta fada tana wuceta, Umaimah ta rakata da harara, wallahi badan tafi samun yanci anan ba da gidan su zata tafi haka kawai mata ta sakata a gaba ta ringa mata masifa daga an mata abin kirki anzo mata barka? Ai shikenan maganin ta itama gobe ta qara.
Haka rayuwa taci gaba da mirginawa da dadi babu dadi Umaimah na zaune gidan Hajiyayye har Sukayi arba'in ranar kuwa bata qara kwana a gidan ba ta tattara ta wuce dan daman tuni taso tafiya Mama ce ta hana saboda Anty Larai ta tafi qauyensu yarinyarta bata da lafiya gashi su Asad sun dawo daga hutu dan haka hidimomin sunwa Hajiyayyen yawa.
A dan zaman da sukayi ko fada anyi shi yafi sau cikin kwando, Umaimah rashin jiz Hajiyayye rashin haquri, haka zata biye mata suyita hayaniya musamman da Mijinta ba mazauni bane shiyasa Umaiman ke samun yanda take so.
Sam ta manta da wani Khalil da shirginsa dan tun waccen ranar bata sake haduqmwa dashi ba daman ba fita ta fiya yi ba, idan ma ta fita ko kallon gidan su batayi, abu daya ta kasa gane kansa Khalil din na yawan fado mata a rai, duk kuma sanda ta tuna shi se taji irin faduwar gaban ranar na har ta ringa ayyana a ranta kodai maye ne? Idan ma mayene to sedai yaci kansa amma ita kam kurwarta daci ne da ita.
ko ranar da Hajiyarsu ta shiga gidan yiwa Maman Asad barka qin fitowa tayi su gaisa tana ji tana ta tambayar ta ina take ta bige da baccin qarya, tana jinta tana wasu soki burutsun data kasa gane kansu.
Ita kanta Yaya Hajiyayyen bata fuskanci abinda Hajiyar take magana akai ba kawai dai ta ringa binta da toh, koda ta sake tambayar Umaiman itama babu wata magana daga gareta da haka zancen ya shiririce.
Komawarta gida da kwana biyu result dinsu ya fito masha Allah ta fita da sakamako mekyau, nan da nan aka shiga hidimar registration na NYSC bayan dan lokaci kadan suka shiga Camp, badan taso ba aka barta a Kano saboda gaba daya qawayen nata basa Kano, Fannah sun koma Miduguri da Mijinta dan shima dan can ne, Rumasa'u ma Jigawa ta tafi zata zauna a gidan Yayarta, Fauziyya, Nabila da Nadiya daman Kudu suka ce zasuje wanda itama tayi niyyar bin ayarin dukda bata da tabbacin a gida za'a barta amma dai da ko iya camping taje tayi in yaso daga baya a nema mata Relocation se gashi ana fara Registration din Yaya Aminu ya shiga ya fita ta hanyar abokinsa aka barta a Kanon tayi Camp dinta a Qaraye bayan sun fito akayi posting nata nan cikin Sakatariyar Audu Baqo.
Lafia lau take fita aikinta da take jin dadi a yanzu ko ba komai yana debe mata kewa, zancen manena dai abu shiru kamar anyi ruwa an dauke, ita a yanzu bazata iya tuna yaushe rabon da ace ana sallama da ita ba. Duk samarin sun zama sedai a kira waya ko ayi chatting,